Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:a cikin lokaci

Discussion page of a cikin lokaci
Revision as of 20:47, 23 June 2019 by Maintenance script (talk | contribs) (Quick edit: appended Category:Glosbe (pid:))
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)

Glosbe's example sentences of a cikin lokaci [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar a cikin lokaci:
    1. A cikin lokaci, Jehobah ya cika alkawarinsa na ’yanta mutanensa daga bauta a Babila kuma ya mai da bauta ta gaskiya a Urushalima.
      Right on time, Jehovah fulfilled his promise to free his people from Babylonian exile and restore true worship in Jerusalem. [2]

    2. An yi wata tambaya a jaridar game da Majami’ar Mulkin da aka gina a birnin Martos cewa: “Ta yaya mutane masu ba da kai suka fito daga yankuna dabam-dabam [a ƙasar Sifen] zuwa birnin Martos don su gina wannan wuri mai kyau da tsari a cikin ƙanƙanin lokaci, a wannan duniyar da ke cike da masu son kai?”
      Commenting on the construction of such a Kingdom Hall in the town of Martos, the paper asked: “How is it possible that in this present world based on selfishness, volunteers from various regions [of Spain] unselfishly travel to Martos in order to erect a building that has broken all records for speed, perfection, and organization?” [3]

    3. Ayoyin da suka biyo bayanta sun bayyana cewa a cikin dogon lokaci, waɗanda aka kira ranaku a alamance, Allah ya tsara duniya don mu rayu a cikinta, kuma ya halicci dukan abubuwa masu ban al’ajabi da ke duniyarmu.
      The verses that follow explain that in a series of long periods, figuratively called days, God went on to prepare our earthly home, bringing into existence all the wonders of our natural world. [4]

    4. 8 Maƙasudi na uku da za ku iya cim ma wa a cikin ɗan lokaci shi ne shirya yin kalami a kowane taron ikilisiya.
      8 A third short-term goal you could set is that of preparing an answer for each congregation meeting. [5]

    5. Ta hanyar salon fassara da na’urar buga littattafai a harsuna masu yawa, ana buga talifofin nazari na Hasumiyar Tsaro a cikin harsuna 135 a lokaci ɗaya, kuma fiye da kashi 95 na masu karatunta a gewayen duniya za su iya nazarin wannan littafin a yarensu.
      By means of coordinated translation methods and multilanguage publishing equipment, the principal articles in The Watchtower are published simultaneously in 135 languages, and over 95 percent of its readers worldwide can study the material in their own language at the same time. [6]

    6. Ko da yake tsakiyar mako ne kuma an yi sanarwar a cikin ƙurarren lokaci, mutane 25 ne suka hallara, sun tako ne a ƙasa wasu kuma sun zo a kan jaki.
      Although it was midweek and on short notice, 25 came, arriving on foot and on burro. [7]

    7. (Wahayin Yahaya 20:1-3, 6; 21:3, 4) A cikin wannan lokaci na lalacin ƙasa, za su yi tsammanin ganin Aljanna da aka kafa a duniya.
      (Revelation 20:1-3, 6; 21:3, 4) In these times of ecological crisis, they relish the certain prospect of seeing Paradise established on earth. [8]

    8. Wannan ne karo na farko a tarihin ƙasar Amirka da Kotun Ƙoli ya sake yanke hukunci da ya bambanta da wanda ya yanke da farko a cikin gajeren lokaci.
      It was the first time in U.S. history that the Supreme Court had reversed itself in such a short period of time. [9]

    9. 28 Kwanaki 2,300 na Daniel sura 8 da kuma kwanaki 1,290 da 1,335 na sura 12, duk sun wuce—can bayanmu a cikin nisan lokaci.
      28 The 2,300 days of Daniel chapter 8 as well as the 1,290 and the 1,335 days of Da chapter 12 are all past —behind us in the stream of time. [10]

    10. 2 Babbar gata ce mu sa hannu cikin shuka gaskiyar Littafi Mai-Tsarki a cikin wannan lokaci na ƙarshe.
      2 It is a great privilege to share in the sowing of Bible truth in this time of the end. [11]

    11. (Kolossiyawa 3:14) Saboda haka, waye a tsakaninmu zai fara gwada ƙarfin gami da ya kasance tsakaninsu a cikin wannan lokaci mai yawa sosai?
      (Colossians 3:14) Who of us, then, can begin to fathom the power of a bond that has existed over such an immense span of time? [12]

    12. Amma, a wani lokaci a cikin tafiyarsu kuma don dalilin da ba a ambata ba, Yohanna Markus ya bar abokansa kuma ya koma gida.
      But at a certain point in their journey and for a reason not specified, John Mark left his companions and returned home. [13]

    13. 17:15-17) Allah ya ce za a haifi Ishaku “a cikin wannan lokaci baɗi war haka.”
      17:15-17) God said that Isaac would be born “at this appointed time next year.” [14]

    14. 7 Don ku ƙarfafa bangaskiyarku, ku kafa maƙasudai da za ku iya cim ma wa a cikin ɗan lokaci.
      7 To help strengthen your faith, why not set some short-term goals? [15]

    15. A annabce wannan yana waƙiltar yaƙi, ƙarancin abinci, cuta, kuma waɗannan abubuwan duk sun auku ne a cikin wannan lokaci mai tsawo da aka kira “kwanaki na ƙarshe.”
      These prophetically represent war, food shortages, and pestilence, all of which have occurred over the extended period of time that is referred to as “the last days.” [16]

    16. Domin ajizancin da muka gada, dukanmu muna da halin yin “kishi,” har Kiristoci da suka daɗe a cikin gaskiya a wani lokaci suna yin kishin yanayi, dukiya, gata, ko kuma iyawar wasu.
      Because of inherited imperfection, we all have “a tendency to envy,” and even longtime Christians may occasionally feel jealous of the circumstances, possessions, privileges, or abilities of others. [17]

    17. (b) A cikin wane lokaci ne muke, kuma me ya kamata mu yi?
      (b) In what period are we living, and what should we do? [18]

    18. Hakika, wannan saurayin yana zuwa don nazarin kullum, har suka gama littafin nan Sanin a cikin ɗan lokaci.
      In fact, the young man came for a study daily, and the Knowledge book was completed in a relatively short time. [19]

    19. Tun da ƙasidun ba su da rubutu da yawa, za a iya fassara su da sauƙi kuma a cikin ƙanƙanin lokaci.
      Because they have little text, they can be translated quickly and easily. [20]

    20. Mene ne aka cim ma ta wajen gina Majami’un Mulki a cikin ƙanƙanin lokaci?
      What has the construction of quickly built Kingdom Halls provided? [21]

    21. Hakazalika, ganin cewa abubuwan da Yesu ya annabta suna faruwa a cikin ƙayyadadden lokaci alamu ne cewa ƙarshe ya kusa.
      Likewise, the occurrence within one time period of all the things Jesus foretold would be a recognizable sign that the end is near. [22]

    22. (Matta 6: 7, 8) Muna iya yin addu’a a cikin ladabi, kowane lokaci, da kuma a kowane wuri.
      (Matthew 6:7, 8) We can pray in any respectful position, at any time, and at any place. [23]

    23. Amma, zai fi kyau a tattauna wasu batutuwa masu wuya da yaron a wani lokaci cikin makon don kada ya ji kunya a gaban ’yan’uwansa.
      However, it may be best to discuss sensitive personal issues privately with a child at another time during the week so as to avoid embarrassing him in front of his siblings. [24]

    24. “Na yi mamaki cewa ta wajen gwada ƙa’idodi ko labarai da ke cikin Nassi da juna, a yawancin lokaci, za ka sami amsar a cikin Littafi Mai Tsarki,” in ji Steven.
      “It amazed me that by simply comparing a number of Scriptural principles or accounts, often the truth of a matter was right there all the time,” says Steven. [25]

    25. Mun san hakan ta ja-gorar da aka ba dattawa a cikin Nassi, waɗanda wani lokaci sukan yi shari’a da waɗanda suke yin zunubi mai tsanani a cikin ikilisiya.
      This is reflected in the Scriptural guidance given to elders, who sometimes have to handle cases of gross sin in the congregation. [26]


Retrieved June 23, 2019, 4:46 pm via glosbe (pid: 13629)