#Hausa transcriptions of some of today's news from DW Hausa @BBCHausa and others. <> Labaran duniya a rubuce na yau 2022-03-30. https://t.co/bU6918gQot
— Hausa Internet Radio (@HausaRadio) March 30, 2022
hausaradio/DWHausa/safe/2022-03-30
- Mai gabatarwa (host): Zaharaddeen Umar Dutsen Kura
- 'Yan bindiga sun taso jihar taraban Najeriya a gaba, inda suka datsa wata gada mai matuƙar mahimmanci ga sufarin jihar...
- Sannan za ku ji 'yan Najeriya masu amfani da jirgin kasar - Kaduna zuwa Abuja - na nuna takaici da alhininsu kan harin da 'yan bindiga suka kai wa jirgin a ranar litinin.
- Za mu ji yadda 'yan ƙasar Ghana ke ji bayan da gwamnati ta buɗe iyakokin kasar na tudu da kuma teku.
hausaradio/BBCHausa/dare/2022-03-30 [1]
- Masu gabatarwa (hosts): Sani Aliyu (ya karanto labaran duniya daga ofishin Abuja),
- Hukumar kare hakkin bil adama ta duniya ta ce hare haren da Rasha ke kaiwa a Ukraine sun jefa fararen hula cikin mummunanar hali, kuma hakan zai iya zama laifin yaƙi.
- China ta ce ta duƙufa wajen ganin ta yi ƙoƙadaddangantakarta da Rasha, ta kuma yi Allah wadai da takunkuman da ƙasashen duniya ke ƙaƙagawa Rashar.
- A Najeriya, majalisar waƙilan ƙasar ta ɗage zaman bin bahasi da ta shirya da manyan jami'an tsaro da ministocin ƙasar a kan harin da aka kaiwa jirgin ƙasa saboda rashin halittar jami'an da aka gayyata.
- "Mataimakin majalisa ya ce ya yadda da wakilcinsu, amma akwai tambayoyin da ba za su iya amsa su ba saboda ba su ke da nauyin tsare mutane ba. An ɗaga taron nan sai an samu halartar su wadannan jami'an da ake kira."
- Toh har wayau a Najeriyar, hukumomi a jihar Niger sun ce haɗarin kwale-kwale ya hallaka aƙalla mutum takwas wadanda ke kokarin tserawa harin 'yan bindiga a wani ƙauye na jihar
- "Akwai biyu da Allah Ya musu rasuwa, akwai kuma kananan yara shida, sannan akwai wasu mutum biyar da har yanzu ana nan ana kokarin ganin yadda za a zaƙalo su ko a raye ko a mace."
Rikicin Ukraine: Shakku game da janyewar Rasha - Labaran Talabijin na 30/03/22 [2]
- Ukraine ta nuna shakku game da shirin Rasha na rage yawan dakarunta a ƙasar.
- Za mu kuma ga mayaƙan Syria da suka niƙi garin fafatawa a Ukraine ɗin da sunan Rasha.
- Yanzu dai an san ƙasashe biyar da za su wakilci nahiyar Afrika a gasar ƙwallon ƙafar da za a yi a ƙarshen shekara a Qatar.
- Other world news (at the 6th minute)... Kwamishinar kare hakkin bil adama majalisar dinkin duniya, Michelle Bachelet, ta ce hare-hare kan mai uwa da wabi da Rasha ke kaiwa a yankuna masu cinkoson jama'a a Ukraine, za su iya kasancewa laifuffukan yaƙi. Da take jawabi a majalisar kare hakkin jama'a a Geneva. Ms. Bachelet ta ce mamayar Rashar ta jefa Ukraine cikin uku. Kuma ta tilastawa miliyoyin jama'a tserewa. Ta yi kira ga Rashar da ta daina kai hare-haren ba da ɓata lokaci ba. Ta kuma janye sojojinta daga Ukraine ɗin.