#
|
Yan Najeriya na yi wa gwamnatin Buhari shaguɓe kan kama Akanta Janar da EFCC ta yi [1]
|
Nigerians Reaction over Buhari's Government EFCC's arrest of Accountant General
|
1
|
An wayi garin Talata 17 ga watan Mayun 2022
|
--
|
2
|
ƴan Najeriya suna ta mayar da martani kan
|
Nigerians are reacting to
|
3
|
kamun da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon ƙasa wato EFCC ta yi wa Babban Akantan kasar, bisa zarginsa da almundahanar kuɗi har naira biliyan 80.
|
the arrest of the Accountant General by the Economic and Financial Crimes Comission (EFCC) for alleged embezzlement of N80 billion.
|
4
|
Hukumar,
|
The commission,
|
5
|
a cikin wata sanarwa
|
in a statement
|
6
|
da ta wallafa a shafinta na Facebook,
|
posted on its Facebook page,
|
7
|
ta ce ta kama Ahmed Idris ne a ranar Litinin a Kano da ke arewacin kasar.
|
said it had arrested Ahmed Idris on Mon in the northern city of Kano.
|
8
|
EFCC na zargin Ahmed da karkatar da kuɗin ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi.
|
The EFCC accuses Ahmed of misappropriating funds through his friends and family and other means.
|
9
|
Ta ce an yi amfani da kuɗin wurin gina rukunin gidaje a Kano da Abuja.
|
--
|
10
|
An kama Ahmed Idris
|
Ahmed Idris was arrested
|
11
|
bayan ya ƙi amsa gayyatar da EFCC ta rinƙa aika masa
|
after he refused an invitation from the EFCC to appear before it
|
12
|
domin tuhumarsa kan zarge-zargen da ake yi masa,
|
for questioning over allegations against him,
|
13
|
kamar yadda hukumar ta bayyana.
|
according to the commission.
|
14
|
Dandalin sada zumunta na Tuwita da Facebook
|
The social networking site Twitter and Facebook
|
15
|
sun zama manyan wuraren da ƴan ƙasar suka bazama suna bayyana ra'ayoyinsu a kan wannan lamari da ya kunno kai.
|
have become major forums for citizens to express their views on this emerging issue.
|
16
|
Maudu'ai biyar ne da suka danganci batun suke tashe a Tuwita da suka hada da #80bn da #Ahmed Idris da #EFCC da #Accountant General da kuma #ASUU, inda dubban mutane ke tattaunawa.
|
Five topics related to the issue are being raised (trending) on Twitter including #80bn ($192,687,504) and #AhmedIdris and #EFCC and #Accountant General and #ASUU, where thousands of people are debating.
|
17
|
A dandalin Facebook kuwa kusan mutum 25,000 ne ke tsokaci kan batun da safiyar Talatar.
|
On Facebook, about 25,000 people commented on the issue on Tuesday morning.
|
18
|
Mutane sun fi mayar da hankali ne wajen yi wa Shugaba Buhari shaguɓe
|
People have been more vocal in their opposition to President Buhari
|
19
|
tare da alaƙanta batun
|
and linked the issue
|
20
|
da yajin aikin da malaman jami'a ke yi a halin yanzu,
|
to the ongoing university teachers' strike,
|
21
|
wanda ya sanya ɗalibai zaman gidan tilas.
|
which has forced students to stay home.
|
22
|
Yayin da wasu kuma suke ganin abin kunya ne
|
While others see it as a shame
|
23
|
a ce ana samun irin wannan lamari na almundahana a gwamnatin Buhari,
|
to see such corruption prevalent in the Buhari administration,
|
24
|
wacce tun kafin kafuwarta ta dinga da'awar cewa za ta yi yaƙi da cin hanci da rashawa.
|
which even before its inception claimed to be fighting corruption.
|
25
|
Ga dai abubuwan da wasu ke faɗa a Tuwita:
|
Here are some comments on Twitter:
|
26
|
@LadyRoza_001 ta ce:
|
@LadyRoza_001 said:
|
27
|
"A ƙasar da ke fama da talauci,
|
"In a poor country,
|
28
|
mutum ɗaya zai saci naira biliyan 80 cikin ƙasa
|
one person would steal 80 billion naira
|
29
|
da shekara huɗu da ɗarewarsa kan wannan muƙami.
|
in less than four years of holding this position.
|
30
|
Wannan lamari ne mai muni."
|
This is a terrible thing."
|
31
|
— `ℝ𝕠𝕫𝕒😈🌶️ (@LadyRoza_001) May 17, 2022 [2]
|
--
|
32
|
@ifeanyidamian11 ya ce:
|
@ifanyidamian11 said:
|
33
|
"A yanayin da ake ciki da ɗalibai ke zaune a gida saboda yajin aiki tsawon wata biyu,
|
"In a situation where students are living at home due to a two-month strike,
|
34
|
amma wani mai son zuciyar ya sace naira biliyan 80, yayin da ita ASUU ke neman a biya ta abin da ko kusa da wancan kuɗin bai kai ba."
|
one volunteer stole N80 billion, while ASUU is seeking compensation for that or less. the money is not enough."
|
35
|
— Ifeanyi Damian (@ifeanyidamian11) May 16, 2022 [3]
|
--
|
36
|
A shafin BBC Hausa na Facebook kuwa kusan mutum 3,00 ne suka yi tsokaci kan labarin.
|
On the BBC Hausa Facebook page, almost 3,00 people commented on the story.
|
37
|
Abdullahi Auwal Sulaiman ya ce: "A daidai lokacin da ASUU suke yajin aiki a kan biliyan 200, sai ga shi mutum daya kacal ya saci biliyan 80 shi kadai. Allah ya isar mana.
|
Abdullahi Auwal Sulaiman said: "At a time when ASUU is on strike for over 200 billion, only one person has stolen 80 billion. God forbid.
|
38
|
Abubakar Ambasador ya ce: "Kai jama'a! Wai su waye za su riƙe amana a wannan kasar de don Allah? Kowa ya samu dama kawai ya kwashe dukiyar ƙasa. Innalillahi Wa'inna Ilaihin Raji'un!
|
Abubakar Ambassador said: "O people! Who will be faithful in this country please? Everyone has the opportunity to plunder the land. Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un!
|
39
|
Hassan Yabour ya ce: "Wato dai kowa jira ya kai ya samu dama a Lanjeriya. Ya Allah ka da ka ba duk mai son satar kudin Lanjeriya damar samun mukami.
|
Hassan Yabour said: "That is to say, everyone should wait for the opportunity in Nigeria. O God, do not give anyone who wants to steal Nigerian money as soon as on gets the chance.
|