1-5
- Alif Lam Mim. --Quran/2/1
- Wannan littafi ne da babu wani kokwanto a cikinsa; shiriya ne ga masu taqawa. --Quran/2/2
- Wadanda suke yin imani da abin da galibi kuma suke tsayar da salla kuma suke ciyarwa daga abin da Muka azurta su da shi. --Quran/2/3
- Wadanda suke yin imani da abin da aka saukar maka da abin da aka saukar a gabaninka, kuma suke sakankancewa da ranar lahira. --Quran/2/4
- Wadannan suna kan (babbar) shiriya daga Ubangijinsu, kuma wadannan su ne masu samun babban rabo. --Quran/2/5
Tafsiri:
Allah swt ya bud'e wannan Sura da harufin Alif da Lam da Mim.