Toggle menu
24.1K
670
183
158.6K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/2/Rijayar Lemo Tafsir

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 06:01, 16 January 2025 by Admin (talk | contribs)

1-5

  1. Alif Lam Mim. --Quran/2/1
  2. Wannan littafi ne da babu wani kokwanto a cikinsa; shiriya ne ga masu taqawa. --Quran/2/2
  3. Wadanda suke yin imani da abin da galibi kuma suke tsayar da salla kuma suke ciyarwa daga abin da Muka azurta su da shi. --Quran/2/3
  4. Wadanda suke yin imani da abin da aka saukar maka da abin da aka saukar a gabaninka, kuma suke sakankancewa da ranar lahira. --Quran/2/4
  5. Wadannan suna kan (babbar) shiriya daga Ubangijinsu, kuma wadannan su ne masu samun babban rabo. --Quran/2/5

Tafsiri:

Allah swt ya bud'e wannan Sura da harufin Alif da Lam da Mim. Ban da ita wannan Sura da akwai surorin Alqur'ani da dama da Allah ya bud'e su da irin wadannan haruffa. Da dama daga cikin malamai suna cewa, Allah ne kad'ai ya san abin da yake nufi da su (only Allah knows the meaning of these disjointed letters). Wasu kuma sun yi qoqarin bayyana ma'anoninsu. Amma magana mafi inganci ita ce, Allah yana nuna mu'ujizar AlQur'ani ne ta hanyar ambaton wadannan haruffa. Domin suna tabbatar wa larabawa cewa babu wanda zai iya kawo wani abu irin Alqur'ani, duk kuwa da cewa haruffansa su ne haruffan da suke magana da rubutu da su.

Allah ya siffanta

Contents