Toggle menu
24.2K
670
183
158.7K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/18/IRIB Hausa Tafsir

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 11:52, 11 March 2016 by Admin (talk | contribs)

IRIB Hausa Tafsir ɗin Suratul Kahf

Links

Suratul Kahfi, Aya Ta 1-6 (Kashi Na 498)

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da muke kawo muku fassarar ayoyin kur'ani mai girma. Da fatan za a kasance a tare da mu a cikin shirin domin aji ci gabansa daga inda mu ka tsaya a baya.

Yanzu sai a saurari aya ta 1 zuwa ta 3 a cikin suratul Kahfi.

الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَنزَلَ عَلَى عَبْدِهِ الْكِتَابَ وَلَمْ يَجْعَل لَّهُ عِوَجَا{1} قَيِّماً لِّيُنذِرَ بَأْساً شَدِيداً مِن لَّدُنْهُ وَيُبَشِّرَ الْمُؤْمِنِينَ الَّذِينَ يَعْمَلُونَ الصَّالِحَاتِ أَنَّ لَهُمْ أَجْراً حَسَناً{2} مَاكِثِينَ فِيهِ أَبَداً{3}

  1. Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya saukar da littafin da babu karkata a cikinsa ga bawansa.
  2. (Littafin ne) mikakke saboda ya yi gargadi mai tsauri daga azabarsa- ubangiji- kuma ya yi bushara ga muminai da su ke yin ayyukan kwarai da cewa suna da kykkyawan lada.
  3. Za kuma su dawwama a cikinsa har abada.

Wannan surar ta fara ne da yi wa Allah godiya saboda saukar da wahayin da ya yi ga manzonsa. Tana kuma koya mana cewa ba saboda ni'imomin abin duniya ne kadai ake yi wa Allah godiya ba, ana yi masa godiya saboda shiriyar da ya yi mana wacce ita ce ni'ima mafi girma. Ni'ima ce wacce ta zo acikin littafin Allah da ya ke na shiriya wanda babu karkata acikinsa. Littafi ne wanda ya ke a mike da ya ke kunshe da bayani akan addini na gaskiya. Sau da yawa a cikin kur'ani ubangiji yana bayyana addini da cewa: Shi ne addini mikakke, yana kuma kiran mutane ne da su bi mikakkiyar hanya ta gaskiya. Hanya ce wacce sako-sako ko wuce gona da iri a cikinta. Kuma ma'aiki yana yi wa mutane gargadi da kuma bushara saboda su kasance cikin fadaka a koda yaushe.

Darussan da su ke a cikin wadannan ayoyi.

  1. Ni'imar kur'ani tana da girman gaske da muhimmanci ta yadda ubangiji ya ke yi wa kansa godiya.
  2. Bushara da gargadi da annabi ya ke yi akan koyarwar da ta zo a cikin kur'ani ne, ba daga gare shi ba ne domin kur'ani shi ne addini mikakke.

Yanzu kuma sai a saurari aya ta 4 da ta 5 acikin wannan sura ta Kahfi.

وَيُنذِرَ الَّذِينَ قَالُوا اتَّخَذَ اللَّهُ وَلَداً{4} مَّا لَهُم بِهِ مِنْ عِلْمٍ وَلَا لِآبَائِهِمْ كَبُرَتْ كَلِمَةً تَخْرُجُ مِنْ أَفْوَاهِهِمْ إِن يَقُولُونَ إِلَّا كَذِباً{5}

    1. Kuma ya yi gargadi ga wadanda su ke cewa Allah ya riki ɗa.
    2. Ba su da masaniya da shi, kuma ba su da masaniya da iyayensu. Kalmar da ta ke fitowa daga bakunansu tana da girma. Abinda su ke fada ba wani abu ba ne face karya.

    Ayoyin da su ka gabata suna magana ne akan gargadi da wa'azi. Amma wadannan ayoyin kuwa suna yin magana ne akan zance mara tushe da ke cewa ubangiji yana da Da. Kirictoci da yahudawa da kuma mushrikai duk sun yi tarayya akan wannan. Mushrikai suna cewa mala'iku 'ya'yan Allah ne, su kuma kiristoci suna cewa Isa ne dan Allah, yayin da yahduawa su ke cewa Uzairu ne dan Allah. Hakikanin gaskiya shi ne cewa wannan irin tunani yana cin karo da akidar tauhidi wanda ya zo a cikin saukakkun littatafai. Darussan da su ke cikin wadannan ayoyin. 1-Fada da gurbatattun akidu wadanda su ke karkatattu shine aiki mai muhimmanci da annabawa su ke yi. 2-Wajibi ne akida ta ginu bisa ginshikin ilimi idan kuwa ba haka ba to za ta kai mutum ga karkacewa. 3-Jahilci da rashin sani ne su ke ingiza mutum ya rika jinginawa ubangiji abubuwan da ba su dace ba. Yanzu kuma sai a saurari aya ta 6 acikin suratu kahfi. فَلَعَلَّكَ بَاخِعٌ نَّفْسَكَ عَلَى آثَارِهِمْ إِن لَّمْ يُؤْمِنُوا بِهَذَا الْحَدِيثِ أَسَفاً{6} "Tamkar kana son ka halaka kanka saboda bakin ciki idan ba su yi imani da wannan zancen ba." Wannan ayar tana kwantarwa da ma'aiki hankali ne dangane da halin mutane. Ya kasance yana yin bakin ciki saboda ganin yadda mushrikai ba su yi imani da zancen gaskiya ba. Yadda ma'aiki ya ke bakin cikin ganin cewa kafirai sun ki yin imani da gaskiyar da ya zo musu da ita, yana yin tsananin da zai iya sanadiyyar mutuwarsa. Yana yin haka ne saboda jin tausayinsa ga mutane da son ganin sun shirya. To wannan ayar ta sauka ne saboda na bashi nutsuwa akan hakan. Darussan da su ke cikin wannan aya. 1-Damuwa akan cewa mutane ba su karfi gaskiya ba wani abu ne mai kima wanda annabawa su ke da shi. 2-Jagororin addini da masu wa'azi wajibi ne a gare su su rika yin kwazon shiryar da mutane da gyara halayensu da akidunsu, koda kuwa ba su sami sakamako na zahiri ba. Karshen wannan shirin kenan sai kuma mun sake haduwa da ku a cikin wani shirin anan gaba.

    Suratul Kahfi, Aya Ta 7-10 (Kashi Na 499)

    Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin da mu ke kawo mu ku fassarar ayoyin kur'ani mai girma.

    Idan kuma ba a mance ba muna cikin suratu kahfi ne da mu ka tsaya a aya ta shida. Da fatan za a kasance a tare da mu domin aji ci gaban shirin daga inda mu ka tsaya a baya.

    Yanzu sai a saurari aya ta 7 da kuma 8 acikin suratu kahfi.

    إِنَّا جَعَلْنَا مَا عَلَى الْأَرْضِ زِينَةً لَّهَا لِنَبْلُوَهُمْ أَيُّهُمْ أَحْسَنُ عَمَلاً{7} وَإِنَّا لَجَاعِلُونَ مَا عَلَيْهَا صَعِيداً جُرُزاً{8}

    "Mune mu ka sanya abinda ya ke kan doron kasa a matsayin ado gare ta, saboda mu jarabce su ko wanene ya fi iya kyautata aiki. Mu ne kuma za mu maida abinda yak e kanta- kasar- ya zama fako busasshe."

    A baya mun ga yadda ma'aiki ya ke nuna matukar damuwa akan rashin imanin mushrikai. Damuwa ce ta mai jin tausayi a gare su saboda sun ki karbar gaskiya. Har ubangiji yana yin magana da shi akan cewa damuwar da ka ke ciki saboda ba su yi imani ta yi tsananin da ka kashe kanka.

    To wannan ayar tana cewa: Ubangiji ya halicci duniya ne a matsayin fage na jarabawa domin kyawun da ta duniyar ta ke da shi yana fisgar wasu su damfaru da ita har su mance da Allah. A cikin wannan halin ne na fisguwa da duniya rayuwa za ta zo karshe ta yadda dukkani abubuwan da su ke masu sheki za su dushe. A hakikanin gaskiya wadannan ni'imomin masu jan hankali suna a matsayin jarabawa ce domin sani ko wanene daga cikin mutanen zai kyautata aikin kwarai. Kuma su wanene su ka nutse wajen aikata barna da fasadi.

    Shakka babu rayuwar ba ta tafiya falle daya, idan wata rana an sha zuma to wata rana za a sha madaci. Idan wani lokacin an sha wahala wani lokacin a sha dadi.

    Saboda haka jarabawa ce da ta ke banbanta daga wani zuwa wani a cikin yanayi irin wannan. Kuma da haka ne ita kanta rayuwar ta ke zama mai ma'ana.

    Darussan da su ke cikin wannan aya.

    1-Kyale-kyalen duniya mai gushewa ne ba shi dawwama. Za a iya amfani da kyale-kyalen duniya domin kyautata ayyuka, amma ba a maida su su zama manufa ta karshe ba.

    2-Duk wata ni'ima da abin duniya suna a matsayin jarabawa ne ga mutum. Domin kuwa duk wani abu da Allah zai baiwa mutum yana tare da nau'i a tare da shi, kuma dole ne ya bada jawabi akansa.

    3-Yadda aka kyautata aiki shi ne mai muhimmanci ya yawansa ba. Ubangiji yana son mu yi aiki mafi kyawu ne, ba aiki mai yawa ba.

    Yanzu kuma sai a saurari aya ta 9 da kuma ta 10 acikin suratu kahfi.

    أَمْ حَسِبْتَ أَنَّ أَصْحَابَ الْكَهْفِ وَالرَّقِيمِ كَانُوا مِنْ آيَاتِنَا عَجَباً{9} إِذْ أَوَى الْفِتْيَةُ إِلَى الْكَهْفِ فَقَالُوا رَبَّنَا آتِنَا مِن لَّدُنكَ رَحْمَةً وَهَيِّئْ لَنَا مِنْ أَمْرِنَا رَشَداً{10}

    "Shin ka san cewa mutanen kogo da Raqimu suna daga cikin ayoyinmu masu ban mamaki? "

    "Yayin da samarin su ka nemi mafaka acikin kogo su ka ce ya ubangijinmu ka bamu rahamarka ka kuma shiryar da mu acikin ayyukanmu."

    Shugabannin kuraishawa sun aike da mutane guda biyu zuwa ga yahudawa domin su yi musu nazari da bincike dangane da annabin musulunci. Su kuwa su ka fada musu cewa ku yi masa tambayoyi guda uku idan ya har ya ba ku jawabi ingantacce to ku tabbata annabi ne. Idan kuwa bai baku jawabi ingantacce ba to makaryaci ne.

    Tambaya ta farko ita ce dangane da wasu samari da su ka kauracewa mutanensu, sai ku ji ko ya makomarsu ta kasance?

    Manzon Allah ya fada musu cewa: Gobe zan ba ku jawabi sai dai bai hada da fadin cewa: Insha Allahu ba. Sai da aka dauki kwanaki goma sha biyar sannan jibrilu ya sauka ga manzon Allah.

    Mutanen kogo, wato ashabul-kahafi, wasu samari ne masu imani da su ke rayuwa cikin ni'ima da jin dadi na abin duniya. Sai dai domin kare akidarsu ta tauhidi sun juyawa duniya baya su ka fake acikin kogo. Cikakken bayani akan abinda ya faru da wadannan samarin bayan shigarsu cikin kogo zai zo a ayoyi masu zuwa.

    A kusa da wannan suna na ma'abota kogo sunan Raqimu ya zo. Suna ne na wuri da kuma kogon da ma'abota kogon su ka fake acikinsa. Saboda haka ana kuma kiransu da sunan ma'abota Raqimu.

    An kuma rubuta sunayensu ajikin allon da aka kafe a bakin kogon da su ka fake acikinsa. Domin kuwa kalmar raqim tana nufin rubutu.

    Kamar yadda ya zo acikin littatafan tarihi mutanen kogo sun rayu ne bayan annabi Isa a garin da ya ke a karkashin ikon daukar Roma. Kuma dagutun da ya ke mulki a wancan lokacin shi ne Daqayanusu.

    Alkur'ani mai girma a cikin wadannan ayoyin ya bayyana cewa mutanen kogo sun yi hijira ne zuwa kogo domin su kare addininsu da imaninsu. Ya kuma bayyana su a matsayin samari wanda ya ke nufin masu jarunta ba nuni ne da shekarunsu ba.

    Imam ja'afar sadiq ya bayyana cewa: Wasu daga cikinsu suna da shekaru masu yawa, amma saboda imanin da su ke da shi ne aka ambace su da samari.

    Labarinsu a cikin kur'ani ya fara ne daga kan hijirarsu zuwa cikin kogo. Bai yi magana akan rayuwarsu ta baya ba. Sai dai addu'ar da su ka rika yi tana nuni da cewa suna son ka iwa ga kamala ne da samun shiriya. Ba saboda neman abin duniya ko mukami na siyasa ba ko wani dalili da ya ke sa mutum ya kauracewa mutanensa. Suna neman hanyar tsira a wurin Allah da son kare akidarsu.

    Darussan da su ke cikin wannan aya.

    1-Kare addini, shi ne mafi muhimmanci daga kare gida da iyali. Idan har ya zama wajibi sai an yi hijira to dole a yi ta duk da matsalolin da su ke cikinta.

    2-Addu'a tana da ma'ana idan an hada ta da aiki. Mutanen kogo sun yi hijira sannan su ka yi addu'a, ba zama su ka yi su ka mika hannu ba suna addu'a kadai ba tare da aiki ba.

    3-A cikin koyarwa ta addini samartaka tana nufin sadaukar da kai domin kare addini da yin hijira daga cikin gurbatacciyar al'umma domin kiyaye addini.

    Karshen shirin namu kena sai kuma wani lokacin idan mun sake haduwa.