Toggle menu
24K
669
183
158.3K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

part of speech

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

Noun

Singular
part of speech

Plural
parts of speech

  1. The parts of speech are a traditional grouping of word classes into: noun, pronoun, verb, adjective, adverb, preposition, interjection, conjunction, and sometimes article.

Synonyms

Related words

Darasi a kan "Parts of Speech" (Rabe-raben Kalmomi Cikin Jumla)

A yau za mu fara karatu a kan ‘Parts of Speech,” wato yadda julma ya rarraba, ko kuwa mu ce rabe-raben kalmomi cikin jumla.

Farawa a kan wannan yana da muhimmanci saboda duk magana da mutum zai yi, zai gina tana a kan jumla. Saboda haka, idan mai karatu ya san yadda jumla ya rarraba, zai ba shi saukin yadda zai gina na shi jumlar.

Bisa mashahurin bayanai na masana harshen Turanci, kalmomi cikin jumla sun rarraba har zuwa ababuwa guda takwas. Ma’ana idan mutuum ya gina jumla, rubuta wa ya yi ko furtawa, a na iya samun wadannan ababuwa guda takwas ko kasa da haka. Ba dole a samu dukkaninsu ba, amma dole ne ya zamo an samu wasu da ga cikinsu. Wadannan ababuwa sune:

  1. Noun (Suna)
  2. Pronoun (Wakilin suna)
  3. Adjective (Siffan suna)
  4. Verb (Aiki/Fi’ili)
  5. Adverb (Siffan aiki/fi’ili)
  6. Preposition (kalma ce da ke yawan zuwa kafin suna – za mu yi cikakken bayaninta a gaba)
  7. Conjuction (Kalma mai hada sunaye – shima bayaninsa zai zo a nan gaba)
  8. Interjection (Motsin rai)

A takaice, za mu iya cewa darasinmu na yau ya kasance a kan rarrabuwan kalmomi cikin jumla, wanda kamar yadda muka yi bayani, sun rarrabu har gida takwas kamar yadda muka kawo su a lissafe.

(Source / daga: https://www.bakandamiya.com/group/topic/view/38/6/darasin-farko-parts-of-speech-rabe-raben-kalmomi-jikin-jumla)

Part of speech defined

Part of speech is a group to which each word is assigned in accordance with its syntactic function. In grammar each word is allocated in its grammatical class. Since we are in primary school, our teachers taught us noun, pronoun, verb, adverb, adjectives, conjunction, interjection, preposition, this is part of speech, English words occupied in these classes of words.

SASSAN MAGANA

(PART OF SPEECH) Sassan magana (Part of Speech) wani bangare ne da ake jera kalmomi a sassa daban-daban da ake amfani dasu wajen yin magana ta yadda zasu tafi da ma’anar kalmomin cikin jimla da zance, don haka a nahawun turanci ko wace kalma ana ajeta a sashen nahawunta don amfani a wannan sashe ta kuma bayar da ma’ana. Duk Kalmar da aka xauka aka kai sashen da ba nata ba, babu wata rawar da zata iya takawa sai ma ta vata nahawun zancen.

In zamu iya tunawa tun lokacin muna firamari malamanmu turanci sun sha koya mana me ake nufi da suna (noun) wakilin suna (pronoun) aikatau (Verbs) siffatau (Adjectives) bayyanau (Adverbs) mahada (Conjection) nuna dangantaka (Preposition) waxannan su ne sassan magana (Part of Speech) da muke amfani dasu a turanci.

Source: https://www.facebook.com/groups/548563591918234/permalink/3472167079557856/