113
Links for Surat Al-Falaq (The Daybreak)
- http://legacy.quran.com/113
- http://www.islamicstudies.info/tafheem.php?sura=113&verse=1&to=5
- https://archive.org/details/SurahAlFalaqdaybreak-MiracleDreamTafseer-NoumanAliKhan, Audio 1, Audio 2
- قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ Qul a’uzu birabbil falaq <> Say: I seek refuge in the Lord of daybreak. <> Ka ce: Ina neman tsari ga Ubangijin safiya.
- مِن شَرِّ مَا خَلَقَ Min sharri ma khalaq <> From the evil of that which He created. <> Daga sharrin abin da Ya halitta.
- وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ Wa min sharri gawsiqeen iza waqab <> And from the evil of darkness when it settles. <> Da sharrin dare, idan ya yi duhu.
- وَمِن شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ Wa min sharrinnaffa thaati fil uqad <> And from the evil of the blowers in knots <> Da sharrin mata masu tofi a cikin ƙulle-ƙulle.
- وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ Wamin sharri hasidin iza hasad <> And from the evil of an envier when he envies. <> Da sharrin mai hasada idan ya yi hasada.
DARUSSA DAGA 113-SURATUL FALAƘ
Mabuɗin Sura: 1. Sunanta: Wannan Sura ta shahara da suna 'Suratul Falaƙ', saboda kalmar 'Al-Falaƙ' da ta zo a ayarta ta farko. Amma a mafi yawan hadisai da maganganun sahabbai an kira ta da 'Suratu Ƙul A'uzu Bi Rabbil Falaƙ'.
2. Sanda Aka Saukar Da Ita: Sura ce Makkiyya bisa magana mafi inganci.
3. Jerin Saukarta: Ita ce Sura ta ashirin (20) a jerin saukar surorin Alƙur'ani, ta sauka bayan 'Suratul Fili' kafin 'Suratun Nasi'.
4. Adadin Ayoyinta: Ayoyinta biyar ne (5).
5. Falalarta: Hadisai da yawa sun inganta game da falalarta tare da 'Suratun Nas' da 'Suratul Ikhlas'; daga cikinsu akwai: • Hadisin A'isha (ra) inda ta ce: Annabi (saw) ya kasance a duk dare idan ya zo kwanciya sai ya haɗa tafukan hannayensa biyu, ya yi tofi a cikinsu, sai ya karanta 'Ƙul Huwallahu Ahad' da 'Ƙul A'uzu Bi Rabbil Falaƙ' da 'Ƙul A'uzu Bi Rabbin Nasi' sannan ya shafe jikinsa gwargwadon ikonsa da su; yana farawa ta kansa da fuskarsa da gaban jikinsa, yana yin haka har sau uku. [Bukhari #5017 da Abu Dawud #5056 da Tirmizi #3399].
• An karɓo daga Aliyyu ɗan Abu Ɗalib (ra) ya ce: Kunama ta harɓi Manzon Allah (saw) yana cikin salla, yayin da ya gama sai ya ce: "Allah ya la'anci kunama, ba ta ƙyale mai salla ba balle waninsa." Sai ya nemi a kawo masa ruwa da gishiri, sai ya riƙa shafa su a wurin harɓin yana karanta 'Ƙul Ya Ayyuhal Kafirun' da 'Ƙul A'uzu Bi Rabbil Falaƙ' da 'Ƙul A'uzu Bi Rabbin Nas'. [Ɗabarani, Al-Mu'ujamus Saghir, shafi na 117. Dubi, Al-Bani, As-Sahiha #548].
•An karɓo daga Uƙuba ɗan Amir (ra) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: "Ya Uƙuba ɗan Amir, yanzu ba na sanar da kai wasu surori waɗanda ba a saukar da kamarsu ba a cikin Attaura da Linjila da Alƙur'ani ba? Kada ka bari wani dare ya wuce ka sai ka karanta su a cikinsa, su ne, 'Ƙul Huwallahu Ahad' da 'Ƙul A'uzu Bi Rabbil Falaƙ' da 'Ƙul A'uzu Bi Rabbin Nas'. [Ahmad #17452].
6. Dalilin Saukarta: Zaidu ɗan Arƙam (ra) ya ruwaito cewa, akwai wani Bayahude da yake zaune wajen Annabi (saw), yana shiga har cikin gidansa, (wato kafin a saukar da ayar hijabi). Annabi (saw) ya amince masa, to amma sai ya yi wa Manzon Allah (saw) wasu ƙulle-ƙullen sihiri ya jefa a cikin rijiyar wani mutumin Madina, sai Manzon Allah (saw) ya kamu da rashin lafiya na tsawon wata shida. Sai wasu Mala'iku biyu suka zo duba shi, ɗaya ya zauna a daidai kansa, ɗayan kuma ya zauna a daidai ƙafafunsa. Sai ɗaya ya tambayi ɗan'uwansa: "Ka san mene ne rashin lafiyarsa?" Sai ya amsa masa cewa: "Ai mutumin nan 'wane' ne da yake zuwa wajensa shi ne ya yi masa wasu ƙulle-ƙulle ya jefa a cikin rijiyar 'wane' mutumin Madina. Da a ce zai aika wani zuwa wannan rijiya don ya samo ƙulle-ƙullen, da zai ga ruwan rijiyar ya yi fatsi-fatsi. Sai Mala'ika Jibrilu (as) ya zo masa da ƙula'uzai biyu, ya faɗa masa cewa: " 'Wane' Bayahude, shi ne ya yi maka sihiri, sihirin kuma yana can cikin rijiyar 'wane'. Sai Manzon Allah (saw) ya tura Aliyyu (ra), da ya je ya sami ruwan wannan rijiya ya yi fatsi-fatsi, ya kuma ciro waɗannan ƙulle-ƙulle ya kawo wa Manzon Allah (saw), sai Jibrilu (as) ya umurce shi ya kwance ƙulli ɗaya ya karanta aya ɗaya. Yana yi sai ya fara jin sauƙi. Duk sanda ya kwance ƙulli ya karanta aya ɗaya sai sauƙin yana ƙaruwa, haka ya yi ta kwance su ƙulli-ƙulli yana karanta musu aya ɗaya-ɗaya, yana gamawa sai ya ji ya warke gaba ɗaya, ya miƙe cikin nishaɗi kamar ba abin da ya taɓa samun sa. [Dubu, Ɗabarani, Al-Mu'ujamul Kabir #5011 da 5013 da 5016 da Ahmad #19267 da Nasa'i #4080].
7. Babban Jigonta: Tana umurni da neman tsarin Allah (swt) daga duk wani sharri na sarari da na ɓoye.
Ref [1]: Fayyataccen Bayani na Ma'anoni da Shiriyar Alƙur'ani na Dr. Muhammad Sani Rijiyar Lemo, shafi mai lamba 907-909.