Toggle menu
24.1K
670
183
158.5K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

hausaradio/2022-06-11

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

VOA Hausa Safe [1]

Host: Muhammad Hafiz Baballe (intro), Sarfilu Hashim Gumel (world news 0:53-6:00)

  1. Yayin da mamayar Rasha ta yi wa Ukraine ya shiga na wata na huɗu, jami'an Ukraine sun ƙara damuwa cewa ƙasashen yamma, na iya fuskantar gajiyar yaƙi. Suna fargabar cewa Rasha za ta iya amfani da wannan damar wajen tirsasa/tursasa wa Ukraine tasasanta. Lamarin da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya bujirewa, yana mai cewa za ta bi ƙa'idojinta na zaman lafiya. Gajiyar dai na ƙaruwa, mutane suna son wani nau'i na sakamako wanda ke amfani ga kansu. Kuma muna son wani sakamako kam inji shi. A halin da ake ciki kuma, ana cigaba da gwabza faɗa a yau Jumu'a domin neman iko da birnin Severodonetsk. Jami'an Ukraine sun ƙara yin kira da a ƙara taimaka musu da makamai da suka haɗa da roka da manyan bindigogi daga ƙasashen yamma.
  2. A ɗaya ɓangaren kuma, matsalar abinci na ƙaruwa a duniya, sakamakon yaƙin da ake yi a ƙasar Ukraine a cewar masana. Inda ake sa ran Afrika, za ta fi fuskantar matsala. Manyan ƙasashen duniya, China da Amurka, sun ce suna ƙoƙarin datsale matsalar. Amma a lokaci guda, suna zargin juna da ta'azzara rikicin. Wata jaridar ƙasar, The China Daily, ta ɗora alhakin lamarin a wani ɓangare kan Washington. Tana mai cewa: farashin abinci ya kai ƙoƙoluwar da ba a taɓa gani ba, yayin da takardar alkamar Rasha da ta Ukraine ke fuskantar cikas a tashar jiragen ruwa da kuma takunkumin da ƙasashen yamma suka ƙaƙaba. A nata ɓangaren, ƙasar Amurka ta zargi ƙasar China da yin katsa-landan/katsalandan, bayan da shugaban ƙasar Xi Jinping, ya bayyana a farkon wannan shekarar cewa: "Batun samar da abinci a ƙasar China, shi ne abin da ya fi ɗaukar hankali." Kuma ya buƙaci manoma da su ƙara yawan noma domin tabbatar da ƙasar da ta fi yawan al'umma a duniya ta dogara da kanta.
  3. Yaƙi da hauhawar farashin kayayyaki, ya sa 'yan Zimbabwe na ƙirga yatsun su na ƙafa yayin da suke fafutukar/fafitikar sayen abinci ga iyalansu. Wata jita-jita ta yanar gizo da ta ɓarke a ƙasar cewa: mutane masu tsananin buƙata suna sayar da yatsunsu a biya su kuɗi. Rahoton na ƙarya ya haɗu sosai, har mataimakin ministan yaɗa labaran ƙasar, Paradza [2], ya ziyarci masu sayar da kayayyaki akan tituna a tsakiyar birnin Harare, a farkon wannan watan don ƙaryata wannan jitajita. Ɗaya bayan ɗaya, 'yan kasuwar sun cire takalmansu domin nuna cewa suna da yatsun su goma bakiɗaya... yayin da kafafen yaɗa labarai na ƙasar Zimbabwe suka yi na binciken ta hoton bidiyo.
  4. Shugaban Amurka Joe Biden ya ce gwamnatinsa na yin duk mai yiyuwa wajen ganin an shawo kan hahawar farashin kayayyaki.