Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

hausaradio/BBCHausa20190522

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

Media

  1. BBC Hausa Shirin Safe with host (mai gabatar da shirin) Fauziya Kabir Tukur (@fawzeyah) [1]
  2. BBC Hausa Shirin Hantsi with Fauziya Kabir Tukur [2]
  3. BBC Hausa Shirin Rana with Jabir Mustapha Sambo [3]
  4. BBC Hausa Shirin Yamma with Jabir Mustapha Sambo

Labaran Talabijin: Tarzoma ta barke a birnin Jakarta don nuna adawa da sake zaben shugaban Indonesiyar. [4][5]

BBC Hausa Headlines for Wednesday May 22nd 2019

  1. UK: Firam ministan Birtaniya, Theresa May, za ta gabatar da sabon shirinta na yarjejeniyar ficewar k'asar daga tarayyar Turai yau a gaban majalisa a k'ok'arin ganin yarjejeniyar ta samu karb'uwa. [6]
  2. 🇳🇬 Nigeria: A Najeriya, babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ta ce ba wani bane ya jefa k'asar cikin matsalar tsaron da ake fama da ita illa gwamnati karan kanta [7]:
    "Kullun abin da ake gwadawa mutane cewa ainihin tashin hankalin bai kai yadda ake tsammani da shi ba."
  3. An ce wai komai ya yi farko zai yi k'arshe. Shekara tara bayan fara fim d'innan mai dogon zango na k'asar Amirka, mai suna Game of Thrones da ya yi fice a fad'in duniya. An saki b'angaren k'arshe na shirin mai d'auke da abubuwan ban al'ajabi. Toh sai dai b'angaren ya dawo cece-kuce a tsakanin masu kallon shirin. [8][9][10]
    1. "Na yi farin ciki da yadda aka k'are Brandon Stark shi ne ya cancanci ya hau kujerar mulki saboda shi kad'ai ya san tarihi."
    2. "Gaskiya dai ni, yadda ya k'are, ban ji dad'in haka ba ko kad'an. John Snow daga farko, na so a ce shi ne ya zamanto ya yi taken over iron throne d'innan."
  4. 🇸🇩 Sudan: Toh ana cigaba da matsawa gwamnatin rik'en k'warya ta soji a Sudan kan ta sake komawa kan teburin shawara da jagororin masu zanga-zanga bayan tattaunawar ta samu tsaiko a ranar Talata.
  5. 🇾🇪 Yemen: Shugaban shirin samar da abinci na majalisar d'inkin duniya, ya ce k'ananan yara na mutuwa a Yemen saboda wasu jami'ai da sukan karkatar da kayan agaji masu muhimmanci.
  6. 🇳🇬 Nigeria: A Najeriya, majalisar wakilan k'asar, ta karb'i rahoto akan wani k'udurin doka da ke buk'atar a haramta amfani da jakar leda wajen gudanar da harkokin yau da kullun.
  7. 🇳🇬 Nigeria: Matasa maza da mata ne a Najeriya ke rungumar sana'a a hannu bibbiyu, inda sukan zamanantar da wasu tsoffin sana'o'in don dogaro da kai.
    "Ina yin Arabian, wato na Larabawa ke nan. Ina yin na Indian na Indiyawa. Ina na Chinese, mutanen k'asar Sin. Kala-kala dai. Ba irin wanda ba na yi saboda ina son girki. Duk inda na je, duk k'asar da na je, sai na shiga cikin su na koyi wani abu. Sannan sai kuma in k'ara da nawa."
  8. 🇬🇦 Gabon: Shugaban k'asar Gabon, ya sanar da sauke mataimakinsa da ma wani minista. Za mu ji mai ya yi zafi.
  9. 🇳🇬 Nigeria: A daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan yawan tafiye-tafiyan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, k'asar ta sanar da rufe ofisoshin jakadancinta a wasu k'asashen duniya. Toh ko ya ya masana ake kallon wannan mataki?
    "In su suna da ofisoshin su a nan Najeriya, watak'ila rufewa su ma za su yi. Abin da ake kira tit-for-tat: in kai mini, ni ma in yi maka."
  10. 🇬🇭 Ghana: Toh muna ɗauke da hira da wata 'yar wasan ƙwallon zari-ruga (rugby) a Ghana, wadda ta ke wasan da hijabi. (za ku iya kallon labarin a bidiyo)
    "In dai abin bai hana ni kan addini ba, in dai abinnan bai hana kan... kar ki yi sallah, kar ki yi hijabin ki don na samu matsala a wurinnan... Amma tunda dai abin bai ce... na yi salla na. Na yi in sa kaya na yadda ya kamata. Kowa ba perfect ba ne."
  11. 🇪🇺 EU: Yayin da miliyoyin mutane a faɗin Turai za su kaɗa ƙuri'arsu a zaɓen majalisar dokokin nahiyar a gobe. Wasu da ke so a dama da su, sun ce banbancin launin fata bai kare musu gwiwa ba.
    "Muna da matsalar nuna banbancin launin fata. Wannan abu ne da na taso a cikinsa tun farkon rayuwata. Amma ganin wasu a cikin mu na kaiwa ƙololuwa, hakan zai ƙarfafa gwiwar matasa da dama a faɗin turai."
  12. 🇳🇬 Nigeria: Majalisar ministocin Najeriya ta yi zamanta na bankwana a yau, gabanin ƙarewar wa'adin farko na mulkin shugaba Muhammadu Buhari. Toh ko yaya wasu daga cikin ministocin suka ji?
    "Wannan jagorancin da aka ba mu girma ne sosai da ba ka gane muhimmancin shi sai kana cikin shi. Muna fatan kuma da cewa mai girma shugaban ƙasa zai kammala alƙawarin shi."
  13. 🇿🇼 Zimbabwe: A Zimbabwe kuwa, wasu mutane biyar ne aka gurfanar a gaban kotu da laifin yunƙurin yin juyin mulki.
  14. 🇺🇬 Uganda, 🇰🇪 Kenya: A Afrika, akwai d'umbin mata masu aikatau. Za mu ga wasu 'yan Uganda da suka je Kenya neman aiki. (za ku iya kallon labarin a bidiyo)