Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

voa60/2020-10-16

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

VOA60 Africa for Friday (Juma'a) Oct 16th, 2020

English [1] Hausa [2] [3]

  1. VOA60 Afirka for Friday (Juma'a) Oct 16th, 2020
    1. Guinea: Supporters of the Union of Democratic Forces of Guinea (UFDG) greet the candidate of the opposition party, Cellou Dalein Diallo, in the capital, Conakry, for the campaign's final stretch before the Sunday election.
      A Guinea, magoya bayan jam'iyyar adawa ta UFDG sun karɓi ɗan takararsu Cellou Dalein Diallo, a ranar ƙarshe ta kamfe kafin zaɓen ranar Lahadi. --voa60/2020-10-16

    2. Ivory Coast: Two main opposition candidates call on their supporters to "actively boycott" the "electoral process" ahead of the October 31 presidential election, at a press conference by former prime minister Pascal Affi N'Guessan and former president Henri Konan Bédié.
      Manyan 'yan takarar jam'iyyar adawa biyu a Ivory Coast, tsohon firam minista da tsohon shugaban ƙasa sun yi kira ga magoya bayansu da su ɗaura cewa duk wata harkar zaɓe, gabanin zaɓen shugaban ƙasa na ranar 31 ga watannan... --voa60/2020-10-16

    3. Angola: President João Lourenço arrived in a socially distanced National Assembly building for the start of a new session of parliament Thursday.
      Shugaban ƙasar Angola Joao Lourenco, ya isa ginin majalisar dokokin ƙasar da aka bada tazara na fara sabon zama na 'yan majalisar ƙasar. --voa60/2020-10-16

    4. South Africa: Black protesters led by South Africa's Economic Freedom Fighters (EFF) party marched Friday toward the Magistrate Court in town of Senekal, where two suspects were to appear for a hearing on a murder of a white farmer. The case reignited racial tensions in the country.
      Masu zanga-zanga baƙaƙen fata ƙarƙashin jagorancin jam'iyyar EFF a Afirka ta Kudu, sun yi tattaki zuwa kotun majistiri a garin Senekal, inda wasu mutane biyu za su bayyana a wata shari'a kan kisan wani manomi farar fata. --voa60/2020-10-16

    5. Egypt: Designer Ashgan al-Abhar is catering to people with disabilities with clothes that fit their needs amid a lack of options in commercial retail stores.
      Mai yin kayayyakin ƙawa a Masar a Ashgan al-Abhar na yi wa nakasassu abinci tare da tufafi da zai dace da buƙatun su, yayin da ba su da zaɓi a shagunan sayar da kaya. --voa60/2020-10-16

VOA60 World for Friday (Juma'a) Oct 16th, 2020

English [4] Hausa [5] [6]

  1. VOA60 Duniya for Friday (Juma'a) Oct 16th, 2020
    1. Thailand: Thai police fired stinging liquid from water cannon at thousands of Thai protesters on Friday in the most violent escalation of three months of demonstrations against the government of Prime Minister Prayuth Chan-ocha.
      'Yan sanda a Thailand, sun harba wani ruwa mai zafi kan dubban masu zanga-zangar adawa da gwamnatin firam minista Prayuth Chan-ocha wadda ta rikiɗe zuwa tashin hankali... --voa60/2020-10-16

    2. Russia: President Vladimir Putin proposed on Friday that Russia and the United States extend the new START arms control treaty that expires in February for at least a year without imposing any conditions.
      Putin ya bada shawarar cewa Rasha da Amurka su tsawaita yarjejeniyar sarrafa makamai ta START da za ta ƙare a watan Febrairu ba tare da ginda* wani sharaɗi ba. ... --voa60/2020-10-16

    3. Vietnam: Thirteen bodies were recovered from a landslide triggered by torrential rains that flooded part of central Vietnam, killed at least 36 people and left a dozen others missing since last weekend
      An gano gawarwaki 13 daga wurin da ƙasa ta daftare sanadiyyar ruwan sama mai ƙarfi a tsakiyar Vietnam. Mutane 36 ne suka mutu. Wasu da dama ne suka ɓata tun a makon da ya wuce. --voa60/2020-10-16

    4. Spain: People working in the hospitality industry take to the streets in Barcelona after the regional government of Catalonia announced that bars and restaurants are to be closed across the region for the next 15 days to slow rising coronavirus infections.
      A Spain, mutane da ke aiki a ɓangaren yawon buɗe ido sun fito kan tituna a Barcelona, bayan da gwamnatin yanki ta Catalonia ta sanar da cewa za ta rufe shagunan barasa da na abinci don rage Coronavirus. --voa60/2020-10-16

    5. Switzerland: Anti-viral medication remdesivir was found to have little or no effect on COVID-19 patients' length of hospital stay or chances of survival, according to a clinical trial by the World Health Organization.
      An gano cewa maganin remdesivir bai da wani tasiri sosai akan marasa lafiyar COVID-19 da suke kwance a asibiti, a cewar wani gwaji a asibiti na hukumar lafiya ta duniya. --voa60/2020-10-16