Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

aikatau

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Revision as of 16:46, 15 November 2020 by Admin (talk | contribs) (Noun)
(diff) ← Older revision | Latest revision (diff) | Newer revision → (diff)

Noun

Tilo
aikatau

Jam'i
babu (none)

Singular
verb

Plural
verbs

m

  1. wani aiki da za a yi don samun abin masarufi
    1. Nijar Ben Omar ya ziyarci kasar ta Saudiya inda suka gana da mata ‘yan Nijer masu aikatau da suke ciki a wuraren da suke aikatau saboda tsananin wahalar aiki da cin zarafi yayinda [1]
    2. haramtawa mutane shigar da yara kanana aikatau da duk wasu al’amuran muzgunawa rayuwar Alhaji kabir Alhassan Rurrumi shugaban masu rijaye na majalisar yace " wanna doka ta magana [2]
    3. Makonni kusan biyu kenan da ma'aikatar kwamishinar al'amuran mata da bunkasar walwalar aure, da barace-barace, da tallace-tallace, da aikatau da dai makamantan su. [3]
    4. Ma’aikatar Al’umuran Mata da Walwalar Jama’a ta kaddamar da yekuwa kan illar fitsara da ce yawan tallace-tallace da barace-barace da aikatau na ‘ya’ya mata [4]
  2. kalma mai bayyana aiki a nahawu. <> verb, verbs.
  3. aikatau is the past tense of aikata
  4. koda - sana'ar dakau ko niƙau.

Glosbe's example sentences of aikatau

  1. aikatau. <> form, verb, verbs.
    1. Mecece ma’anar aikatau na Ibrananci da aka juya “saurara” da kuma ‘tarar da’ a Kubawar Shari’a 28:2? <> What is the meaning behind the Hebrew verbs rendered “keep listening” and “overtake” at Deuteronomy 28:2?
    2. Maimakon su ce “samun sanin” Allah, suka fassara aikatau ɗin “san” Allah ko kuma “sanin” Allah. <> Instead of saying “taking in knowledge” of God, they simply render the verb “to know” God or “knowing” God.
    3. An yi amfani da wannan aikatau, “sauri” sau huɗu game da wannan matar a labarin. <> Four times in this one account we find the same verb, “to hasten,” used regarding this woman.
    4. 2 Aikatau na Ibrananci da aka juya “saurara” a Kubawar Shari’a 28:2 na nufin ci gaba da sauraro. <> 2 The Hebrew verb rendered “keep listening” at Deuteronomy 28:2 denotes continuous action.
    5. Amma wata majiya ta ce: “Aikatau na Helenanci mai nuna sa’in da ake ciki, yana ba da umurnin da ke nuna cewa a daina wasu ayyukan da aka soma.” <> One reference work says: “The Greek verb tense is a present imperative, implying a command to stop doing some action already in progress.”
    6. Game da siffar aikatau da aka fassara ‘ruɗi’ a Ru’ya ta Yohanna 12:9, wata majiya ta ce “yana nuna abin da ake ci gaba da yi ne ya zama halin mutum.” <> Regarding the form of the verb rendered “is misleading” at Revelation 12:9, one reference work says that it “indicates a continuous action that has become a habitual character.”
    7. Ƙamus na Vine’s Expository Dictionary of New Testament Words ya ce, “a zaman aikatau wannan kalmar tana nufin maganin da ke kawar da ƙaiƙayi.” <> According to Vine’s Expository Dictionary of New Testament Words, “a verbal form of the word signifies medicines which allay irritation.”
    8. Aikatau na yare na asali da aka yi amfani da shi a nan yana nufin ci gaba da aiki. <> The original-language verb used here denotes continuous action.
    9. Aikatau da aka haɗa da shi wasu lokatai ana amfani da shi cikin Littafi Mai Tsarki game da hidima wadda mutum yake wa kansa, irinsu ba mutane abinci. <> The verb associated with it is sometimes used in the Bible with regard to personal services, such as waiting at tables.
    10. Aikatau na Ibrananci da aka fassara ‘tarar da’ an gano cewa furci ne na farauta wanda sau da yawa yana nufin “a kama” ko “a kai ga.” <> The Hebrew verb translated “overtake” has been identified as a hunting term most often meaning “to catch up with” or “to reach.”
    11. 17 Aikatau na Ibrananci da aka fassara “zan tuna” yana nufi fiye da kawai tuna abin da ya wuce. <> 17 The Hebrew verb rendered “I shall remember” implies more than simply to recall the past.
    12. Kalmar aikatau phi·leʹo, mai nufin “ka so wani, ka yi muradin wani, ka so (kamar yadda wani zai ji game da aboki na kud da kud ko kuma ɗan’uwa),” an yi amfani da ita sau da yawa a cikin Nassosin Helenanci na Kiristoci. <> The verb phi·leʹo, meaning “to have affection for, to be fond of, or to like (as one might feel about a close friend or a brother),” is used often in the Christian Greek Scriptures.
    13. Aikatau na Ibrananci da aka fassara “daskare” yana nufin ya yi kauri. <> The Hebrew verb translated “congealed” means to shrink or thicken.
    14. Aikatau na Helenanci da aka fassara “biɗan aiki” yana nufin mutum ya miƙa hannunsa don ya ɗauki wani abin da hannunsa bai kai ba. <> The Greek verb translated “reaching out” means stretching to grasp something, perhaps something beyond your normal reach.
    15. Sau huɗu a wannan labarin mun ga wannan aikatau, “sauri,” da aka yi amfani da shi game da wannan matar. <> Four times in this one account we find the same verb, “to hasten,” used regarding this woman.
    16. 19, 20. (a) Mecece ma’anar aikatau na Ibrananci da aka fassara “yi jinƙai” ko kuma “ji tausayi”? <> 19, 20. (a) What is the meaning of the Hebrew verb rendered “show mercy” or “have pity”?
    17. A cikin Nassosi, aikatau na Ibrananci da na Helenanci da suke da ma’ana ta juyowa suna da ma’anar juya baya, sake juyawa. <> In the Scriptures, Hebrew and Greek verbs pertaining to conversion have the sense of turning back, turning around.
    18. 10 Kalmar aikatau ta Ibrananci da aka fassara ‘yin tunani’ tana nufin “bin abu a zuciya.” <> 10 The Hebrew verb translated “concern [oneself]” also means “meditate, muse,” “go over a matter in one’s mind.”
    19. Wani littafin bincike ya bayyana cewa: “Aikatau na Ibrananci na kalmar nan ji yana kuma nufin matakan da aka ɗauka a sakamakon hakan.” <> One reference work explains: “Hebrew verbs for feelings sometimes refer as well to the actions that result from them.”
    20. ‘Mutum ya yi tsayin daka, tsaya da aminci, ko kuma nacewa’ shi ne abin da aikatau na Helenanci da ake yawar fassara shi “jimrewa” yake nufi cikin Littafi Mai Tsarki. <> ‘Standing one’s ground, remaining steadfast, or persevering’ is the thought behind the Greek verb often translated “endure” in the Bible.
    21. (2 Timothawus 2:15) Furcin nan “rarrabe . . . sosai” daga kalmar aikatau ne na Helenanci mai goyo da ainihi take nufin “yanka a miƙe,” ko kuma ‘a yanka babu karkata.’ <> (2 Timothy 2:15) The expression “handling . . . aright” is from a compound Greek verb that originally meant “straightly cutting,” or ‘to cut straight.’
    22. An ɗauko sunan daga aikatau na Ibrananci da ke nufi “yana zama.” <> Commonly translated “Jehovah, the divine name comes from a Hebrew verb that can describe action and can be translated “to become.”
    23. Wannan kalmar ta kusa da ta ƙarshen ta fassara aikatau na Helenanci da yake nufin “gogewa, . . . kashe ko kuma halaka.” <> That last phrase translates a Greek verb that can mean “to wipe out, . . . cancel or destroy.”
    24. Wani littafin neman bayani ya yi bayani cewa aikatau ra·chamʹ “yana nuna juyayi mai zurfi kuma mai taushi, kamar wanda yake zuwa idan aka fuskanci kasawa ko kuma wahalar waɗanda muke ƙauna ko kuma waɗanda suke bukatar taimakonmu.” <> One reference work explains that the verb ra·chamʹ “expresses a deep and tender feeling of compassion, such as is aroused by the sight of weakness or suffering in those that are dear to us or need our help.”
    25. Alal misali, aikatau na Ibrananci ra·chamʹ ana yawan fassara shi “yi jinƙai” ko kuma “ji tausayi.” <> For example, the Hebrew verb ra·chamʹ is often rendered “show mercy” or “have pity.”


Google translation of aikatau

Business, labor.