Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

voa60/2020-10-28

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

voa60/2020-10-26 > voa60/2020-10-28

VOA60 World for Wednesday (Laraba) Oct 28th, 2020

English [1] Hausa [2] [3]

  1. VOA60 Duniya for Wednesday (Laraba) Oct 28th, 2020 [4]
    1. Nigeria: Authorities report that at least 13 states have established judicial panels to hear complaints about police brutality and the shooting of protesters in independent investigations pushed by protesters to demand the end of a police branch called the Special Anti-Robbery Squad (SARS).
      Hukumomi a Najeriya, sun sanar da cewa aƙalla jihohi 13 sun kafa kwamitotin shari'a don sauraron ƙorafe-ƙorafe kan cin zalin jama'a da ake zargin 'yan sanda. --voa60/2020-10-28

    2. United States: U.S. Secretary of State Mike Pompeo meets Sri Lankan Foreign Minister Dinesh Gunawardena and says that the Chinese Communist Party is a "predator" violating Sri Lanka's sovereignty.
      Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya gana da ministan harkokin wajen Sri Lanka. Ya kuma ce jam'iyyar kominisancin China, ta farauta ce da ke keta 'yaucin* Sri Lanka--voa60/2020-10-28

    3. Lebanon: Lebanon and Israel, two countries still considered to be at war with each other with no diplomatic ties, launched a second round of sea border talks under the U.N. in Naqura.
      Lebanon da Isra'ila, ƙasashe biyu da ba sa shiri da juna, ba sa kuma hulɗa diflomasiya (diplomacy), sun fara tattaunawa zagaye na biyu akan batun iyakokinsu a teku. --voa60/2020-10-28

    4. China: The foreign ministry said U.S. senators are telling "all kinds of lies" after they put together a resolution calling the “forcible transfer” of Muslim minorities in the country genocide.
      Ma'aikatar harkokin wajen China ta ce sanatocin Amurka suna yin ƙarereyiyu* bayan da suka fidda wani ƙudari inda suka bayyana wani tilas ta kwashe Musulmai marasa rinjaye a ƙasar a matsayin kisan ƙare-dangi. --voa60/2020-10-28

    5. Switzerland: Beatrice Fihn, executive director of the International Campaign to Abolish Nuclear Weapons, says that an international treaty to ban nuclear weapons will be put in place soon. She says that the treaty will be "a new start to a new era of nuclear disarmament."
      A Switzerland, Beatrice Fihn, babbar direktar hukumar neman kawar da makaman nukiliya, ta ce nan ba da daɗewa ba, za a cimma yarjejeniyar ƙasa da ƙasa ta haramta makaman nukiliya. --voa60/2020-10-28


VOA60 Africa for Wednesday (Laraba) Oct 28th, 2020

English [5] Hausa [6] [7]

  1. VOA60 Afrika for Wednesday (Laraba) Oct 28th, 2020 [8]
    1. Tanzania: Voters in Tanzania cast their ballots on Wednesday in a presidential election that the opposition warns is already deeply compromised by manipulation and deadly violence.
      Masu zab'e a Tanzania sun kad'a kuri'a a zab'en shugaban k'asa wanda 'yan adawa suka yi gargad'in cewa yana cike da murd'a-murd'a da mummunar tashin hankali. --voa60/2020-10-28

    2. Tanzania: In the semi-autonomous Zanzibar region, hundreds of men and women formed separate queues from before dawn in the Garagara neighborhood outside the capital, Stone Town, where on Tuesday police had fired tear gas and live rounds and beat up civilians.
      A yankin Zanzibar, d'aruruwan mata da maza sun tattaru a unguwar Garagara. Inda a ranar Talata, 'yan sanda suka harba hayak'i mai sa hawaye da harsasan gaske kan jama'a. --voa60/2020-10-28

    3. Ivory Coast: International observers have arrived in Abidjan to monitor the electoral process Saturday that will determine the next leader of Ivory Coast. Concerns about violence have increased in recent weeks, after demonstrations and attacks in several parts of the country.
      Wakilan kasa da kasa sun isa Abidjan, babban birnin Ivory Coast don sa ido akan shirn zaben shugaban kasa da za a yi ranar Asabar. An kara samun fargabar tashin hankali a 'yan makwannin nan, bayan zanga-zanga da hare-hare a sassan kasar. --voa60/2020-10-28

    4. Nigeria: A judicial panel investigating claims of police brutality and the shooting of protesters has begun hearing complaints in Lagos in a nation on edge following its biggest upheaval in 20 years. Authorities say at least 13 states established judicial panels to hear complaints.
      Wani kwamitin shari'a na bincike kan zargin cin zalin jama'a da ake yi wa 'yan sanda da harban masu zanga-zanga, ya fara zaman sauraran korafe-korafe a jihar Legas da ke Najeriya da ta fuskanci tashin hankali.--voa60/2020-10-28

    5. Algeria: The great mosque of Algiers, the third largest in the world and the largest in Africa, will be inaugurated on Wednesday during a first collective prayer.
      A Algeria, a ranar Laraban nan ne, ake bude babban masallacin Algiers, wanda shi ne na uku mafi girma a duniya kuma na daya na girma a Afirika. --voa60/2020-10-28