- Google outage: YouTube, Docs and Gmail knocked offline
- Published14 December 2020
- Google applications including YouTube, email and Docs have suffered a rare service outage, with users unable to access many of the company's services.
- The outage started shortly before noon UK time, lasting more than half an hour before services were restored.
- Users around the world reported problems with Gmail, Google Drive, the Android Play Store, Maps and more.
- Google's search engine, however, remained unaffected by the problems affecting its other services.
- The brief outage had a significant impact on the company's millions of users, many of whom rely on Google services for basic work apps such as email and calendars.
- The outage also affected Google-connected smart devices such as Home speakers - leading some users to complain on social media of being unable to switch off some lights in their homes.
- It also had a knock-on effect on other apps, with players of the smartphone game Pokémon Go, for example, reporting being unable to log in.
- "We're aware of a problem with Gmail affecting a majority of users.
- The affected users are unable to access Gmail," the statement said, with the word "Gmail" replaced by other services.
- Such failures in Google's systems are rare, though a problem with some servers caused difficulties for US users in June 2019.
|
- Google outage: Manhajojin Google na Gmail da Youtube sun daina aiki na ɗan lokaci
- 14 Disamba 2020
- Manhajojin Google da suka haɗa da YouTube da email da Docs sun tsaya cak, wanda abu ne da ba a saba gani ba, inda masu amfani da shafukan suka kasa amfani da su.
- Manhajojin sun daina aiki ne na sama da mintuna 30 kafin suka dawo suna aiki, kuma hakan ya faru kafin karfe 12:00 na rana agogon Birtnaniya.
- Masu amfani da manhajojin a faɗin duniya sun yi ta ƙorafin cewa suna samun tsaiko da manhajojin Gmail da Google Drive da Android Play Store da Maps da sauransu.
- Sai dai shafin matambayi ba ya ɓata na Google da ake zuwa duba bayanai bai fuskanci wata matsala ba.
- Tsaikon da manhajojin suka samu ya yi tasiri matuƙa ga miliyoyin mutanen da ke amfani da su waɗanda suka dogara kan Google ɗin domin yin ayyukansu na yau da kullum, musamman tura saƙon email da kuma kalanda.
- Wannan matsalar ta shafi har wasu na'urorin Google da ke amfani da intanet, kamar sifiku na jin waƙa - inda wasu suka yi ƙorafi a kafefen sada zumunta cewa sun kasa kunnawa da kashe fitulun ɗakinsu.
- Haka kuma wasu da ke gudanar da wasan game na Pokémon Gosun sun yi ta ƙorafin cewa sun kasa bugawa.
- A wata sanarwa da Google ɗin ya fitar, ya ce "Muna sane da matsalar da manhajar Gmail ke fuskanta da ke damun miliyoyin masu amfani da shi.
- "Waɗanda lamarin ya shafa sun kasa shiga Gmail ɗinsu," in ji sanarwar, inda kalmar ta "Gmail" ɗin ta maye gurbin sauran manhajojin.
- Ba a cika samun irin waɗannan abubuwan ba, sai dai wasu matsaloli da aka samu na kamfanin sun jawo cikas ga masu amfani da manhajojin na Google a Amurka a Yunin 2019.
|