Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

hausaradio/BBCHausaTV2020-09-29

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

https://youtu.be/ksAwPZJe_Pw transcribed with the help of https://youtubeloop.net/watch?v=ksAwPZJe_Pw (audio)

Toh jama'a barka da sake saduwa da ku a cikin shirin, ga taƙaitattun labaran duniyar da wasanni daga nan BBC.

  1. Za mu je Najeriya domin ganin ɓarnar da ambaliyar ruwa wanda kogin Kwara ya haddasa a wasu yankunan jihar Niger.
  2. A karon farko, shugaba Trump na Amurka da abokin hamayyarsa za su fafata a muhawarar talabijin a yaƙin neman zaɓe.
  3. Ana gudanar da bincike a wajen haƙar ma'adinan Jade, inda zabtarewar ƙasa ta janyo mutuwar sama da mutum 100 a Myanmar.

Nigeria

Toh a bana dai, ambaliyar ruwa na yin ɓarna a sosai a sassa daban-daban na nahiyar Africa. Ana samun asarar rayuka da dukiya kuma ruwan na tashin ɗinbin jama'a daga muhallansu. A Nigeria dai, ruwan ya mamaye yankuna da dama da suka haɗa da jihar Niger. Ɓarnar ta sa hukumomin jihar na neman agaji daga gwamnatin tarayya. Abokin aikin mu Zaharaddeen Lawal ya ziyarci wasu yankuna na jihar ga kuma rahotansa:

(1:20) Mahukunta sun tabbatar da mutuwar mutum 27, wasu 3 kuma sun ɓata zuwa yanzu sakamakon ambaliyar a sassan jihar. Lamarin dai ya faru ne a ƙananan hukumomi ashirin da biyu cikin ashirin da biyar (22/25) na jihar. Garuruwa 500 ne ambaliyar ta shafa, galibi wadanda ke kusa da gaɓar koguna. Al'amarin dai ya shafi fiye da mutum 60,000 a cewar hukumomin jihar. Ƙaramar hukumar Mokwa, na cikin wuraren da lamarin ya fi muni, inda ambaliya daga garin kogin Kwara ta shafe garuruwa fiye da 16. Yayin da muke tafiya a cikin jirgin ruwa zuwa yankunan da ambaliyar ta shafa, na shaidawa garuruwa da dama wadanda duk ruwa ya shafe su. Babu kowa da ake iya gani a cikinsu. Kasancewar muna cikin jirgin ruwa ne, na samu da ƙyar, na zanta da wata mata wadda ta shaida min halin da suke ciki da kuma irin taimakon da suke buƙata.

(2:11) A garin da muke yanzu, dukkan mu, kamar mutum 15, kamar mutum 12, ya sami ɗakin da zai iya kwana... Ba mu da ɗakin da za mu kwana, gwamnati ta yi mana taimakon da za a taso da mu a kai mu can... shi ne muke so yanzu, a yi mana taimako.

Game da buƙatar wadannan mutanen, na sake yi wa matsagunnai, na tuntuɓi sakateran gwamnatin jihar Niger, Ahmad Matane, inda ya shaida min cewa gwamnatin jihar za ta sake yi wa mutanen da ambaliyar ta shafa matsagunnai, har ma sun fara da garuruwan Muregi da Ketso, wadanda suke ƙaramar hukumar Mokwa. Sannan ya ce sun rarrabawa mutanen kayan abinci da magunguna. (2:50) Sai dai ya ce ambaliyar tafi ƙarfin gwamnatin Niger ita kaɗai. Ya ce suna buƙatar ɗauki daga gwamnatin tarayya.

Myanmar

Gwamnatin Myanmar na guzanar da bincike akan abinda ya haddasa mummunar zabtarewar ƙasa a wurin haƙar ma'adinan dutsen Jade. [1] Wanda kuma ya hallaka sama da mutane 170. Ana dai matsawa gwamnatin lambar kawo sauyi a aikin hak'ar ma'adinan mai cike da hadari. Wanda kuma a nanne ake samar da kashi 70 cikin 100 (70%) na dutsen jade a duniya. Da kuma ake samun biliyoyin daloli. Ga rahoton Ibrahim Mijinyawa:

Addu'o'in da ake yi kenan ga wadanda suka mutu da kuma wadanda suka bata, daga bala'in zabtarewar k'asa mafi muni a Myanmar wanda ya auku a nan wurin hak'ar dutsen jade, mai daraja mafi girma a duniya. Wadanda suka tsira da ransu, sun ce, babu wani gargadi da aka yi musu. Ruwa da taku ne suka rik'a kwararowa a lokacin da suke neman dutsen jade wanda ya yi saura a cikin ramuka.

Na yi ta wintsilawa a cikin ruwa. Duwatsu na bugu na. Na zaci mutuwa zan yi.

Ya dai yi kokarin tsira da ransa amma abokansa basu tsira ba.

Kamar 'yan uwa ne suke. Ba na jin dad'i ganin cewa ni ne na tsira. Ina jin, ina ma a ce bala'in nan mafarki ne, mara dad'i.

Masu d'iban dutsen jade, wadanda 'yan kad'an ne da ke taka rawa a masana'antar da ke samun biliyoyin dala, wacce kamfanonin da ke da alak'a da sojojin Myanmar ke gudanarwa da kuma k'ungiyoyin 'yan tawaye masu d'auke da makamai. Tawagar gwamnati da ke gudanar da bincike, ta ce, an yi wa mutane gargadin saukar ruwan sama mai k'arfi. Sannan kuma tawagar ta fisa da wadanda suka tsira bayan da ta ce wadanda suka mutun, sun nuna had'ama.