Toggle menu
24.1K
669
183
158.4K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/072 does-your-head-explode-at-night

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations


#: Does your head explode at night? [1] <> Kana jin kamar kanka na tarwartsewa da daddare? [2]

#: Our article aboutexploding head syndrome[3] <> Wani rubutu da da BBC ta yi a kan larurar da ke damun wasu mutane wadanda a wani lokaci da daddare sukan ji kamar bam ya tashi a kansu, [4]

#: prompted many of you to share your strange and intriguing stories, [5] <> ta sa masu karatu da dama sun bayyana mana labarai masu daure kai a kan larurar. [6]

#: says William Park. [7] <> Kamar yadda William Park ya sheda mana [8]

#: In our recent article about living with exploding head syndrome, [9] <> A kasidar da BBC ta rubuta kwanan nan kan yadda ake rayuwa da larurar da mutum kan ji kamar kansa ya tarwatse, [10]

#: we talked to Niels Nielsen about his experiences with the condition. [11] <> mun tattauna da Niels Nielsen yadda yake rayuwa da larurar. [12]

#: Despite being relatively unknown, its surprisingly common, [13] <> Duk da cewa kusan ba a san wannan larura ba sosai, abin mamaki mutane da dama na da ita, [14]

#: with 18% of students in one study reporting that they had experienced the phenomenon. [15] <> kusan kashi 18 cikin dari na daliban da aka yi wani nazari a kansu sun ce sun taba samun matsalar. [16]

#: Nielsen describes the feeling as asudden crescendo of noise, then a profound and jarring explosion of sound, electrical fizzing and a bright flash”. [17] <> Nielsen ya bayyana larurar da cewa, za ka ji wani kara ne kwatsam da kuma wani hasken wuta". [18]

#: This description prompted many of you to come forward with your own stories. [19] <> Wannan bayanin ya sa yawancin mutane sun bamu labarin yadda su ma suka taba jin wannan abu yadda ya faru da su. [20]

#: Garry Fowler, for instance, had no idea about the syndrome: [21] <> Misali Garry Fowler, ba shi da masaniya kan yadda larurar take: [22]

#: I have had this happen many times [23] <> "abin ya faru da ni sau da dama [24]

#: but had no idea of its cause [25] <> amma ban san abin da ke haddasa shi ba [26]

#: or that it was a recognised syndrome.” [27] <> ko kuma ma a ce wata larura ce da aka san da ita." [28]

#: And he wasnt alone. [29] <> Kuma ba shi kadai ba ne ba shi da masaniya a kan larurar. [30]

#: Mat Porton commented that he only realised it was a recognised condition when he heard it discussed on Radio 4. [31] <> Mat Porton ya bayyana cewa sai da ya ji ana tattaunawa akan matsalar ne a tashar Rediyon BBC 4 ya san cewa matsala ce da aka san tana faruwa. [32]

#: Jess Dominguez added: [33] <> Jess Dominguez shi ma ya yi karin bayani da cewa, [34]

#: Its comforting to know Im not crazy and that these are real things Ive experienced.” [35] <> “na ji dadi da na san cewa ba larurar tabin hankali nake da ita ba kuma wannan abu ne na gaske wanda ya faru da ni.” [36]

#: For some, like Kimia Mokhtari Aubin, it only happens once a lifetime, [37] <> Ga wasu mutanen irinsu Kimia Mokhtari Aubin, sau daya matsalar ke faruwa ga mutum a rayuwa, [38]

#: but others have been left haunted by the experience after many years. [39] <> amma kuma wasu na zama da tunani da kuma fargabarta shekaru da dama bayan ta faru [40]

#: Aza Mohammed reached out to us by email to share a story from his childhood in Iraq. [41] <> Ta hanyar email Aza Mohammed ya ba mu labarin yadda abin ya faru da shi tun yana yaro a Iraki. [42]

#: During the Iraq-Iran war, he and his classmates were evacuated from his school because of a bomb scare. [43] <> A lokacin yakin Iran da Iraki, an kwashe shi da 'yan ajinsu daga makarantarsun saboda fargabara tashin bam. [44]

#: That night he was woken up by an explosion [45] <> A wannan daren wata kara mai tsanani ta tashe shi daga barci, [46]

#: and he ran to his parents in tears, only for them to tell him that no bomb had gone off. [47] <> inda ya tashi ya gudu zuwa wurin iyayensa yana kuka, inda suka gaya masa cewa ba wani bam da ya tashi. [48]

#: Even 30 years later he is unable to explain why his ears were still buzzing from the sound long after he woke up. [49] <> Har bayan shekara 30 da aukuwar lamarin bai iya bayar da bayanin dalilin da ya sa kunnensa yake rugugi ba na wanna kara tsawon lokaci bayan ya tashi daga barci. [50]

#: Several others, like Ivy Deseaux Putnam, also said the noise of exploding head syndrome sounded like gunshots or bombs to them: [51] <> Mutane da dama kamar Ivy Deseaux Putnam, sun ce karar da mutum ke ji ta wannan larura kamar ta harbe-harben bindiga ko tashin bam ce. [52]

#: “[[[It]]] sounds like gunshots in my bedroom, [53] <> Ya ce, kara ce kamar ta harbin bindiga a dakina, [54]

#: a glass door shattering [55] <> ko wata kofar gilas aka fasa [56]

#: or a sonic boom above my house.” [57] <> ko wata gagarumar fashewa a saman gidana. [58]

#: Wendy Derbyshire added: [59] <> Wendy Derbyshire ta kara da cewa: [60]

#: I truly thought a bomb had gone off in the neighbourhood [61] <> " A gaskiya na dauka bam ne ya tashi a unguwarmu, [62]

#: but realised I was mistaken [63] <> amma sai na ga ba haka ba ne, [64]

#: when I checked outside and there was no disturbance. [65] <> lokacin da na duba waje na ga ba wata hatsaniya ko gujeguje. [66]

#: It really was unbelievably loud.” [67] <> Karar ta wuce hankali." [68]

#: Irene McNeil got in touch by email to describe her experiences. [69] <> Irene McNeil ta email ta bayyana mana yadda abin ya same ta da yadda ta ji. [70]

#: She too referred to the noise as a gunshot, [71] <> Ita ma ta ce ta ji abin ne kamar karar harbin bindiga, [72]

#: but her experience left her with severe pain [73] <> amma kuma ita abin ya sa mata tsananin ciwo [74]

#: and numbness that took months to subside. [75] <> da wani yanayi a makogaronta wanda sai bayan watanni da aukuwar abin ya fara raguwa. [76]

#: No one else who got in touch reported such a strong physical reaction to the phenomenon. [77] <> Ba wani kuma cikin wadanda suka ba mu labarin yadda abin ya same su, wanda ya gaya mana yadda ya yi musu tsanani haka. [78]

#: She told us that she still feels numbness in her throat even after 30 years. [79] <> Ta gaya mana cewa har yanzu tana jin wani abu a makogwaronta bayan shekara 30 da aukuwar abin. [80]

#: A lack of sleep is thought to increase the risk of experiencing exploding head syndrome. [81] <> Ana ganin matsalar rashin barci na iya kara hadarin gamuwa da wannan larura ta jin kamar kanka ya tarwatse. [82]

#: The condition is also linked to sleep paralysis [83] <> Ana danganta matsalar da kasa barci, [84]

#: and both are thought to share an underlying cause, [85] <> kuma ana ganin dukkanin larurorin kusan suna da sanadi iri daya ne, [86]

#: so many of your experiences, [87] <> saboda haka da dama daga cikin mutanen da suka ba mu labarinsu na matsalar, [88]

#: like Zoe Stewarts, combined the two phenomena: [89] <> kamar Zoe Stewart ya hada larurorin biyu. [90]

#: I have both. [91] <> Ya ce, ina da duka matsalolin biyu. [92]

#: Sleep paralysis always felt like drowning to me, [93] <> Matsalar kasa barci tana min in ji kamar ruwa na ci na, [94]

#: with desperate kicking to reach the surface but never being able to reach air. [95] <> ina ta kokarin in yo sama, amma na kasa. [96]

#: Exploding head sounds like someone turning the volume up on white noise as loud as it will go and leaves my ears ringing.” [97] <> Tarwatsewar kai kuwa, mutum zai ji ne kamar wani yana kunna wani kara ne mai tsanani, da ya cika ma kunne ta ko'ina. [98]

#: When combined with sleep paralysis the experience can be terrifying. [99] <> Idan ka hada wannan larura da ta kasa yin barci za ka ji abin ya kai tsanani matuka. [100]

#: After reading this freaky story shared by Rachael Roseann Blythe [101] <> Kuma bayan karanta labarin Rachael Roseann Blythe [102]

#: we were left in awe of how powerfully the condition physically affects the body: [103] <> mun ma rasa yadda za mu iya kwatanta karfin tasirin da hadakar larurorin biyu za su yi wa jikin mutum. [104]

#: The combined effect of seeing bright lights, [105] <> Idan mutum ya yi tunanin haduwar wannan matsaloli a kansa a lokaci daya, wato ganin haske mai tsanani, [106]

#: hearing loud noises [107] <> da jin kara mai tsananin gaske, [108]

#: and being unable to move that comes with sleep paralysis [109] <> da kasa motsi, sannan kuma [110]

#: and exploding head syndrome [111] <> da jin tarwatsewar kanka duk a lokaci daya. [112]

#: have led some to believe that the conditions could explain alien abduction stories. [113] <> To hakan zai sa wasu su yarda da irin labarin nan na kunne ya girmi kaka (na yadda wasu aljanu ko dodanni za su sace mutum su tafi wata duniya da shi). [114]

#: In our article, Nielsen told us; “I can definitely see how they could gravitate towards a supernatural explanation.” [115] <> Bayan karanta rahoton matsalar da BBC ta fara rubutawa, wasu mutanen sun bayyana yadda suke rayuwa da larurar, tun da yanzu sun san yadda za su gane ta. [116]

#: Emily Rose Matthews says she is able torecognise the feeling immediately[117] <> Emily Rose Matthews ta ce, a yanzu tana iya gane alamun larurar da ta fara taso mata [118]

#: having experienced it regularly, [119] <> saboda tana samunta akai akai, [120]

#: and she is able to jolt herself fully awake with a burst of mental effort to avoid the worst effects. [121] <> kuma tana iya daure wa cutar da ta taso mata don kada ta kai ga tsananinta. [122]

#: The article struck a chord with many of you [123] <> Rubutun ya sosa wa yawancin mutane inda yake musu kaikayi, [124]

#: and it is noticeable how varied the experiences were. [125] <> kuma ta fito fili cewa kowa da yadda yake jin irin tasa larurar (wadanda suke da ita). [126]

#: Nielsen said the episodes now dont bother him, [127] <> Nielsen ya ce yanzu larurar ba ta damunsa sosai, [128]

#: but for others it seems that the condition is something they have to live with every day. [129] <> amma ga wasu masu larurar matsala ce da za su ci gaba da rayuwa da ita yau da kullum. [130]

Contents