- TikTok copycat removed from Google's Play Store
- Published 10 June 2020
- Zynn has been widely downloaded
- since launching last month
- Google has removed video app Zynn from its Play Store
- amid accusations it has been stealing content from other apps.
- The TikTok-style app offers cash payouts to users who sign up and watch videos,
- and has became one of the most downloaded apps in the US.
- But it has sparked a number of complaints from social media influencers who claim their videos are being reposted without permission.
- Zynn said it had launched a new method for users to report plagiarism.
- The popular video platform is funded by Kuaishou,
- the Chinese rival to TikTok owner ByteDance.
- Zynn was first made available officially to users at the beginning of May.
- However, according to Wired,
- many of the copycat accounts on the platform
- uploaded their first posts in February.
- Users earn money on the app by watching videos and inviting friends to sign up.
- Earnings can then be used to buy gift cards, or transferred via PayPal.
- Now a number of popular TikTok users, some with millions of followers, have come forward claiming that accounts pretending to be them have begun appearing on Zynn.
- “I feel that it’s honestly sad that they are stealing creators’ content and impersonating people,”
- a TikTok influencer told Wired.
- The app's community guidelines ban users from posting
- "anything that you do not own or do not have permission from the owner to share". Google has removed the app from its Play Store amid the controversy, although the tech giant has yet to confirm its reason for doing so.
- The BBC has asked Zynn and Google for comment.
- A spokesman for Apple said the company is "investigating" the app,
- which is currently still available on its app store.
|
- TikTok: An cire wata manhajar Zynn daga rumbun Google's Play
- 10 Yuni 2020
- Ana ta sauke manhajar Zynn a fadin duniya
- tun bayan kaddamar da ita a watan jiya
- Google ya cire manhajar Zynn da ake daukar hoton bidiyo daga cikin tsarinta
- yayin da ake tsaka da zargin manahajar da satar fasahar wasu manhajojin.
- Zynn da ta saci tsarin manhajar TikTok ya sanya gasar kudi ga masu amfani da shi da suka shiga suka kalli bidiyo,
- cikin gaggawa ya zama daya daga cikin manhajojin da aka fi saukewa a kan waya a Amurka.
- Amma ya janyo korafe-korafe daga wajen masu yawan mabiya da ke ikirarin ana kara wallafa bidiyonsu a intanet ba da izininsu ba.
- Zynn ya ce ya kaddamar da sabuwar hanya ga masu amfani da shi domin su shigar da karar masu satar fasaha.
- Fitacciyar manhajar dai na samun kudinta ne daga Kauishou,
- wani dan kasar China da ke takun saka kamfanin TikTok wanda ya mallaki byteDance.
- A farkon watan Mayu ne wannan manhaja ta Zynn ta zama ta wadatu ga masu son ajiye ta kan wayoyinsu.
- Haka kuma jaridar Wired
- ta ce mafi yawan shafukan da aka bude da suka yi satar fasaha,
- sun fara wallafe-wallafe ne a watan Faburairu.
- Masu amfani da manhajar na samun kudi duk lokacin da suka kalli bidiyo kuma suna gayyatar abokansu su sauke manhajar.
- Ana karbar kudin ne ta hanyar kyautar kati, ko kuma aika kudi ta Paypal.
- Yanzu masu amfani da TikTok na korafin ana bude wasu sabbin shafuka da bayanansu a Zynn.
- "A ganina abin takaici ne wannan domin kuwa satar fasaha ne, da kuma sojan gona kan bayanan mutane,"
- Wani mai amfani da TikTok ya shaidawa Wired.
- Ya kamata masu lura da harkokin kafafen
- "Su hana kowa wallafa abin da ba nasa ba ko kuma tura wani abu ba tare da sanin wanda ya mallake shi ba".
- BBC ta tambayi Zynn kan wannan mataki na Google.
- Mai magana da yawun manhajar ya ce kamfanin yana bicike kan manhajar,
- wadda har yanzu take kan rumbun Google.
|