Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/027 asking what people do

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

#: Why you shouldn't ask people what they do [1] <> Me ye dangantakar aikinmu da kimarmu a rayuwa? [2]

#: Why do we ask people weve just met what they do for a living? [3] <> Me ye sa mu ke tambayar mutanen da mu ka hadu da su aikin da su ke yi? [4]

#: It can indicate an unhealthy link between our work and identity. [5] <> Hakan na iya zama alamar mummunar alaka tsakanin aikinmu da kuma sanin mu su waye. [6]

#: In the first few minutes of striking up conversation with a stranger, [7] <> Cikin minticon farko na fara tattaunawa da bakin ido, [8]

#: Yasaman Hadjibashi is inevitably asked a question we all get: [9] <> akan tambayi Yasaman Hadjibashi abinda aka saba tambayar kowannenmu: [10]

#: what do you do?” [11] <> "Wane aiki ki ke ne?" [12]

#: The answer she gives is intentionally vague. [13] <> Da gangan ta ke kin bada amsa kai tsaye. [14]

#: She could mention her MBA from Harvard Business School, [15] <> Ta na iya fadar digirin MBA da take da shi daga Jami'ar Harvard, [16]

#: or the fact that shes a top executive at Barclays Africa Group. [17] <> ko kuma matsayinta na babbar jam'ia a bankin Barclays Group Africa. [18]

#: Instead, [19] <> Maimakon haka, [20]

#: the Johannesburg-based chief data officer offers a less-than-detailed answer which, she hopes, will separate her work identity from who she is outside of work. [21] <> Yasaman kan bada amsar da take fatan za ta bambance tsakanin rayuwarta da kuma aikinta. [22]

#: I would like people to get to know me before they know my credentials,” she says. [23] <> Ta ce "Zan so mutane su san ni tukun kafin su san me ye aiki na. [24]

#: Its almost my test because Id like to know if they start being respectful anyway.” [25] <> Hakan kuma kamar wani gwaji ne in ga ko za su mutuntani ba tare da sanin matsayina ba?" [26]

#: Hadjibashi isnt the only one feeling torn between her social and work identity: [27] <> Ba Hadjibashi ce kadai ke kokarin bambance tsakanin rayuwarta da aikinta ba: [28]

#: career experts say that in a social setting, [29] <> kwararru akan harkokin aiki sun ce [30]

#: even the most successful people will benefit from disentangling their sense of self from what they do. [31] <> ko mutanen da suka samu gagarumar nasara a sana'o'insu za su yi amfani da bambance tsakanin waye su da kuma me suke yi. [32]

#: Retaining a distinct identity causes less grief during a job loss, [33] <> Rarrabe tsakanin rayuwarka da aikinka na rage alhini idan ka rasa aiki, [34]

#: creates more authentic connections outside of the office [35] <> ya na bada damar kulla kyawawan alakoki a wasu harkokin da basu shafi ofis ba, [36]

#: and helps people feel more respected even when away from a powerful job. [37] <> sannan kuma ya na sa mutum jin kimarsa ba ta ragu ba idan ya bar wani babban aiki. [38]

#: But as companies [39] <> Sai dai kuma a wannan zamani da kamfanoni da dama [40]

#: require a full-time connection to work, [41] <> ke bukatar ma'aikatansu su mai da hankali dari bisa dari kan ayyukansu, [42]

#: many workers find themselves unable to separate their identity from what they do professionally. [43] <> abu ne mai matukar wuya ga ma'aikata da dama su rarrabe tsakanin rayuwarsu da kuma aikinsu. [44]

#: This may ultimately negatively affect their wellbeing, says Al Gini, [45] <> Hakan zai iya sa musu rashin jin dadin rayuwa kamar yadda Al Gini, [46]

#: a business ethics professor at Loyola University in Chicago and author of My Job, My Self. [47] <> malamin harkokin kasuwanci a jami'ar Loyola ta Chicago kuma mawallafin littafin 'Aikina, Rayuwata' ya bayyana: [48]

#: The less we have in other interests, the more dependent we are on our job. [49] <> "Karancin abubuwan yi a waje na sa mu kara dogaro da ayyukanmu. [50]

#: So when we lose it, you totally fall apart,” Gini says. [51] <> Don haka da zarar mun rasa aikin sai rayuwarmu ta sukurkuce." [52]

#: To be sure, those who inquire about work identity are simply trying to piece together social status, [53] <> Hakika, ma su tambayarmu aikinmu na kokarin gano matsayinmu cikin al'umma, [54]

#: in the same way some Asian cultures [55] <> kamar yadda a wasu al'ummomi na nahiyar Asiya [56]

#: focus on lineage and the parentswealth rather than the occupation, [57] <> kan damu da sanin iyaye da kakannin mutum tare da arzikinsu maimakon sana'a [58]

#: says Ho Shee Wai, a psychologist and director of the Counselling Place in Singapore. [59] <> in ji Ho Shee Wai, mai ilimin halayyar dan Adam kuma darakta a cibiyar Counselling Place da ke Singapore. [60]

#: But even as others ask about occupation [61] <> Sai dai duk da cewa mutane kan tambayemu aikinmu ko sana'armu ne [62]

#: as a way to figure out your standing, [63] <> domin su san matsayin da zasu ajiye mu, [64]

#: name-dropping your company [65] <> bayyana sunan kamfanin da ka ke wa aiki [66]

#: or accomplishment too early on [67] <> ko kuma matsayinka a sana'a [68]

#: can create a false sense of self or deeply associate you with a job youre eager to leave. [69] <> na iya sa mutane su alakanta kimarka da aikin da watakila ma kokari ka ke ka bar shi. [70]

#: Dont fall into the trap of thinking these labels define you,” she says. [71] <> A cewar Ho Shee Wai; "Kar ka yadda aikinka ko sana'arka su zamo ma'aunin kimarka." [72]

#: Leaving work behind [73] <> Barin aiki a gefe [74]

#: Those who only identify themselves through their work [75] <> Mutanen da ke alakanta kimarsu da sana'o'insu ko aikinsu kurum [76]

#: can ultimately fall into depression should it go away, [77] <> na iya shiga matsananciyar damuwa duk lokacin da su ka rasa su, [78]

#: while others can more quickly rebound from the loss, [79] <> yayinda wadanda ba haka su ke ba za su iya girgijewa cikin hanzari, [80]

#: according to Susan Krauss Whitbourne, psychology professor at the University of Massachusetts Amherst in the US. [81] <> a cewar Susan Krauss Whitbourne, farfesar ilimin halayyar dan Adam a jami'ar Massachusetts Amherst da ke Amurka. [82]

#: Making a point to discuss non-work related topics with friends and family members can help build that necessary barrier between your work and social self, she adds. [83] <> Ta kara da cewa abinda zai kawo nisanta aiki da rayuwa shi ne kokarin tattauna abubuwan da basu shafi aiki ba da abokai da kuma 'yan uwa. [84]

#: But those who are happiest with their jobs need to spend even more time disconnecting. [85] <> Amma ma'aikatan da su ka fi gamsuwa da ayyukansu su ne ma su ka fi bukatar nisanta rayuwarsu da aikin. [86]

#: Workers who enjoy their work [87] <> Ma'aikatan da ke jin dadin aikinsu [88]

#: for more intrinsic reasons such as appreciating the job and having fun at the office, [89] <> saboda ganin muhimmancin abinda su ke yi ko kuma annushawar da su kan samu a wurin aiki, [90]

#: are more deeply attached to their work identity [91] <> su ne su ka fi alakanata rayuwarsu da ayyukansu [92]

#: than those who work simply for money and status, [93] <> fiye da wadanda su ke yi don kudi ko matsayi, [94]

#: according to research from Krauss Whitbourne. [95] <> a cewar wani bincike da Krauss Whitbourne ta gudanar. [96]

#: While having an intrinsic love for your job on a day-to-day basis [97] <> Ta kara da cewar, ko da yake jin dadin aikinka [98]

#: can help make you happy, [99] <> na sa ka farin ciki a rayuwa, [100]

#: it can make separating from your work identity even more complicated, she adds. [101] <> hakan na sa raba tsakanin aikinka da rayuwarka ya wahalar kwarai da gaske. [102]

#: Steps to a well-rounded identity [103] <> Matakan samun 'yantacciyar kima a rayuwa [104]

#: For one, creating a unique brand that focuses on your skills [105] <> Na farko, ka gabatar da kanka bisa kwarewarka [106]

#: rather than the name of your company or job title can help, [107] <> ba tare da ka dangana da kamfanin da ka ke aiki ba ko kuma matsayinka a kamfanin, [108]

#: says Francois Daumard, an IT executive in San Francisco. [109] <> in ji Francois Daumard, wani jami'in fasahar sadarwa da ke San Francisco. [110]

#: When Daumard transitioned from working at buttoned-up Microsoft to the more startup feel of Apple [111] <> Lokacin da Daumard ya sauya wurin aiki daga Microsoft zuwa Apple, [112]

#: and now to a lesser-known firm, [113] <> sannan ya koma wani kamfanin da bai shahara kamar wadannan ba [114]

#: he decided to tell those he met about his role in the IT world [115] <> sai ya koma gabatar da kansa a matsayin kwararre a harkar fasahar sadarwa [116]

#: without a mention of companies or official job titles. [117] <> ba tare da ambaton kamfanin da ya ke wa aiki ko matsayinsa a kamfanin ba. [118]

#: The transition helped him [119] <> Wannan dabarar ta taimaka masa wurin [120]

#: create a more consistent identity, especially in front of acquaintances who werent always aware of his job moves. [121] <> tsare kimarsa musamman a idon mutanen da ba su da alaka ta kusa da shi. [122]

#: But for most people, [123] <> Sai dai, dabarar da tafi ci ga mafi yawan mutane, [124]

#: the trick is finding hobbies that are truly valued outside of work, [125] <> ita ce samun wani abin debe kewa mai muhimmanci, wanda bai danganci aikinsu ba, [126]

#: says Krauss Whitbourne, who spends several hours per week on crafts and quilting. [127] <> a cewar Krauss Whitbourne, wacce ke bada sa'o'i da dama cikin mako guda ta na sakar tuma-kasa. [128]

#: You need to be seeing those hobbies [129] <> Ta ce; "Kamata ya yi ki dauki wannan abin debe kewar [130]

#: as important and not just a stupid thing you do,” she says. [131] <> a matsayin wani abu mai muhimmanci a rayuwa ba wai kawai rage lokaci ba. [132]

#: Many employees pursue leisure activities outside of the office, [133] <> Ma'aikata da yawa na yin sana'o'in hannu domin debe kewa kurum [134]

#: but drop them quickly as duties pile up at work. [135] <> kuma da zarar aiki ya fara yawa sai su yi watsi da su. [136]

#: The key is to prioritise them [137] <> Abinda ya kamata shi ne ki ba su muhimmanci [138]

#: in a way that encourages them to highlight those activities during an introduction. [139] <> ta hanyar da zaki iya gabatar da kanki a matsayin mai yin wadannan abubuwan lokacin da duk ku ka hadu da bakin ido." [140]

#: Even with a fulfilling career, Hadjibashi says the diversity of her social circle[141] <> Duk da Hadjibashi ta gamsu da sana'arta, ta ce irin mutanen da take hulda da su[142]

#: be it stay-at-home mums, teachers or entrepreneurs[143] <> matan aure mazauna gida, malamai, 'yan kasuwa[144]

#: keep her from being recognised solely for her work. [145] <> sun sa ba ta yadda ta alakanta kimarta kan aikin da ta ke yi kacokan ba. [146]

#: With friends, [147] <> Idan ta na tare da kawayenta, [148]

#: her work isnt naturally a discussion point [149] <> aikinta ba ya cikin abinda su ke tattaunawa [150]

#: because it can sound very technical to those outside of her industry. [151] <> domin mutane da dama ba sa iya fahimtar aikinta. [152]

#: On the other hand, [153] <> Haka kuma, [154]

#: identifying with who she is outside of work [155] <> alakanta kimarta da abubuwan da take yi idan ta bar wurin aiki [156]

#: gives her more time to be her most authentic, [157] <> na ba ta damar ta gudanar da rayuwa mai inganci. [158]

#: she adds: [159] <> Ta kara da cewa; [160]

#: Just spending time with these individuals [161] <> "Kasancewa tare da kawayena [162]

#: helps me to switch off.” [163] <> na ba da damar nisanta tsakanin rayuwata da aikina." [164]

Contents