- A spender marries a saver — now what? [1] <> Almubazzari ya auri matsoluwa- Ya kenan? [2]
- Related podcast: https://www.inoreader.com/article/3a9c6e7bc1db10b8-spender-vs-saver-navigating-money-talks-in-marriage
<small><small> --[[bbchausa_verticals/086-A_spender_marries_a_saver]]</small></small>
https://www.bbc.com/worklife/article/20151027-a-spender-marries-a-saver-now-what
|
https://www.bbc.com/hausa/vert_cap/2015/11/151117_vert_cap_a_spender_marries_a_saver
|
A spender marries a saver — now what?
|
Almubazzari ya auri matsoluwa- Ya kenan?
|
You've heard that money is the cause of many arguments between partners. But can a spender marry a saver and live happily ever after?
|
Ina ganin ka sha jin cewa kudi shi ne ke jawo musu da sabani tsakanin ma'aurata ko masoya da dama. To ko almubazzari zai iya auren matsoluwa kuma su zauna lami lafiya?
|
From the day they met it was clear: Taylor Murray and his wife are polar opposites when it comes to money.
|
Tun daga ranar da suka hadu abu ne da yake a zahiri cewa Taylor Murray da matarsa kishiyoyin juna ne idan ana maganar kudi.
|
“I’m the spender and my wife is the saver,” said Murray, 33, who lives in California.
|
"Ni ne mai kashe kudi matata kuma mai tsimi," in ji Murray mai shekara 33 wanda ke zaune a California.
|
- “She knows the bank balances
- without looking at the chequebook,
- and has an iron will when it comes to resisting impulse buying.
- “She sometimes feels like I’m being irresponsible
- and I sometimes feel like she needs to let go and live a little.”
- This sounds like a recipe for marital disaster;
- money arguments are the number one predictor of divorce,
- according to research from Kansas State University in the US.
- But, it’s not the case for Murray and his wife.
- He believes the couple has benefited from both viewpoints.
- “We’ve had some exciting trips due to my impulsiveness
- and we’ll remember those good times forever,”
- said Murray, who is a senior developer for call centre software company CallTools.com.
- “We also have a nice house with a decent mortgage and six months’ income in the bank as an emergency fund. That’s due to her great planning.” Although Murray and his wife have made it work, getting into a relationship with someone who is your money opposite can be stressful. In one survey, self-identified “tightwads” who were married to “spendthrifts” were half as likely to report that they were “perfectly happy” with their marriage as couples who described themselves as philosophically matched when it came to money, according to research from the University of Michigan’s Ross School of Business in the US.
|
- Ta san nawa ne a cikin asusunmu na ajiya na banki da ka,
- ba tare da ta duba littafinmu na banki ba.
- Kuma tana da kafiya kan kin sayen wani abu wanda haka kawai yazo maka a rai ko kayi sha'awarsa.
- Wani lokacin tana ganin ni almubazzari ne,
- ni kuma ina mata kallon matsoluwa ce.
- Wannan ya zama kamar hanyar magance matsalar aure,
- domin musu a kan kudi shi ne abin da ya fi haddasa mutuwar aure,
- kamar yadda binciken da aka yi a jami'ar jihar Kansas da ke Amurka ya nuna.
- To amma sabanin haka, lamarin ya sha bamban a wurin Murray da matarsa.
- Yana ganin su a nasu bangaren sun amfana ne daga dabi'a da ra'ayin junansu.
- "Mun yi tafiye-tafiye masu dadi saboda sha'awata
- kuma za mu dade ba mu manta da su ba,"
- in ji Murray, wanda kwararre ne wajen yin manhajar kwamfuta a kamfanin CallTools.com.
- "Muna da gida mai kyau da tarin kudin da ya kai albashin wata shida a asusunmu, a matsayin na ko-ta-kwana, kuma duka wadannan sun samu ne sakamakon tattalinta." Ko da yake Murray da matarsa su dai sun yi nasara a zamantakewarsu ta aure duk da sabanin da suke da shi wurin kashe kudi, to amma abu ne mai wuyar gaske ka iya zaman aure da wadda ra'ayinka ya bambanta da nata ko nashi kan kashe kudi. A wani bincike da aka yi, kusan rabin matsolo-matsolon da ke auren almubazzarai ne suke ganin su suna jin dadin aurensu, idan aka kwatanta da auren wadanda suke ganin tasu ta zo daya da abokan aurensu a fannin kashe kudi da tanadi. Kamar yadda binciken na makarantar nazarin harkokion kasuwanci ta jami'ar Michigan a Amurka ya nuna.
|