Baqara 1-5
- Alif Lam Mim. --Quran/2/1
- Wannan littafi ne da babu wani kokwanto a cikinsa; shiriya ne ga masu taqawa. --Quran/2/2
- This is the Book about which there is no doubt in it! It's a guide/guidance for those mindful of Allah. (See also Quran/1/6, Quran/19/76, Quran/guidance)
- dhālika l-kitābu lā rayba fīhi hudan lil'muttaqīn
- Wadanda suke yin imani da gaibi kuma suke tsayar da salla kuma suke ciyarwa daga abin da Muka azurta su da shi. --Quran/2/3
- Who believe in the unseen, establish prayer, and donate / spend out of what We have provided for them
- alladhīna yu'minūna bil-ghaybi wayuqīmūna l-ṣalata wamimmā razaqnāhum yunfiqūn
- Wadanda suke yin imani da abin da aka saukar maka da abin da aka saukar a gabaninka, kuma suke sakankancewa da ranar lahira. --Quran/2/4
- And who believe in what has been revealed to you, [O Muhammad], and what was revealed before you, and of the Hereafter they are certain [in faith]
- and who believe in what has been revealed to you ˹O Prophet˺ and what was revealed before you, and have sure faith in the Hereafter.
- wa-alladhīna yu'minūna bimā unzila ilayka wamā unzila min qablika wabil-ākhirati hum yūqinūn (yaƙini)
- Wadannan suna kan (babbar) shiriya daga Ubangijinsu, kuma wadannan su ne masu samun babban rabo. --Quran/2/5
- Those are upon [right] guidance from their Lord, and it is those who are the successful
- It is they who are ˹truly˺ guided by their Lord, and it is they who will be successful.
- ulāika ʿalā hudan min rabbihim wa-ulāika humu l-muf'liḥūn
Tafsiri:
Allah swt ya bud'e wannan Sura da harufin Alif da Lam da Mim. Ban da ita wannan Sura da akwai surorin Alqur'ani da dama da Allah ya bud'e su da irin wadannan haruffa. Da dama daga cikin malamai suna cewa, Allah ne kad'ai ya san abin da yake nufi da su (only Allah knows the meaning of these disjointed letters). Wasu kuma sun yi qoqarin bayyana ma'anoninsu. Amma magana mafi inganci ita ce, Allah yana nuna mu'ujizar AlQur'ani ne ta hanyar ambaton wadannan haruffa. Domin suna tabbatar wa larabawa cewa babu wanda zai iya kawo wani abu irin Alqur'ani, duk kuwa da cewa haruffansa su ne haruffan da suke magana da rubutu da su.
Allah ya siffanta wannan Alqur'ani da cewa, babu wani kokwanto a cikinsa,
- Allah describes this Quran as having no doubt in it,
wato duk abin da ya qunsa tabbatacce ne kuma gaskiya ne,
- that is, everything it contains is certain and true,
don haka ne ya zama shiriya ga masu taqwa,
yana nuna musu gaskiya da bayyana musu hukunce-hukunce wad'anda suka shafi aqidunsu da ibadunsu da kuma mu'amalolinsu.
- showing them the truth and explaining to them the rulings that affect their beliefs, their worship, and their dealings.
An kira Alqur'ani da sunan Littafi duk kuwa da kasancewarsa ba a tattara shi wuri guda ba a lokacin;
- The Quran was called the Book, even though it was not collected in one place at the time;
an yi haka ne domin a yi ishara zuwa ga cewa, nan gaba za a tattara shi wuri guda ya zama littafi wanda Musulmi a kowane lokaci za su riqa karantawa.
- This was done to indicate that in the future it would be collected in one place and it will become a book that Muslims would read at all times.
Sannan Allah swt yana fayyace siffofin masu taqwa wadanda Alqur'ani yake shiryar da su.
- Then Allah (swt) describes the characteristics of the pious people whom the Quran guides.
Sun siffantu da siffofi guda biyar kamar haka: <> They are described with five characteristics as follows:
- Suna yin imani da gaibu. Gaibu shi ne duk abin da manzanni suka zo da shi, suka ba da labarinsa, kuma ido bai gan shi ba. Wannan ya had'a da imani da ranar lahira da abin da ta ƙunsa na hisabi da mala'iku da labarin manzanni da littafan da Allah ya saukar gabanin zuwan Manzon Allah swt. Imani da gaibu shi ne yake bambance wa tsakanin mutum mumini da kafiri, saboda yana imani da duk wani abu da Allah ya ba da labarinsa ko Manzonsa ya fad'a ko da kuwa bai gano shi da hankalinsa ba.
- They believe in the unseen. The unseen is everything that the messengers brought, reported, and the eye has not seen. This includes belief in the Day of Judgment and what it entails, the angels, the stories of the prophets, and the books that Allah revealed before the coming of the Messenger of Allah (swt). Belief in the unseen is what distinguishes a believer from a disbeliever, because he believes in everything that Allah has reported or His Messenger has said, even if he does not understand it with his own mind.
- Suna tsayar da salla, wato suna yin ta kamar yadda shari'a ta koyar da su tare da kula da lokutanta da rukunanta da wajibanta da sharuɗɗanta.
- Suna ciyar da abin da Allah ya azurta su da shi. Sukan fitar da zakkar dukiyoyinsu, hakanan suna sadaka ta nafila da abin da Allah ya hore musu.
- Su ne waɗanda suke yin imani da Alƙur'anin da Allah ya saukar wa Annabi Muhammadu (SAW) gaba ɗaya ba tare da ware ɓangare ko sun riƙa tawilin karkatar da ma'anonin wani ɓangare na Alƙur'ani ba, kamar yadda 'yan bidi'a suke yi ga wasu ayoyin waɗanda ba sa goyon bayan bidi'o'insu da aƙidunsu. Hakanan suna yin imani da dukkan littattafan da Allah ya saukar wa manzanni da annabawan da suka gabata, har da su kansu manzannin da annabawan.
- Su ne waɗanda suka tabbatar da zuwan ranar tashin alƙiyama da abubuwan da za ta zo da su na tayar da matattu da yi musu hisabi da suka wa mutanen ƙwarai da Aljanna; masu miyagun laifuffuka kuwa a saka musu da wutar Jahannama. An ware batun imani da ranar lahira duk kuwa da cewa ya shiga cikin batun imani da gaibu, saboda a zaburar da mutane ga ayyukan alheri a kuma tsoratar da su game da munanan ayyuka.
Sannan Allah swt ya faɗi sakamakon masu waɗannan siffofi da cewa, suna kan wata shiriya mai girma daga Allah mai yi musu tarbiya ta ƙwarai. Domin babu wata shiriya da ta kai siffantuwa da waɗannan siffofi. Don haka su ne waɗannan suke da babban rabo daga Allah, wato samun yardar Allah da gidan Aljanna ranar gobe alƙiyama.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Girman mu'ujizar Alƙur'ani.
- The greatness of the miraculous Quran.
- Allah swt ya yi ishara zuwa ga cewa, za a tattara Alƙur'ani wuri guda don ya zama littafin da Musulmi za su riƙa ɗauka suna karantawa a kowane zamani.
- Allah (swt) has indicated that the Quran will be collected in one place so that it will be a book that Muslims will carry and read at any point in time.
- Alƙur'ani shiriya ne ga mutane masu taqwa. Watau masu kiyaye dokokin Allah. Gwargwadon taƙawar bawa gwargwadon yadda zai dace da shiriyar Alqur'ani. Wanda kuma ya rungume shi yana aiki da shi to babu shakka shiriyarsa za ta riƙa hauhawa tana ƙaruwa.
- The Quran is a guidance for the pious. That is, those who observe the laws of Allah. The measure of a servant's piety is as much as it is in accordance with the guidance of the Quran. And whoever embraces it and acts upon it, then undoubtedly his guidance will continue to increase and increase. (See also Quran/19/76)
- Duk abin da Alqur'ani ya qunsa gaskiya ne babu kokwanto ko kad'an a cikinsa.
- Everything the Quran contains is true, without the slightest doubt. (See also Quran/2/2, Quran/18/1, Quran/difference_from_raib_and_iwaj)
- Falalar yin imani da gaibu, domin shi ne abin da yake buqatar qarfin imani, sab'anin abin da kowa yake iya gani ko yake iya ji, wannan abu ne da babu mai iya musanta samuwarsa.
- Girman sha'anin tsai da salla, domin ita ce rukuni na biyu daga cikin rukunan Musulunci.
- The importance of establishing prayer, because it is the second of the pillars of Islam.
- Falalar ciyar da dukiya don Allah. <> The virtue of giving zakat and donating sadaqa for Allah's sake.
- Siffar masu taqawa ta ƙunshi bauta wa mahalicci ba kyautata wa mahluki.
- Imani da duk littattafan da Allah swt ya saukar wa manzanninsa, domin sanin cewa Allah swt bai bar bayinsa hakanan sakaka ba tare da bayyana musu hanyar shiriya ba.
- Shiriya da rabauta ba za su taɓa samuwa ga bawa ba sai ya rungumi wannan hanyar, ya siffantu da waɗannan siffofi.
Baqara 6-7
- Lalle waɗanda suka kafirta, duk ɗaya ne a gare su, ka yi musu gargaɗi ko ba ka yi musu ba, ba za su yi imani ba. --Quran/2/6
- Allah Ya toshe zukatansu da jinsu, kuma akwai wani lulluɓi a kan idanunsu, kuma suna da azaba mai girma. --Quran/2/7
Tafsiri:
A nan Allah yana ba da labarin kafirai ne da irin taurin kansu wajen kafirce wa abin da Annabi SAW ya zo da shi na gaskiya.
- Here, Allah is telling the story of the disbelievers and their stubbornness in rejecting what the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) brought as truth.
Allah ya faɗa wa Annabi (SAW) cewa, waɗannan kafirai sun kai matuƙa ga kafircinsu; yana da wuya wa'azinsa ya sa su saurare shi, har su yi imani, don haka kada kafircinsu ya dame shi.
- Allah told the Prophet (PBUH) that these disbelievers had reached the extreme of their disbelief; it was difficult for his preaching to make them listen to him and believe, so he should not be troubled by their disbelief.
Domin Allah ya riga ya toshe musu zukatansu saboda zunubbansu, don haka imani ba zai sami hanyar shiga cikinsu ba.
- Because God has already sealed their hearts because of their sins, faith will not find its way into them.
Kuma ya doɗe musu kunnuwansu saboda kafircinsu, don haka ba za su taɓa jin kiransa ba balle su amsa masa.
- And He has deafened their ears because of their disbelief, so they will never hear his call, let alone respond to it.
Sannan akwai yanar da ta rufe musu idanuwansu ta yadda ba za su taɓa ganin gaskiya ba balle su yarda da ita.
- And then there is a web/barrier that has blinded their eyes so that they will never see the truth, let alone believe it.
Saboda haka suka cancanci azaba mai girman gaske. <> Thus why they deserve a great punishment.
Wannan yana nuna cewa, kafirci idan ya yi yawa a tare da bawa yakan toshe masa dukkan ƙofofin samun shiriya,
- This shows that, when disbelief becomes too much in a person, it blocks all the doors to guidance.
duk kuwa yadda aka yi fama da shi ba zai taɓa karɓar gaskiya ba, don ba ya jin ta, ba ya ganin ta kuma ba ya fahimtar ta saboda tsatsar zunubi da kafirci da suka lulluɓe shi.
no matter how people struggle with him, he will never accept the truth, because he does not hear it, see it, or understand it due to the sheer sins and unbelief that have enveloped him.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Lallashin Annabi SAW da nuna masa kada damuwa ta hallaka shi saboda ganin mutanensa sun ƙi yin imani da gaskiyar da yake kiran su zuwa gare ta.
- Idan mai kira zuwa ga Allah SWT ya bayyana wa mutane gaskiya suka bijre masa, to wannan ba zai cutar da shi komai ba, domin shi ya sauke nayin da yake kansa.
- Annabi ko waninsa babu wanda ya san abin da Allah ya riga ya rubuta wa wadanda ake kira na shiryuwarsu ko ɓatansu, Allah ne kaɗai ya san haka.
- Tsananin haɗarin girman kai da bijire wa gaskiya da dogewa a kan kafirci, domin yin haka yakan toshe zukata har ya zamanto duk wani alheri ba ya ratsa su.
Baqara 8-10
- A cikin mutane kuma akwai wadanda suke cewa: "Mun yi imani da Allah kuma mun yi imani da ranar lahira," alhalin su ba muminai ne ba. --Quran/2/8
- Suna ganin suna yaudarar Allah ne da wadanda suka yi imani, amma kuwa ba kowa suke yaudara ba sai kawunansu, kuma su ba sa jin hakan. --Quran/2/9
- Akwai wata cuta (ta munafunci) a cikin zukatansu, sai Allah Ya ƙara musu wata cutar, kuma suna da wata azaba mai raɗaɗi saboda ƙaryar da suke yi. --Quran/2/10
Tafsiri:
Daga nan har zuwa aya ta 20 Allah SWT yana mana bayanin munafuƙai ne tare da fallasa su da bankaɗo munanan siffofinsu don kowa ya gane su a kowane lokaci a kuma kowane yanayi.
A lokacin da Annabi SAW yana zaune a Makka mutane kashi 2 ne: muminai sai kafirai. To amma bayan Musulmai sun yi hijira zuwa Madina, sai aka samu kashi na uku, su ne munafuƙai. Munafiki shi ne wanda yake bayyana Musulunci a bakinsa, amma yana ɓoye kafirci a zuciyarsa. Allah ya bayyana wasu siffofinsu a nan.
Yana daga cikin siffofinsu suka riƙa bayyana imani da baki amma suna ɓoye kafirci a zukatansu, shi ya sa Allah ya ce: "Waɗannan ba muminai ne ba." Kuma saboda wautarsu suna yin haka ne wai don a zatonsu suna yaudarar Allah ne tare da muminai, watau a tsammaninsu Allah bai san abin da suke ɓoyewa ba. Wannan ta sa idan yaƙi ya ɓarke tsakanin muminai da kafirai to su ba za a taɓa su ba, kuma ba za a taɓa dukiyarsu ba, sannan in an ci nasara a kan cewa, kawunansu kadai suke yaudara ba, domin babu mai cutuwa da abin da suke yi su kadai.
Allah ya ce, akwai cuta a zukatansu. Cutar kuwa ita ce ta shakka da ruɗani da munafunci, wannan ya sanya Allah ya ƙara musu wata cutar, domin duk sanda aka saukar da wata aya ga Annabi SAW to za su kafirce mata, sai cutar zukatansu ta ƙara hauhawa, haka za su yi ta rayuwa har mutuwarsu sannan su je su tarar da azaba mai radadi tana jiran su a lahira saboda ƙaryar da suke ƙirƙira da kuma ƙaryara Annabi SAW da suka riƙa yi.
Narrated Abu Huraira:
The Prophet (ﷺ) said, "The signs of a hypocrite are three: 1. Whenever he speaks, he tells a lie. 2. Whenever he promises, he always breaks it (his promise ). 3. If you trust him, he proves to be dishonest. (If you keep something as a trust with him, he will not return it.)" https://sunnah.com/bukhari:33 |
An karɓo daga Abu Huraira rA yana cewa:
"Manzon Allah SAW yana cewa: "Alamar munafiƙi 3 ce: 1. Idan ya yi magana sai ya yi ƙarya, 2. kuma idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, 3. idan kuma aka amince masa sai ya yi ha'inci." [Bukhari #33 da Muslim #59] |
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Faɗakarwa a kan haɗarin munafurci da munafukai.
- Furta kalamar shahada da baki kawai ba zai wadatar ba har sai zuciya ta ƙudurce ta, domin Musulunci na gaskiya shi ne miƙa wuya ga Allah SWT a zahiri da baɗini.
- Munafukai suna nuna wa Musulmi cewa sun yi imani, alhalin ƙarya suke yi ba su yi imani ba.
- Luɗufin da Allah ya yi wa muminai yayin da ya tona asirin munafukai tun da wuri.
- Tabbatar da cewa munafukai ba muminai ba ne samsam.
- Munafukai mayudara ne, don haka wajibi ne ga muminai su yi hattara da su.
- Duk yaudarar mayaudari a kansa za ta ƙare.
- Munafurci yana toshe basira, don haka duk wani munafuki ba ya fahimtar cewa kansa yake cuta.
- Munafurci muguwar cuta ce wadda idan mai ita bai yi saurin magance ta ba, to za ta yi ta ƙaruwa ne har ta kai shi ga aukawa cikin azaba mai raɗaɗi.
- Haɗarin ƙarya da ƙaryara gaskiya. Ƙarya a wurin munafiki ƙaruwa take yi koyaushe.
Baqara 11-13
- Idan kuma aka ce musu: "Kada ku yi ɓarna a bayan ƙasa", sai su ce: "Mu fa masu gyara ne kawai." --Quran/2/11
- Saurara, lalle su su ne maɓarnata, amma ba sa jin hakan. --Quran/2/12
- Idan kuma aka ce da su: "Ku yi imani kamar yadda mutane suka yi imani", sai su ce: "Shin za mu yi imani ne kamar yadda wawaye suka yi imani?" Saurara, lalle su ne wawayen, sai dai ba su sani ba. --Quran/2/13
Tafsiri:
Har ila yau, Allah yana ƙara bayyana wani mugun halin na munafuƙai wanda shi ne, duk sa'adda sahabbai za su yi musu wa'azi su nuna musu kuskurensu, su neme su da su tuba zuwa ga Allah, sai su riƙa yi wa sahabban kallon wasu wawaye jahilai marasa hankali da har suka yarda suka bar garuruwansu da gidajensu da dukiyoyinsu suka yi hijira don wai su yi addinin Musulunci; sai su nuna su fa ba za su taɓa yin wauta irin wannan ba. Sai Allah ya mayar musu da martani da cewa, ai ko su ne tsantsar wawaye, tun da har suka guje wa abin da zai amfane su na imani da Allah suka rungumi abin da zai cutar da su saboda tsabar jahilci da wauta.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Munafurci babbar ɓarna ce a bayan ƙasa.
- Yana daga cikin babban bala'i ga mutum a ƙawata masa mummunan aikinsa har ya riƙa ganinsa kyakkyawa.
- Haɗarin dake tattare da rikirkicewar tunani wanda zai kai ga maɓarnaci ya riƙa ɗaukan kansa mai shi mai gyara ne.
- Daga cikin mummunar siyasar munafukai a kowane zamani shi ne yadda suke sanya rigar masu kawo gyara cikin al'umma, masu fafutukar daidaita rayuwar jama'a, amma a fakaice suna yaƙi da addini da masu addini, suna yi wa abokan gabar Musulmi farfaganda domin lalata aƙidun Musulmi da kyawawan halayensu na addini da zamantakewa da shugabanci.
- Faɗakar da muminai da jawo hankalinsu a kan kada su ruɗu da da'awar munafukai da yaudararsu.
- Kiran munafukai zuwa ga abin alheri sau tari ba shi da wani amfani, domin yadda suke taƙama da marnar da suke kai yana ƙara musu bijire wa gaskiya.
- Faɗakar da Musulmi da kada su ruɗu da farfagandar Munafukai.
- Kariyar da Allah yake ba wa sahabban Annabi SAW da muminai.
- Tabbatar da hajilcin munafukai.
- Duk ɓarancin da ba ya gane cewa shi maɓarnaci ba ne, to shi wawa ne.
Baqara 14-15
- Idan kuma suka haɗu da waɗanda suka yi imani sai su ce: "Mun yi imani." To amma idan suka keɓanta da shaiɗanunsu (iyayen gidansu) sai su ce: "Mu fa lalle muna nan tare da ku, mu kwai izgili ne muke yi." --Quran/2/14
- Allah Yana yi musu izgili, kuma Yana yi musu talala cikin shisshiginsu suna masu ɗimuwa. --Quran/2/15
Tafsiri:
Wata muguwar sifa ta munafuƙai kuma har ila yau ita ce, yin fuska-biyu, wato idan sun shiga cikin muminai ko sun haɗu da su a hanya sai su riƙa nuna musu suna tare da su, su ma wai muminai ne. To amma da zarar sun koma ga manyan kafirai ko Yahudawa sai su nuna musu cewa, mu fa tare da ku muke, ku bar waɗancan muminai izgili kawai muke yi musu, amma zuciyarmu ba ta son su ko kaɗan. Allah SWT ya mayar musu da martani da cewa: Ai Allah ne yake yin izgili gare su, shi ya sa ya ƙyale su ba tare da ya ba wa muminai dama su gama da su ba, yake kuma ƙawata musu munanan ayyukansu, har ma suke zaton ko a kan gaskiya suke, ba su san cikin ɗimuwa da duhu suke rayuwa ba.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Ƙasƙancin munafukai da wulaƙanta kansu da suke yi da kuma nuna son duniya shi ne ya haifar musu da munafurci a zukatansu.
- Duk wanda zai riƙa nuna fuska-biyu ya kuma riƙa ɓoye rashin gaskiyarsa, to wannan ƙasƙantaccen mutum ne.
- Bayyana yadda munafukai suke haɗa kai da kafirai maƙiya Musulunci domin yaƙar Musulmi.
- Damuwar munafukai har kullum ita ce, yadda za su gamsar da 'yan'uwansu kafirai cewa, manufarsu guda ɗaya ce, kuma su fa imaninsu ba na gaskiya ne ba.
- Bayanin yadda Allah SWT yake kunyata munafukai, yake fallasa abin da suke faɗa wa kafurai a asirce.
- Haɗarin yi wa muminai izgili, domin yin haka siffa ce ta munafukai.
- Irin aikin mutum irin sakamakonsu, yadda munafukai suke yi wa muminai izgili su ma haka Allah SWT yake saka musu da yi musu izgili.
Aya 16
Waɗannan su ne suka musanya shiriya da ɓata, don haka kasuwancinsu bai yi riba ba, kuma ba su zamo shiryayyu ba.
Tafsiri:
A nan Allah SWT yana fito da haƙiƙanin matsayin munafuƙai, ta yadda suke nuna tsananin sha'awarsu da ƙaunarsu ga hanyar ɓata, suke ɗaukar ta a matsayin wata kadara mai daraja da za su iya kashe ko nawa ne don su mallake ta. Don haka suka amince su bayar da shiriya a matsayin kuɗin da za su fanshi wannan mummunar kadara (wato ɓata) da ita. Wannan shi ne haƙiƙanin kasuwancinsu a duniya; ashe kuwa wannan kasuwanci ne maras riba, kuma mai cike da hasara ta duniya da ta lahira.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Bayani game da tsantsar wautar munafukai da rashin basirarsu wadda har ta kai su suke fifita ɓata a kan shiriya, domin kuwa babu wautar da ta kai irin ta wanda zai ba da kuɗi tsababa don a ba shi wata lalatacciyar kadara.
- Duk wani attajiri yana fatan samun riba ne daga abin da zai kashe kuɗinsa ya saya. To haka su ma munafukai suna zaton cewa za su sami riba a cikin wancan lalataccen kasuwanci da suke yi, alhalin asara kawai suke tabkawa.
- Shiriyar Allah ita ce riba ta gaske. Duk wanda yake kan shiriya ta Allah SWT to shi ne mai samun ribar kasuwancinsa a duniya da lahira. Wanda kuwa ya rungumi ɓata kamar munafuki, to ya tabka hasara ta har abada.
- Sau tari munafukai ba su cika shiriyuwa su dawo kan gaskiya ba.
Baqara 17-18
- Misalinsu kamar misalin wanda ya wahala ga kunna wuta ne, yayin da ta haskaka abin da yake daura da shi, sai Allah Ya tafiyar da haskensu Ya bar su cikin duffai ba sa gani. --Quran/2/17
- Su kurame ne, bebaye ne, makafi ne, don haka ba za su taɓa dawowa (kan gaskiya) ba. --Quran/2/18
Tafsiri:
A nan ma Allah yana ƙara yi mana bayani ne a kan waɗannan munafuƙai, inda ya yi mana kwatance na zahiri domin mu fahimta da gaggawa; ya faɗa mana cewa, misa;in halin da munafuƙai suka tsinci kansu a ciki kamar misalin wani mutum ne da yake tafiya ya samu kansa cikin matsanancin duhu, ga tsoro da ya mamaye shi ta ko'ina, sai ya yi ta fafutukar neman haske, ya wahala sosai har ya samo wuta wadda ta haskaka masa kewayansa, ya zamanto yana ganin komai da ke gabansa da bayansa, ya daina jin tsoron da yake ciki a farko, ya fara farin ciki, sai kwatsam hasken ya ɗauke, ga wuta na ci gabansa balbal, ga zafinta yana bugo shi, amma kuma babu haske sai dai duhu yana dukan duhu; ga duhun dare, duhun hadari, ga na ruwan sama, ga duhun rashin haske, ya samu kansa cikin duffai daban-daban ba ya ganin ko da tafin hannunsa.
To haka sha'anin munafukai yake. Da farko suna rayuwa cikin duhun kafirci, sai Musulunci ya bayyana, sai suka ɗosani haskensa, suka sami kariya ta rayukansu da dukiyoyinsu. To amma da yake ba a kan gaskiya suka yi imani ba, sai hasken Musuluncin ya ɓace musu, yayin da suka mutu aka kai su ƙaburburansu, sai suka tsinci kansu cikin duhu na dukan duhu, ga duhun ƙabari, ga na kafirci, ga na munafunci, ga na saɓon Allah iri-iri, ga uwa-uba duhun wutar Jahannama. Tir da wannan makoma.
Dalilin haka ya sa Allah ya ce da su, su kurame ne ba sa jin duk wata gaskiya ji na fahimta; bebaye ne ba sa iya faɗin gaskiya, sannan makafi ne ba sa ganin gaskiya su bi ta. Don haka ne ma babu yadda za a yi su dawo kan hanya.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Fasahar Alƙur'ani wajen buga misalai don a fahimta.
pg30