Cutar daji ta kashe jarumin 'Black Panther', Chadwick Boseman
- DAGA IRO MAMMAN 29 AUGUST 2020 https://fimmagazine.com/hausa/index.php/labarai/591-cutar-daji-ta-kashe-jarumin-black-panther-chadwick-boseman Hausa pre special characters used https://regexr.com/5bin5 as well as the linkified https://regexr.com/3geqs
FITACCEN jarumin shahararren fim ɗin nan na Amerika mai suna 'Black Panther', wato Chadwick Boseman, ya rasu.
Jarumin, wanda ya taɓa fitowa a fim a matsayin wasu gwarazan Amurkawa baƙar fata, wato Jackie Robinson da James Brown tun kafin ya yi fim ɗin 'Black Panther' na kamfanin Marvel, ya rasu a ranar, Juma'a, 28 ga Agusta, 2020, ya na da shekara 43.
Iyalan sa sun ce cutar daji da ta kama hanjin sa, wato 'colon cancer', ita ce sanadin mutuwar tasa.
Jami'ar yaɗa labarai ta iyalin nasa, Nicki Fioravante, ta faɗa wa kamfanin dillancin labarai na The Associated Press cewa Boseman ya rasu a gidan sa da ke birnin Los Angeles na Amurka a lokacin da matar sa ta ke zaune a gefen sa.
Iyalin nasa sun faɗa a cikin wata sanarwa cewa Boseman ya shekara huɗu ya na fama da wannan cuta.
Iyalin su ka ce: "Mutum mai bajinta ƙwarai, Chadwick ya yi fama da wannan cutar, kuma a daidai lokacin ya ci gaba ya gabatar maku da yawancin finafinan nan da ku ke matuƙar so. Daga 'Marshall' zuwa 'Da 5 Bloods', da 'Ma Rainey's Black Bottom' na August Wilson da wasu finafinan da dama - duk an ɗauke su ne a daidai lokacin da ko kuma a tsakanin lokacin da ya ke shan magani ko ake masa tiyata kan wannan cuta. Abin alfahari ne a rayuwar sa ta sana'a har ya taka rawar fitowa a matsayin Sarki T'Challa a fim ɗin 'Black Panther'."
Boseman dai bai taɓa yin magana a bainar jama'a kan cutar da ke damun sa ba. Da ma shi mutum ne wanda bai cika shiga jama'a ba, kuma ya na kaffa-kaffa da magana ko hira, amma duk da haka ya kan so ya isar da bayani kan muhimmancin sana'ar sa da tasirin ta kan al'adu.
Ya rasu ya bar matar sa da kuma ɗaya daga cikin mahaifan sa, amma bai da ɗa, inji Fioravante.
An haifi Boseman a jihar Carolina ta Kudu, ya samu digirin sa a Jami'ar Howard, sannan ya riƙa fitowa a ƙananan rol na wasannin dirama a talbijin kafin a ba shi babban rol a matsayin jarumi a cikin 2013.
Tun a farkon fara sana'ar sa a Hollywood, Boseman ya bayyana matsayin 'yan fim baƙar fata a masana'antar, inda ake nuna masu wariya. Ya faɗa a wata hira a lokacin tallata fim ɗin '42' cewa: "Idan kai ɗan wasa baƙar fata ne, abin da za ka ci karo da shi ya bambanta da wanda ɗan wasa farar fata zai ci karo da shi. Ba za ka samu dama kamar shi ba. Wannan a bayyane ya ke, kuma gaskiya ne.
“Abin da ya fi dacewa a faɗa shi ne: Sau nawa ka ke ganin fim game da wani gwarzo baƙar fata wanda ke da labarin soyayya … ai ya na da ruhi shi ma. Ya na da tunani. Za a ji wani iri idan an faɗi haka, amma ba ko yaushe ba ne ake ganin wannan ɗin."
Da aka tambaye shi gwarzayen da ya ke so tun ya na yaro, sai Boseman ya ambaci wasu manyan 'yan siyasa da mawaƙa, wato Malcolm X, Martin Luther King Jr., Bob Marley, Public Enemy, A Tribe Called Quest da kuma Prince.
Rol ɗin da ya yi na ɗan wasan ƙwallo ɗin nan Jackie Robinson, inda ya fito tare da shahararren jarumi Harrison Ford a fim ɗin '42' wanda ya fita a cikin 2013, shi ne ya jawo masa farin jini a masana'antar finafinai ta Hollywood inda daga nan ya zama tauraro.
Bayan shekara ɗaya, ya ƙara burge masu kallo a matsayin James Brown a fim ɗin tarihin mawaƙin, wato 'Get On Up'.
Wasan sa a matsayin T'Challa ya fara fita ne tun a mashahurin fim ɗin kamfanin shirya finafinai na Marvel a cikin 2016 mai suna 'Captain America: Civil War', sannan gaisuwar da ya riƙa yi da taken "Wakanda Forever" ta mamaye duniya bayan fitowar fim ɗin sa na 'Black Panther' shekara biyu da su ka gabata.
'Black Panther', fim na farko da wani babban kamfani a Amerika ya shirya tare da yawancin 'yan wasa baƙar fata, ya kasance ɗaya daga cikin finafinan da su ka fi wazgo riba a shekarar.
An yi cinikin dala biliyan 1.3 a sinima a faɗin duniya kuma shi kaɗai ne fim ɗin kamfanin Marvel Studios da aka zaɓa a matsayin 'best picture' a gasar Oscar.
Ya ci matsayi uku a gasar ta Academy Awards - wato 'best original score', 'best costume design' da 'best production design'.
Finafinan Boseman na ƙarshe sun haɗa da fim ɗin gumurzu da aka yi a bara mai suna '21 Bridges', da fim ɗin darakta Spike Lee mai suna 'Da 5 Bloods' inda ya fito a matsayin jagoran wasu sojoji baƙar fata a Yaƙin Vietnam, da kuma na ƙarshen, wato fim ɗin 'Ma Rainey’s Black Bottom' na August Wilson wanda kamfanin Netflix ya ɗauki nauyin shiryawa. A wannan fim, Boseman ya fito ne tare da jaruma Viola Davis.
Labarin mutuwar Boseman ya girgiza 'yan fim da masoyan sa matuƙa, inda aka dinga bayyana alhini a soshiyal midiya.
Shugaban kamfanin Marvel Studios, Kevin Feige, ya faɗa a wata sanarwa ga manema labarai cewa: “Rasuwar Chadwick ta yi matuƙar ragargaza mana zuciya. Shi ne T’Challa ɗin mu, shi ne Black Panther ɗin mu, kuma babban abokin mu. A duk lokacin da ya shigo filin ɗaukar fim, ya kan haske wurin da kwarijin sa da farin cikin sa, kuma a duk lokacin da ya fito a fim, ya kan haifar da wani abu da ba za a iya kankarewa daga zuciyoyin masu kallo ba. Ya wakilci mutane masu burgewa da dama a finafinan sa, kuma babu wanda ya fi shi iya fitowa a matsayin manyan mutane a fim. Ya na da burgewa da kuma kirki da iko da ƙarfi kamar irin mutanen da ya ke fitowa a matsayin su. Yanzu ya shiga jerin su a matsayin wanda ba za a taɓa mantawa da shi ba. Mu iyalan The Marvel Studios mu na matuƙar alhinin rashin sa, kuma a wannan dare mu na taya iyalan sa baƙin ciki.”
Jarumi Mark Ruffalo, wanda ya fito tare da Boseman a matsayin Hulk a finafinan Marvel, ya ce abin alfarma ne a gare shi a ce sun yi fim tare da Boseman. Ya ce: “Dukkan abin da zan ce shi ne al'amuran baƙin ciki da su ka faru a wannan shekara sun ƙaru ta hanyar wannan mutuwa ta Chadwick Boseman. Nagartaccen mutum ne, mai zurfin basira."
Shi ma Don Cheadle, wanda ya fito tare da Boseman a finafinan kamfanin Marvel, ya tura hoton su su biyu tare da faɗin: “Ba zan manta da kai ba, ɗan'uwa na abokin ranar haihuwa ta. Ko yaushe ka kasance haske da soyayya a gare ni. Abin so na … har abadar abadin …”
Darakta kuma jarumi Jordan Peele ya rubuta a Twitter: "Wannan abu ya dagargaza ni". "Wannan mutuwa ta karya min zuciya," inji jarumi kuma marubuci Issa Rae.
Jarumin shirin 'Captain America' Chris Evans ya kira Boseman da sunan "orijina ne na gaske. Ɗan wasa ne mai matuƙar sadaukarwa tare da neman sani a ko yaushe. Ya bar manyan ayyuka da dama da za a iya ƙirƙira tare da shi." Shi kuma abokin wasan Boseman a finafinan kamfanin Marvel, Mark Ruffalo, shi ma ya ce a Twitter: "Ɗan'uwa, ka na daga cikin manyan mutane na kowane ƙarni kuma bunƙasar ka farko ce ma. Allah na son ka. Allah ya jiƙan ka cikin iko, ya kai Sarki."
Shi ma ɗan takarar zama shugaban ƙasa a jam'iyyar Democrat, Joe Biden, ya faɗa a Twitter cewa Boseman "ya saka wa mutane manya da ƙanana tunani a ran su cewa za su iya zama duk abin da su ke so su zama - ko da kuwa su zama manyan jarumai ne."
Saƙon ƙarshe da Boseman ya tura a Twitter shi ne inda ya bayyana shauƙin goyon bayan sa ga 'yar takara zama mataimakiyar shugaban ƙasa ta jam'iyyar Democrat, wato Kamala Harris. Ita ma Kamala Harris ɗin ta tura saƙon ta'aziyyar rasuwar jarumin inda ta kira shi “mai hazaƙa, mai kirki, masani, kuma mai ƙasƙantar da kai."
Babbar ƙungiyar ƙwatar 'yancin baƙar fatan Amurka, wato NAACP, ta yabi Boseman saboda "ya nuna mana yadda ake cin galabar gaba ta hanyar haƙuri da juriya" da kuma "yadda ake tafiya a matsayin Sarki ba tare da an manta da tausayin jama'a ba." Ta kammala da cewa: "#RestInPower #BlackPantherForever."