Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/023 anger outlet

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

#: Need to smash a printer with a baseball bat? Now you can. [1] <> Ko me ya sa yawan fushi tsakanin maaikata ke karuwa? Kana son lalata na'urar gurza takarda yayin da ka fusata ? [2]

#: The people you work with [3] <> Shin ko mutanen da kake aiki tare da su [4]

#: are driving you nuts and youd love nothing more than to scream at them at the top of your lungs. [5] <> suna harzuka ka har ba abun da kake so illa ka yi musu ehu tare da tayar da hakarkari ? [6]

#: Sure, youd feel so much better venting your rage, [7] <> Hakika, za ka fi samun sauki idan ka amayar da abunda ke cikinka, [8]

#: but overt anger remains a taboo at the office. [9] <> sai dai rashin boye fushin wani abu ne da ba'a cika so ba a wajen aiki. [10]

#: In some cases, [11] <> A wasu lokuta [12]

#: it could get you fired. [13] <> hakan yana janyo a kore ma'aikaci daga aiki. [14]

#: Most of us instead keep a tight lid on our fury. [15] <> Akasarin mu mun fi son boye fushin mu. [16]

#: Still, ‘office rageis real and a growing concern, [17] <> Sai dai da gaske fushi a wajen aiki yana ci gaba da zama abun damuwa [18]

#: according to experts. [19] <> kamar yadda masana ke cewa. [20]

#: Lucy Beresford, a psychotherapist and relationship expert, [21] <> Lucy Beresford wata kwararriya ce kan halayyar Adam [22]

#: who studied the phenomenon in a 2007 report for Canon Europe. [23] <> wacce ta yi nazari akan wannan matsala a shekarar 2007 a nahiyar turai. [24]

#: Office life is increasingly frustrating and many workers feel powerless with little control, her research found. [25] <> n/a [26]

#: Lucy Beresford says [27] <> A cewar Lucy Beresford, [28]

#: Eighty-three percent of us have seen a colleague [29] <> kashi 83 cikin 100 na ma'aikata sun taba ganin yadda wani abokin aikin su [30]

#: lose their temper at work [31] <> ya fusata a wajen aiki yayin [32]

#: and 63% of us have lost our temper, according to her study. [33] <> da kashi 63 suka taba harzuka a cewar bincikenta. [34]

#: Other studies show similar statistics. [35] <> Wasu bincike daban daban da aka gudanar sun nuna irin wannan kiyasi. [36]

#: Are we giving people permission to get angry in a safe environment [37] <> Shin ko muna ba mutane damar su fusata a wuraren da suka dace ? [38]

#: Among the worst office irritants: [39] <> Daga cikin abubuwan da ke tada hankali a wajen aiki sun hada da [40]

#: computer crashes, [41] <> sukurkucewar na'urar kwamfuta, [42]

#: uncooperative printers, [43] <> matsalar na'urar gurza takarda, [44]

#: annoying, [45] <> fushi, [46]

#: lazy colleagues [47] <> abokan aiki wadanda ba su da kwazo yin aiki [48]

#: and inconsiderate bosses. [49] <> da kuma shugaban da bai san ya kamata ba. [50]

#: Unsurprisingly, [51] <> Wani abun rashin mamaki kuma shine [52]

#: receiving after-hours work emails [53] <> samun wasikar email a lokacin da mutum ya tashi daga wurin aiki [54]

#: had a similar effect according to a 2015 study [55] <> na janyo irin wadannan matsaloli kamar yadda wani bincike [56]

#: study from the University of Texas at Arlington. [57] <> da aka gudanar a jami'ar Texas a Arlington a shekarar 2015 ya gano. [58]

#: But there might be a better solution [59] <> Sai dai akwai hanyoyi da suka fi dacewa [60]

#: to bottling up the boiling waters, [61] <> don magance yanayin da mutum ya harzuka, - [62]

#: one that lets off steam and keeps you employed. [63] <> wato mutum ya shiga wani daki inda zai fitar da fushin sa, a wasu lokuta da taimakon karamar sanda na wasan kwallon gora. [64]

#: Enter rage rooms, a trend for a safe space [65] <> A wurin sai ka fitar da fushinka wajen farfasa wani abu, [66]

#: where you can unleash your full angersometimes with the help of a baseball bat. [67] <> yayin da zaka bar wani mutum ya kwashe tarkacen daka farfasa. [68]

#: Here, the stressed-out pay to smash items of their choosing and leave someone else to clean up the wreckage. [69] <> Rayuwar wajen aiki na ci gaba da zama abun takaici ga wasu ma'aikata da dama har ta kaiga wasu ma'aikata na ganin basu da yadda zasu yi, kamar yadda bincikenta ya gano. [70]

#: Were giving people permission to get angry [71] <> "Ya ce muna ba mutane dama su amayar da fushin su [72]

#: in a safe environment,” says Ed Hunter, [73] <> a wani wuri da ba shi da hadari," in ji Ed Hunter, [74]

#: founder of The Break Room, [75] <> mutumin da ya kirkiro The Break Room, [76]

#: which opened in Melbourne, Australia, in March. [77] <> da aka bude a birnin Melbourne na kasar Australia, a watan Maris. [78]

#: Its a fairly natural rebellion.” [79] <> "Wannan wata hanya ce na bijirewa." [80]

#: Work stress [81] <> Gajiya a lokacin aiki [82]

#: is a growing concern for both Aussie employers [83] <> na ci gaba da zama abun damuwa ga masu kamfanin Aussie [84]

#: and employees according to a report by health insurer Medibank Private. [85] <> da ma'aikatan su kamar yadda rahoton da kamfanin inshorar lafiya Medibank Private ya fitar. [86]

#: Work-related stress [87] <> Gajiya a lokacin aiki [88]

#: costs Australian business AUD$10 billion a year, [89] <> ya janyowa 'yan kasuwar Australia asarar dala biliyan $10 a shekara [90]

#: according to a 2013 report by independent body Safe Work Australia. [91] <> a cewar wani rahoto da aka fitar a 2013. [92]

#: People love to smash printers. [93] <> Mutane su kan yi sha'awar su farfasa na'urar gurza takarda, [94]

#: We go through more than 15 printers a week [95] <> muna duba irin wadannan na'urori kusan 15 a kowane mako. [96]

#: Were always told not to break things, to control anger, [97] <> "An shaida mana cewa kada mu farfasa wasu abubuwa domin huce fushin mu, [98]

#: to be well-behaved,” says Stephen Shew, [99] <> mu natsu in ji Stephen Shew, [100]

#: co-founder Battle Sports in Toronto, Canada, [101] <> wanda yana cikin wadanda suka kirkiro wasannin Battle Sports a Toronto na Canada, [102]

#: which has a Rage Room amongst other offerings and opened in July 2015. [103] <> wurin da ke da wani daki na amayar da fushi da sauran abubuwa da aka bude a watan Afrilun 2015. [104]

#: Or, ‘if you break things [105] <> "Ko kuma idan ka farfasa wasu abubuwa [106]

#: you have to buy them’. [107] <> to tilas sai ka sayo su ka mayar'. [108]

#: But in the rage room, they can do just that and not get in trouble.” [109] <> Amma idan a dakin huce takaici ne, za ka iya yin haka ba tare ka shiga wata matsala ba." [110]

#: Plus, its fun. [111] <> Huce takaici akan na'urar [112]

#: Rage against the machine [113] <> Kamfanin Battle Sports ya gano cewa wasu na'urorin da ake amfani da su a wuraren aiki na jan hankulan ma'aikata. [114]

#: People love to smash printers. [115] <> "Mutane suna son farfasa na'urar gurza takarda. [116]

#: We go through more than 15 printers a week,” says Shew. [117] <> Muna duba irin wadannan na'urori kusan 15 a kowane mako, in ji Shew. [118]

#: Its the quintessential representation of an office environment,… [119] <> Wuraren da suka bi sahu wajen samar da dakunan da ake huce takaici tare da farfasa abubuwa [120]

#: include the Rage Room in Budapest [121] <> sun hada da Rage Room da ke Budapest [122]

#: and several businesses in the US [123] <> da wasu wuraren kasuwanci a Amurka [124]

#: such as the Anger Room in Dallas, Texas; Tantrums LLC in Houston, Texas; and the Smash Shack in Jacksonville, North Carolina. [125] <> kamar Anger Room a Dallas, Texas da Tantrums LLC a Houston, Texas da kuma Smash Shack da ke Jacksonville, a North Carolina. [126]

#: Fuel to a flame [127] <> Kara harzuka mutum [128]

#: So is this kind of aggression really an effective salve for stress? Well, no. [129] <> Ko irin wadannan yanayi na fusata na taimakawa wajen kawadda gajiya? Amsar ita ce a'a. [130]

#: Fuel to a flame [131] <> Domin kamar zuba fetur ne akan wuta. [132]

#: Rage isnt the best way to deal with your anger, [133] <> Harzuka ba ita ce hanyar da ta fi dacewa ba wajen magance fushi, [134]

#: says professor Brad J Bushman of The Ohio State University, by email. [135] <> in ji Farfesa Brad J Bushman na jami'ar jihar Ohio. [136]

#: Bushman published a study in 2002 that showed Catharsis theory[137] <> Bushman ya wallafa a wani bincike da aka gudanar a 2002 daya nuna cewa[138]

#: acting aggressively or viewing aggression is an effective way to purge angerjust doesnt work. [139] <> Harzuka a matsayin wata hanya ta fitar da fushi ba ta aiki. [140]

#: Indeed, doing nothing at all was more effective. [141] <> Domin rashin yin wani abu ya fi alfanu. [142]

#: It is like using gasoline to put out a flame. [143] <> "Tamkar zuba fetur ne don kashe wuta, [144]

#: It just feeds the flame. [145] <> zai kara tada wutar ne. [146]

#: Angry people are highly aroused (heart rate, blood pressure), and venting keeps arousal levels high. Bushman says. [147] <> Mutanen da suka fusata na shiga cikin wani yanayi da zai sa jinin su ya hau, kuma a lokacin da suke amayar da fushin su, zai sa jinin su ya ci gaba da tashi, in ji Bushman [148]

#: Bushman suggests instead [149] <> Sai dai Bushman ya bada shawarar cewa maimakon haka, [150]

#: using delay tactics to let the anger dissipate, [151] <> sai a yi dubara da za ta sa fushin ya fita a hankali [152]

#: distracting yourself [153] <> ta hanyar kawadda hankalinka [154]

#: or doing something incompatible with anger such as such as watching a (non-violent) funny movie. [155] <> wajen yin wani abu da bashi da alaka da abun da ya saka harzuka, kamar kallon wasanni ko fina-finai da zasu sa ka dariya. [156]

#: No cure-all [157] <> Babu magani [158]

#: Of course, rage room customers prefer the more smashing approach to trying to resolve workplace anger, jilted love, heartbreak and mire. [159] <> Hakika dakunan da ake samar wa don huce takaici mutane sun fi son yadda zasu farfasa abubuwa don huce fushi daga wurin aiki ko kuma cin amana tsakanin masoya ko kuma tsananin bacin rai. [160]

#: The rage room is not a cure-all for your anger [161] <> Irin wadannan dakuna na huce takaici basa magance dukkan fushin ka. [162]

#: Shew says Women make up about 60% of rage room partakers. [163] <> Shew ta ce kashi 60 cikin 100 na wadanda suka fi zuwa irin wadannan dakuna na huce takaici mata ne. [164]

#: Keep calm and carry on [165] <> Ka natsu ka ci gaba da rayuwa [166]

#: Dont get Hangry: The emotion people have the most difficulty controlling is anger. But with the fuel obtained from healthy foods, the brain is better able to control it. [167] <> •Kada ka yi fushi: Mutanen da ke da sanyin rai an fi shan wahala wajen shawo kansu idan suka fusata, amma idan aka samu abinci mai gina jiki kwakwalwa tafi iya sanyaya zuciya. [168]

#: Delay: Let the anger dissipate, count to 10 before responding. If really angry, count to 100! [169] <> •Jinkiri: Ka natsu ka bari hankalinka ya kwanta, ka kirga 1- 10 kafin ka maida martani. Idan kuma ka yi matukar fusata to ka kirga 1-100! [170]

#: Relaxation: Chill out, take deep breaths or listen to calming music. [171] <> •Shakatawa: Ka huta ka ja dogon numfashi ko kuma ka saurari wakoki masu sanyaya rai. [172]

#: Distraction: Think about something else, try working on a crossword puzzle. [173] <> • Yi wani abu dabam: Ka tuna wani abu dabam ko kuma ka gwada yin wasannin na wasa kwakwalwa. [174]

Contents