Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/080-earths-saltiest-place

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
  1. Alignment-in-progress
  2. http://www.bbc.com/earth/story/20160809-earths-saltiest-place-makes-the-dead-sea-look-like-tapwater
  3. https://www.bbc.com/hausa/mujalla/vert_earth/2016/08/160826_vertocals_the_saltiest_place_on_earth

--[[bbchausa_verticals/080-earths-saltiest-place|bbchausa_verticals/080]]

2. BBC - Earth - Earth's saltiest place makes the Dead Sea look like tapwater

2. Ka san wurin da yafi ko’ina gishiri a duniya?
3. The Dead Sea 3. Tafkin Bahar Mayit ‘Dead Sea’
4. is famous 4. ya yi matukar shuhra
5. for its unusually salty water, 5. kan tsananin gishirin ruwansa,
6. but it is actually only the fifth saltiest on the planet 6. amma a duniya shi ne na biyar a jerin wurare masu yawan gishiri.
7. By Ella Davies 10 August 2016 7. 26 Agusta 2016
8. If you think the sea is the saltiest place on Earth, 8. Idan ka na zaton teku ne yafi ko’ina gishiri a duniya,
9. you are mostly right. 9. ka na bisa turba.
10. Water makes up more than two-thirds of our planet's surface, 10. Kaso biyu cikin uku na duniya ruwa ne,
11. and 96% of Earth's water is in the ocean. 11. kuma kaso 96% na ruwan da ke duniya ya na cikin teku.
12. It contains thousands of billions of tonnes of dissolved salt. 12. Akwai biliyoyin ton na narkakken gishiri a cikin ruwan teku.
13. The saltiness varies. 13. Sai dai yawan gishirin kan bambanta,
14. Around the poles, 14. a kuryoyin arewa da kudu,
15. snow and ice dilute the salt, 15. dusar kankara kan narke ta salanta gishirin,
16. while nearer the equator evaporation means the water is saltier. 16. a yankunan da ke tsakiyar duniya kuma zafin rana na sa ruwa ya ragu, don haka sai dandanon gishirin ya karu.
17. But there are places on our planet where you can find water far saltier than the sea. 17. Duk da haka akwai wasu wurare a cikin duniyar nan da su ka fi ruwan teku yawan dandanon gishiri.
18. Few are more famous than the Dead Sea, 18. Wanda yafi shahara a cikinsu shi ne tafkin Bahar Mayit ‘Dead Sea’
19. nestled on the borders of Jordan and Israel. 19. da ke kan iyakar Jordan da Isra’ila.
20. The water here is around 10 times saltier than sea water. 20. Dandanon gishirin kogin ya nunka na teku sau 10.
21. However, it is only the fifth saltiest body of water on Earth. 21. Sai dai a jerin wurare masu tsananin gishiri a lamba ta biyar ya tsaya.
22. It is also not really a sea. Although the word "sea" is used quite freely, it actually denotes a large body of salt water that is partially enclosed by land. 22. Kalmar ‘sea’ a Ingilishi na nufin babban ruwan gishiri da kasa ta yi wa katanga.
23. The Dead Sea is entirely land-locked, 23. Shi kuwa ‘Dead Sea’ kasa ta yi masa kawanya ne baki daya,
24. so really it is a lake. 24. don haka tafki ne
25. It is the saltiness that causes confusion. 25. amma saboda tsananin gishirinsa ake kiransa ‘teku
26. The rocks at the water's edge glitter with crystallised sodium chloride where the Sun evaporates the water. 26. Duwatsun da ke gabar tafkin na kyalkyali da rana saboda hasken gishirin da ya damfare musu daga ruwan.
27. It is the world's deepest hypersaline lake, 27. ‘Bahar Mayit’ shi ne tafki mai tsananin gishiri mafi zurfi a duniya,
28. reaching a depth of 1,080ft (330m), and is widely known as the lowest point on land. 28. inda ya ke da zurfin kafa 1,080 daidai da mita 330.
29. The shoreline is around 1,380ft (420m) below sea level, but the water level does fluctuate. 29. N/A
30. The waters of Don Juan Pond in Antarctica are 44% saline. 30. Amma ruwan da yafi kowanne dandanon gishiri shi ne Kududdufin Don Juan da ke nahiyar Antarctica inda kaso 44% na ruwansa gishiri ne.
31. It is tiny: at 4in (10cm) deep it is barely enough to paddle in. 31. Ba shi da zurfi ko kadan domin kuwa iyakarsa inchi hudu daidai da santimita 10.
32. The cause for its hyper-salinity is not entirely understood 32. N/A
33. The surrounding environment does not exactly lend itself to spa treatments either. 33. N/A
34. The pond was found in the McMurdo Dry Valley, 34. An gano kududdufin ne a kwarin McMurdo Dry Valley,
35. an extreme desert environment cut off by mountains 35. wani yankin hamada da tsaunuka su ka tare,
36. where no snow falls. 36. inda ko dusar kankara ba ta sauka.
37. Don Juan Pond was not named after the fictional libertine, but rather after the two helicopter pilots that discovered it on the notoriously inaccessible continent. 37. N/A
38. "The cause for its hyper-salinity is not entirely understood," 38. “Ba a dai kai ga tantance dalilin da ya sa ya ke da wannan tsananin gishirin ba
39. says geologist Jay Dickson of the California Institute of Technology in Pasadena. 39. in ji masanin yanayin kasa Jay Dickson na Cibiyar Fasaha ta California da ke Pasadena,
40. He has spent years studying the pond, using time-lapse photography to record how it changes. 40. wanda ya kwashe shekaru ya na nazarin yankin.
41. "An important factor – but not a unique property of Don Juan Pond – is that it is a closed basin," says Dickson. 41. “Wani muhimmin abu game da Don Juan shi ne ba shi da hanyar da ruwa ke zurarewain ji Dickson.
42. "An open basin is one that has water flow into it and a channel through which it drains. A closed basin doesn't have this, so any water and salt brought into the pond can't get out." 42. “Don haka duk ruwa ko gishirin da ya shiga ciki ba shi da hanyar fitaDon haka sai dai ruwan ya daskare ko kuma rana ta kona shi.
43. "Don Juan Pond has so much salt that the temperature would have to be -53C for it to freeze, 43. “Yawan gishirin Don Juan ya sa ruwan ba zai iya daskarewa ba har sai tsananin sanyi ya kai -53C,
44. so the water evaporates, 44. don haka sai dai ruwan ya kone
45. leaving the salt behind with some water," he says. 45. ya bar gishirin da dan ruwa kadan
46. "This is part of how it gets so concentrated." 46. Wannan na daga cikin dalilan yawan gishirin kududdufin.
47. While other ponds in Antarctica are fed fresh water by nearby glaciers, 47. Yayin da raguwar kududdufan da ke Antarctica ke cike da ruwan dadi daga tsaunukan kankarar
48. which melt in the summer, 48. da kan narke a lokacin zafi,
49. Don Juan Pond is not diluted in this way. 49. Don Juan ba ya samun wannan ruwan dadin.
50. Dickson says researchers are still trying to find out where the salt water comes from. 50. Dickson ya ce masu bincike na nan su na kokarin gano daga inda ruwan gishirin ya samo asali.
51. But since salinity describes salt dissolved in water, 51. Amma in dai neman wurin da yafi tsananin gishiri a duniya mu ke yi,
52. we have to move from liquids to solids to find a truly record-breaking accumulation of the mineral. 52. sai mun bar cikin ruwa mun koma kan daskararrun abubuwa.
53. The largest salt flat in the world is found in Bolivia. 53. Mafi girman wurin da ake samun gishiri a duniya ya na kasar Bolivia.
54. Salar de Uyuni measures more than 4,050 square miles (10,500 sq km) 54. Salar de Uyuni ya kai fadin murabba’in kilomita 10,500
55. and was formed when a prehistoric mega-lake dried up. 55. kuma ya samo asali ne daga kafewar wannan tafkeken tafki shekaru aru-aru da suka wuce.
56. The basin is now paved with bloated hexagonal salt crystals that stretch as far as the eye can see. 56. A yanzu haka fegin cike ya ke da bangoran gishiri iyakar ganin mai gani.
57. As its description suggests it is remarkably flat, varying in height by less than 3.3ft (1m). 57. n/a
58. Tourists flock to the area to admire its seemingly otherworldly appearance, 58. ‘Yan yawon bude ido kan yi tururwar ziyarar wurin domin kallon ikon Allah,
59. while flamingos visit to breed. 59. yayinda tsuntsayen ‘flamingo’ ke yin kwanci a wurin.
60. Beneath the stark crystalline crust there is brine, 60. Karkashin bangoran gishirin akwai wani gurbataccen ruwan gishiri
61. which is rich in minerals. 61. da ke makil da sinadirai masu amfani.
62. Among other things, it contains half the world's supply of lithium. 62. Daga cikinsu, akwai rabin sinadirin ‘lithium’ na duniya baki daya.
63. The Bolivian government has recently started extracting the valuable soft metal, 63. Gwamnatin Bolivia ta fara hako sinadirin,
64. which is used to make the batteries in our electronic gadgets. 64. wanda ake amfani da shi wurin yin batirin kayayyakin laturonin da muke amfani da su.
65. Salt has been extracted from Salar de Uyuni for centuries. 65. Ana hakar gishiri a Salar de Uyuni tsawon daruruwan shekaru.
66. Nevertheless, the miners, who used pick-axes and shovels to dig and pile up the salt to dry, have barely scratched its surface. 66. Sai dai, mahakan, da ke amfani da diga da shebur wurin hakar gishirin tsawon shekarun nan kamar sakace su ke masa idan aka kwatanta da yawansa.
67. Other places, 67. Wasu wuraren,
68. encouraged by the constant demand for salt – 68. inda ake matukar bukatar gishiri –
69. both for food and to sprinkle on icy roads in winter – 69. domin abinci ko barbadawa a hanya domin narka kankara da sanyi –
70. have extracted far more of the white stuff. 70. sun hako gishirin fiye da Salar de Uyuni.
71. One of the world's biggest exporters of salt is Australia. 71. Daya daga cikin kasashen da tafi kowacce fitar da gishiri a duniya ita ce Australia.
72. It produces 11 million tonnes of the stuff each year, 72. Duk shekara ta kan samar da ton miliyan 11 na gishiri,
73. and sends 90% of it to overseas markets. 73. inda ta kan fitar da kaso 90% zuwa kasuwannin duniya.
74. Salt fields also contribute to China's world-beating salt production figures. 74. China ma na daga cikin wadanda su ka yi fice wurin samar da gishiri a duniya.
75. According to the 2016 figures from the US Geological Survey (USGS), 75. Wasu alkaluma da aka fitar a Amurka a 2016 sun nuna cewa
76. China produces more than 70 million tonnes per year. 76. China na samar da ton miliyan 70 na gishiri a kowacce shekara.
77. What they cannot harvest from above ground 77. Abinda ba za su iya kwasa a ban kasa ba,
78. they extract from below, either in the form of brine pumped out, or rock salt quarried or mined with explosives. 78. sai su haka rami su sa na’urar tunkudo ruwan gishiri ko kuma su hake tsaunukan gishiri ta hanyar amfani da nakiyar fasa dutse.
79. The world's single largest salt mine is in Goderich, Canada. 79. Mafi girman ramin hakar gishiri a duniya ya na Goderich, Canada.
80. The mine, operated by Compass Minerals, 80. Ramin, mallakar kamfanin Compass Minerals
81. reaches a depth of 1,800ft (549m): it is as deep as Toronto's CN Tower is tall. It stretches for 2.7 square miles (7 sq km) and 81. ya kai zurfin kafa 1,800 da fadin murabba’in kilomita bakwai,
82. produces 7.25 million tonnes of salt every year. 82. inda ya kan samar da ton miliyan bakwai na gishiri a kowacce shekara.
83. Its location on the edge of the Great Lakes is the key to its productivity. 83. Kasancewar ramin a yankin Manyan Tafkuna shi ne sirrin samar da gishirin da yawa.
84. There is a large, ancient source of salt beneath the area, which extends under the Canadian border into the north-eastern US. It is the remains of a prehistoric sea from around 420 million years ago. 84. Saboda a yankin an yi wani makeken teku da ya kafe kimanin shekaru miliyan 420 da su ka wuce.
85. Europe also has an impressive stash of minerals. Known as the Zechstein basin, it formed during the Permian period 270-250 million years ago. The area extends from northern Britain, across the North Sea through the Netherlands, Denmark, Germany and Poland. 85. A nahiyar Turai kuwa, manyan cibiyoyin samun gishiri sun hada da arewacin Burtaniya, zuwa kogin Tekun Arewa ‘North Sea’ har zuwa ga Netherlands da Denmark da Jamus da kuma Poland.
86. A comprehensive review published in 1969 suggested that the Upper Kama Basin, west of the Urals, is home to some of the world's largest deposits of rock salt and sodium chloride brines. 86. Sai dai kuma tsaunukan gishiri mafiya girma a duniya, su na kasar Rasha ne a yankin Upper Kama da ke yamma da tsaunukan Urals.
87. As far back as the 15th Century, the town of Solikamsk was established above the basin for salt-mining. 87. Tun cikin karni na 15 kididdigar Kirista aka kafa garin Solikamsk a yankin domin hakar gishiri.
88. It still produces potash (potassium salts) today. 88. Har yanzu kuwa ana samar da kanwa daga wurin.
89. "It's hard to pin this down," 89. “Zai yi wuya mu san inda yafi gishiri a duniya
90. says Ted Nield, editor of the Geological Society's Geoscientist magazine. 90. in ji Ted Nield, editan mujallar kungiyar masu nazarin karkashin kasa.
91. "The problem is that 91. “Matsalar ita ce;
92. most information about largest salt anything is centred on mines, 92. mafi yawan bayanan da ake samu game da samuwar gishiri ya ta’allaka ne da inda ake hakarsa,
93. and the largest mines may not be in the largest deposits." 93. mai yiwuwa ne kuma babbar mahakar gishiri ta duniya ba a wurin da yafi yawan gishiri a duniya aka haka ba
94. For now the best we can do is to say that the saltiest place on Earth is arguably a small pond in Antarctica, 94. Don haka iyakar abinda za mu iya cewa a yanzu shi ne; wurin da yafi kowanne gishiri a duniya wani kududdufi ne a yankin Antarctica,
95. or underneath a remote area of Russia. 95. ko kuma karkashin wani kwari da ke Rasha.
96. But it could also be somewhere else that nobody has yet thought to look. 96. Zai iya yiwuwa kuma wani wurin ne dabam da ba wanda ya sani saboda babu wanda ya yi tunanin ya yi nazarinsa.