1. http://www.bbc.com/earth/story/20140929-the-insect-that-loves-having-sex
|
1. http://www.bbc.com/hausa/mujalla-39788188
|
2. The insect that loves having sex
|
2. N/A
|
3. Obscure world records: which is the most promiscuous female insect of all?
|
3. Ka san baiwar tamatar kudan zuma?
|
4. When it comes to sex,
|
4. Idan ana maganar saduwa
|
5. we tend to see the male of the species as the most promiscuous.
|
5. ce ta namiji da mace tsakanin kowace halitta muna daukar namiji da cewa shi ne ya fi yawan sha'awa.
|
6. Yet, as the story of the record-breaking [en.wikt] honeybee shows us,
|
6. Amma kuma kamar yadda labarin bajintar kudan zuma ya nuna mana,
|
7. females can be just as likely to play the sex game.
|
7. ga alama mata ne za su ciri tuta a wannan fage.
|
8. We know that male animals seek to mate with multiple females to increase their chances of reproductive success.
|
8. Mun san cewa mazajen dabbobi suna son saduwa da mata da yawa domin samun haihuwa da yawa.
|
9. And we think that females are naturally pickier
|
9. Kuma muna daukar cewa mata sun fi tsantseni
|
10. because they invest more energy in
|
10. saboda sun fi mayar da hankali wajen
|
11. producing offspring
|
11. haihuwar 'ya'ya
|
12. and do not increase their chances of reproducing
|
12. kuma ba sa kara damarsu
|
13. by having more than one partner.
|
13. ta hayayyafa domin yawanci suna zama ne da namiji daya.
|
14. These are among the most deeply entrenched concepts of evolutionary biology.
|
14. Wadannan na daga cikin muhimman batutuwan da nazarin samuwar halitta ya mayar da hankali a kai.
|
15. They're also way off the mark.
|
15. Kuma su ma sun kauce hanya ko kuma a ce ba su fahimci lamarin ba.
|
16. The myth of the ardent,
|
16. Labarin nazariyyar halin halittu
|
17. promiscuous male and the coy,
|
17. da ke nuna cewa namiji hariji ne
|
18. choosy female
|
18. mace kuwa tana da son zabi ko tsantseni
|
19. is based on what some have called the Darwin-Bateman paradigm.
|
19. ya dogara ne kan abin wasu suka kira nazariyyar Darwin da Bateman.
|
20. In The Descent of Man and Selection in Relation to Sex, Charles Darwin,
|
20. A wani littafi da ya rubuta (The Descent of Man and Selection in Relation to Sex), Charles Darwin
|
21. one of the founding fathers of the theory of evolution,
|
21. daya daga cikin wadanda suka kirkiro nazariyyar asalin halitta,
|
22. described how males had
|
22. ya bayyana yadda maza suke da
|
23. “strong passions” and “eagerly pursue” females.
|
23. “sha'awa sosai” kuma suke bin mata sosai.
|
24. “The female, on the other hand, with the rarest exceptions,” he wrote,
|
24. Su kuma matan in banda kadan daga cikinsu ya ce,
|
25. “is coy, and may often be seen endeavouring… to escape the male”.
|
25. su na da yanga da jan hankali kuma yawanci sai a dauka suna son gudun namiji ne.
|
26. In 1948 English geneticist Angus John Bateman published
|
26. A 1948 masanin kimiyyar kwayoyin halitta na Ingila Angus John Bateman ya wallafa
|
27. a now famous experiment
|
27. abin da a yanzu aka fi sani da gwajin
|
28. in which equal numbers of male and female fruit flies were placed in bottles.
|
28. da aka samu yawan mata da maza daidai na wasu kwari (fruit flies) wadanda aka sa su a kwalabe.
|
29. He chose flies with mutations such as curly wings,
|
29. Masanin ya zabi kwari ko kudajen da suke da wasu kamanni kamar fuka-fukai da suka dan nade
|
30. small eyes
|
30. da kananan idanuwa
|
31. and thick bristles,
|
31. da kuma gashi mai kauri
|
32. to give him a way to determine the parentage of the resulting offspring.
|
32. domin ba shi damar zaben irin 'ya'yan da za su haifa.
|
33. Bateman concluded
|
33. Daga nan sai Bateman ya ayyana cewa
|
34. there was greater variability in both reproductive and mating success among males than females, and that
|
34. akwai bambanci mai yawa tsakanin maza da mata a fannin haihuwa da saduwa.
|
35. while mating with multiple partners increased the chances of a male passing on his genes, this was not the case for females.
|
35. Yayin da saduwa da yawan mata ke kara damar yuwuwar yada kwayoyin halitta ko kamannin namijin ba haka lamarin yake ba a bangaren mata.
|
36. These ideas have strongly influenced evolutionary biologists for decades.
|
36. Wannan nazarin ya yi tasiri sosai a kan masana kimiyyar samuwar halittu har tsawon shekaru gommai.
|
37. Of course some pointed to examples of species
|
37. Ba shakka wasu daga cikinsu sun nuna misalan yadda wasu jinsun halittun
|
38. in which observations showed the Darwin-Bateman sex roles were reversed,
|
38. inda nazari ya nuna an samu akasin abin da Darwin da Bateman suna nuna na rawar da maza da mata ke takawa a bangaren jima'i.
|
39. but perhaps surprisingly it was not until two papers published in 2007 and 2012 that researchers showed Bateman’s conclusions were based on flawed experimental and statistical methods.
|
39. Amma kuma ba a kai ga gane cewa nazariyyar Bateman ta dogara ne ga gwaji da kuma alkaluman da ke da matsala ko aka yi kura-kurai ba, har sai bayan da aka wallafa wasu kasidu biyu a shekara ta 2007 da 2012.
|
40. Patricia Adair Gowaty, of the University of California, Los Angeles,
|
40. Patricia Adair Gowaty ta jami'ar California a Los Angeles
|
41. repeated his original experiment.
|
41. ta maimaita ainahin irin nazarin da ya yi.
|
42. She pointed out his methods could only identify parentage
|
42. Ta nuna cewa tsarinsa kawai zai iya nuna iyaye ne
|
43. if offspring had the mutations of both its father and mother,
|
43. idan 'ya'ya suna da kamanni na uwa da uba,
|
44. and his data would only be accurate
|
44. kuma bayanansa ko alkaluma za su kasance daidai ne kawai
|
45. if such offspring were just as viable as those with one or no mutations – which they weren’t.
|
45. idan wadannan 'ya'ya suka kasance suna da inganci kamar wadanda suke da kamanni daya ko kuma babu wannan klamanni, wanda kuma ba haka suke ba.
|
46. All of which meant Bateman’s results and the conclusions based on them were wrong.
|
46. Kuma dukkanin wannan na nuna cewa alkaluma da sakamakon nazarin Bateman ba daidai suke ba.
|
47. Which brings us neatly to honey bees.
|
47. Wannan cikin sauki shi ya kawo mu kan kudan zuma.
|
48. Early in life, queens make mating flights during which they mate with multiple drones that die once they have deposited their sperm.
|
48. A farkon rayuwarsu, sarauniyar kudan zuma tana saduwa da mazaje daban-daban wadanda suke mutuwa da zarar sun zuba maniyyinsu.
|
49. They store and use the sperm throughout her life.
|
49. Sarauniyar tana adana wannan maniyyi ta yi ta amfani da shi har tsawon rayuwarta.
|
50. Worker bees in the hives of queens that have had more partners have been shown to produce more honey comb.
|
50. Su kuma matan kudan zuman masu aiki (worker bee) wadanda suke saduwa da namiji fiye da daya sun fi samar da zuma.
|
51. This promiscuity is believed to help improve resistance to disease by boosting genetic diversity.
|
51. Ana ganin wannan harijanci (saduwa da maza da yawa) yana taimaka musu wajen samun kariya daga cututtuka ta hanyar bunkasa kwayoyin halittarsu.
|
52. So it is unsurprising that when Hector Cabrera-Mireles,
|
52. Saboda haka ba abin mamaki ba ne a lokacin da Hector Cabrera-Mireles,
|
53. then at the University of Florida,
|
53. wanda a lokacin yake jami'ar Florida
|
54. reviewed previous studies
|
54. ya sake bibbiyar nazarce-nazarcen da aka yi a baya
|
55. to identify the most polyandrous insect - the species in which the female copulates with the most males - he focused on honey bees.
|
55. domin gano tamatar kwaron da ta fi saduwa da maza ya mayar da hankali kan kudan zuma.
|
56. The European honey bee
|
56. Tamatar kudan zuma na Turai
|
57. was found to mate up to 20 times and the Asiatic honey bee up to 30 times.
|
57. an gano tana saduwa da namiji sau 20 yayin da ta yankin Asia ta ke yin jima'i sau 30.
|
58. However Cabrera-Mireles determined that the Apis dorsata,
|
58. Sai dai Dakta Cabrera-Mireles ya ayyana cewa tamatar
|
59. the giant honey bee of South and Southeast Asia,
|
59. katon kudan zuma na Kudu da Kudu maso gabashin Asiya
|
60. was the most polyandrous of all, with one DNA fingerprinting studying determining that females had up to 53 mates.
|
60. ita tafi saduwa da maza da yawa, inda a bincikensa ya gano cewa mata suna saduwa da maza har 53.
|
61. The female cobalt milkweed beetle has been recorded mating up to 60 times,
|
61. Sai dai kuma a wani nazarin mai binciken ya gano cewa tamatar wani nau'in buzuzu da ake kira 'cobalt milkweed' da Ingilishi tana jima'i har sau 60,
|
62. but was disqualified by Cabrera-Mireles because this figure included multiple matings with the same male.
|
62. sai dai masanin bai zabe ta ba a matsayin wadda ta fi yawan jima'i ba domin takan sadu da namiji daya fiye da sau daya.
|