Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/061 facebook rise

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

#: Facebook is a growing and unstoppable digital graveyard [1] <> Yadda Facebook ya zama makekiyar makabarta [2]

#: At some point, there will be more dead Facebook users than living ones [3] <> A nan gaba, matattu za su fi rayayyu yawa a Facebook, [4]

#: and for those left behind, it is transforming how we experience the death of those around us. [5] <> abinda ke zama wani babban kalubale game da yadda mu ke tunawa da mutuwar wadanda mu ke tare da su. [6]

#: The day after my Aunts passing, [7] <> Washe garin rasuwar gwaggo na, [8]

#: I discovered shed written me a lovely note [9] <> na gano cewa ta rubuta sako, [10]

#: on the front page of the Shakespeare collection shed given me. [11] <> a kundin littafan Shakespeare da ta bani kyauta. [12]

#: I know how important the written word is to you,” it read, “this then is my gift to you.” With all of my love, as always, Aunt Jackie [13] <> “Na san muhimmancin littattafai a wurinka, don haka na baka wannan kyauta. Mai kaunarka koda yaushe, Jackie.” [14]

#: Deeply moved, I opened my laptop and found my way over to her Facebook page. [15] <> Wannan ya sa shaukinta ya kama ni har na shiga intanet na budo shafinta na Facebook. [16]

#: I thought it would be comforting to see pictures of her, and to read some of her witty posts, and to imagine her speaking them in her brassy, brazen, Baltimore screech. [17] <> Niyyata ita ce in karanta abubuwan da take wallafawa a shafin ina kallon hotonta ina riyawa a raina kamar ita ce ke magana. [18]

#: At the top of her Facebook feed was a video posted by my cousin [19] <> Abinda na fara gani shi ne wani sakon bidiyo da danta ya aika [20]

#: showing two elephants playing in water. [21] <> dauke da wasu giwaye biyu su na wasa a cikin ruwa, [22]

#: (My aunt loved elephants. [23] <> kasancewar gwaggon tawa akwai ta da son giwaye. [24]

#: Below that were some tributes from former students, [25] <> Kasan wannan kuma sai sakonnin taaziyya da dalibanta su ka rubuta. [26]

#: as well as the obituary posted by her sister-in-law. [27] <> Kasa da wannan kuma sai sanarwar rasuwarta da surukarta ta wallafa. [28]

#: I scrolled back up. [29] <> Daga nan sai na koma sama. [30]

#: According to Facebook, Aunt Jackie studied English Education at Frostburg State University, [31] <> A cewar Facebook, Gwaggo Jackie ta sami horon koyar da Ingilishi a jamiar Frostburg, [32]

#: was a former English Department Head for Baltimore City schools, [33] <> tsohuwar shugabar sashen koyar da Ingilishi ce a hukumar makarantun Baltimore, Maryland [34]

#: and lives in Baltimore, Maryland. [35] <> kuma ta na rayuwa a garin Baltimore. [36]

#: Lives? I thought. [37] <> Rayuwa kuma? Na tambayi kai na. [38]

#: She doesnt live anywhere. Shes gone. [39] <> Ai ta rasu. [40]

#: But if you happened to come across her profile on Facebook and didnt scroll down to the obituary, then you wouldnt know that. [41] <> Amma idan ka duba shafinta na Facebook ba za ka gane hakan ba, har sai ka bibiya inda aka rubuta sanarwar rasuwarta. [42]

#: She would still be, in some sense, alive. She would behere. On Facebook. [43] <> Wato ke nan ta wata fuskar a iya cewa ta na raye amma rayuwar Facebook. [44]

#: I thought back to the night my family and I stood around Aunt Jackie, [45] <> Sai na tuno ranar da ni dayan uwana mu ka kewaye gadon asibitin da Gwaggo Jackie ke kwance [46]

#: hooked to wires and machines, and watched her pass. [47] <> tare da wayoyi da aka jona mata da naurori lokacin ta na kan gargarar ajali har aka zare ranta. [48]

#: Observing that phenomenon is a strange thing. [49] <> Shaidar fitar ran mutum wani abu ne mai tayar da hankali. [50]

#: There she is, the person you loveyoure talking to her, [51] <> Ga ta nan kwance, ka na yi mata magana, [52]

#: squeezing her hand, [53] <> ka na rike hannayenta, [54]

#: thanking her for being there for you, [55] <> ka na yi mata godiya kan hidimar da ka yi mata a rayuwa, [56]

#: watching the green zigzag move slower and slowerand then shes not there anymore. [57] <> ka na kallon motsin bugun zuciyarta a naura har ta tsaya cik; rai ya yi halinsa. [58]

#: Another machine, meanwhile, was keeping her alive [59] <> Ashe kuma a wata naurar, ta na nan da ranta. [60]

#: While its obvious [61] <> A bayyane ta ke, [62]

#: that people dont outlive their bodies on digital technology, [63] <> rayukan mutane ba sa makale wa cikin naurorin fasahar zamani bayan mutuwar gangar jikinsu [64]

#: they do endure in one sense. Peoples experience of you as a seemingly living person can and does continue online. [65] <> amma dai mutane kan ci gaba da haduwa da su a shafukan sada zumunta irin yadda su kan hadu da su kafin rasuwarsu. [66]

#: How is our continuing presence in digital space changing the way we die? [67] <> Ko yaya wannan ci gaba da wanzuwa a intanet ke shafar yadda mu ke mutuwa? [68]

#: And what does it mean for those who would mourn us after we are gone? [69] <> Kuma wane tasiri hakan ke yi ga wadanda ke makokinmu bayan mun mutu? [70]

#: The numbers of the dead on Facebook are growing fast. [71] <> Adadin matattun da ke Facebook kullum dada karuwa ya ke. [72]

#: By 2012, just eight years after the platform was launched, 30 million users with Facebook accounts had died. [73] <> A 2012, shekaru takwas kacal, da bude Facebook, an samu masu shafuka a dandalin miliyan 30 wadanda su ka mutu. [74]

#: That number has only gone up since. [75] <> Wannan adadin na matukar karuwa, [76]

#: Some estimates claim more than 8,000 users die each day. [77] <> inda wani kiyasin ke cewa kimanin masu shafin Facebook 8,000 ne kan mutu a kullum. [78]

#: At some point in time, there will be more dead Facebook users than living ones. [79] <> A na kan haka, sai an kai inda matattu za su fi rayyayu yawa a dandalin, [80]

#: Facebook is a growing and unstoppable digital graveyard. [81] <> wato ke nan Facebook ya zama wata makekiyar makabarta a intanet [82]

#: Some estimates claim more than 8,000 Facebook users die each day [83] <> wacce kullum kara girma ta ke. [84]

#: Many Facebook profiles announce their owners have passed; [85] <> Akwai shafukan Facebook da dama da ke sanar da cewa masu su sun rasu. [86]

#: they arememorialised”. [87] <> A kan buga kalmardomin tunawa”, [88]

#: The profile is emblazoned with the wordremembering”, and they stop appearing in public spaces, like People You May Know or birthday reminders. [89] <> don haka sai a daina ganinsa a wurare na yau da kullum, irin su tunatarwar zagayowar ranar haihuwarsu. [90]

#: But not all Facebook users who have passed away are memorialised. [91] <> Sai dai ba kowanne matacce ne a Facebook a ke buga masa wannan tambarin ba. [92]

#: Kerry, one of my college dorm mates, killed himself a few years ago, [93] <> Kerry, wani dan dakinmu a jamia ya hallaka kansayan shekarun baya, [94]

#: and his wife and family and friends regularly post updates on his page, and when they do, Kerrys profile populates in my Facebook feed. [95] <> amma matarsa dayan uwansa da ma abokai na ci gaba da wallafa bayanai a shafinsa. Kuma duk san da su ka yi rubutun na kan gani a shafina. [96]

#: Neither Kerry nor my Aunt Jackie are memorialised, [97] <> Amma Kerry da Gwaggo Jackie baa buga musu tambarin mutuwa a shafukansu ba, [98]

#: which means, for all intents and purposes, their deaths havent been recognised by Facebook, or by the unwitting users who chance upon them. Their digital identities continue to exist. [99] <> don haka su na nan a raye a Facebook. [100]

#: Social media has taught us about the power of the momentconnecting right now with people around the globe over awards show, television programmes, football games, social justice issues, and whatnot. [101] <> Amfani da shafukan zumunta dai kan bamu damar kulla alaka nan take da mutane a fadin duniya a lokacin da ake wani biki, ko gasar wasanni ko shirye-shiryen talabijin da sauransu. [102]

#: But now it may be time to consider what comes after all that: our legacy. [103] <> Yanzu kuma lokaci ya yi da zamu duba abinda ke biyo bayan an gama komai da komai: wato bayan mutuwarmu. [104]

#: It used to be that only certain prominent people were granted legacies, [105] <> A baya can, wasu fitattun mutane ne kadai kan bar wani abin tunawa bayan mutuwarsu, [106]

#: either because they left written records for their forebears, or because later inquisitive minds undertook that task. [107] <> ko dai saboda sun ajiye rubutattun bayani ko kuma saboda wani dan ganin kwakwa ya yi aikin binciken tarihinsu. [108]

#: But digital technology changes that. [109] <> Amma fasahar kere-keren zamani ta sauya wannan tsarin. [110]

#: Now, each of us spends hours each week[111] <> A yanzu, kowannenmu na shafe saoi da dama a kowanne mako[112]

#: more than 12, according to a recent surveywriting our autobiographies. [113] <> fiye da saa 12 in ji wasu masananmuna rubuta tarihin rayuwarmu. [114]

#: As Ive told my mother, [115] <> Kamar yadda na shaidawa mahaifiyata, [116]

#: my grandchildren may be able to learn about her by studying her Facebook profile. [117] <> jikokina za su santa ciki da bai ta hanyar nazarin shafinta na Facebook. [118]

#: Assuming the social network doesnt fold, they wont just learn about the kinds of major life events that would make it into my moms authorised biography. [119] <> Saboda ba wai muhimmin abubuwan rayuwa da akan tattara a rubutattun littattafai kawai za su gani ba, [120]

#: Theyll learn, rather, the tiny, insignificant details of her day to day life: [121] <> ta hanyar Facebook za su ga bayanin abubuwa na yau da kullum na rayuwarta, masu muhimmanci da mara sa muhimmanci. [122]

#: memes that made her laugh, [123] <> Za su ga me ke sa ta dariya, [124]

#: viral photos she shared, [125] <> wadannan irin hotuna ke burgeta, [126]

#: which restaurants she and my father liked to eat at, [127] <> wane gidan abinci su ke zuwa da babana, [128]

#: the lame church jokes she was too fond of. [129] <> wadannan labaran ban dariya ne ke burgeta. [130]

#: And of course, theyll have plenty of pictures to go with it. [131] <> Kuma za su sami dimbin hotuna da za su kara haska musu rayuwarta. [132]

#: By studying this information, [133] <> Ta hanyar nazarin wadannan bayanai, [134]

#: my grandchildren will come to know about their great grandmother. [135] <> jikokina za su iya sanin wacece kakar kakarsu. [136]

#: We might think of our public social media record as some type of digital soul: [137] <> Muna iya kallon bayanan da muke bari a shafukan sada zumunta a matsayin ranmu na fasahar zamani: [138]

#: those perusing my Facebook know my religious beliefs, [139] <> wadanda duk ke bibiyata a Facebook sun san akidata ta addini, [140]

#: my political reservations, [141] <> raayina na siyasa, [142]

#: my love for my partner, [143] <> soyayyata da mijina, [144]

#: my literary tastes. [145] <> da kuma irin littattafan da nake so. [146]

#: Were I to die tomorrow, my digital soul would continue to exist. [147] <> Da zan mutu a yau raina zai ci gaba da wanzuwa a Facebook. [148]

#: In the past few years, [149] <> Cikin shekarun baya-bayan nan, [150]

#: several tech companies [151] <> kamfanonin fasahar zamani da dama [152]

#: have extended the idea of a digital soul. [153] <> sun kaddamar da tsare-tsaren da za su bada damar ci gaba da hulda da mutane bayan rayuwarsu. [154]

#: Eterni.me, launched in 2014, [155] <> Eterni.me, wanda aka kafa a 2014, [156]

#: promises to create a digital version ofyouthat will live on after your death. [157] <> ya zo da tsarin samar da makwafinka, wanda zai ci gaba da rayuwa bayan mutuwarka. [158]

#: Death is certain, admits the website[159] <> Mawallafin shafin ya ce mutuwa dole ce [160]

#: but what if you could live forever as a digital avatar, [161] <> amma za ka iya rayuwa har abada ta hanyar makwafinka na intanet, [162]

#: and people in the future could actually interact with your memories, stories and ideas, almost as if they were talking to you?” [163] <> “mutane kuma su ci gaba da hulda da kai ta hanyar tunaninka da labarurrukanka kusan tamkar yadda su ke tattaunawa da kai a lokacin rayuwarka ta duniya. [164]

#: If programs like Eterni.me succeed, [165] <> Idan kamfanoni irin su Eterni.me su ka yi nasara, [166]

#: not only will my grandchildren be able to study my mothers life, [167] <> jikokina, ba bayanin mahaifiyata dalla-dalla kurum zasu iya gani ba, [168]

#: if they want theyll be able to ask her avatartheir intelligent, digitalgreat grandmother” – questions [169] <> har ma su na iya tambayar makwafinta na intanet, [170]

#: and receive answers that my mother, before she passed away, would have probably given them. [171] <> kuma su sami amsoshin da in da sun risketa kan ta mutu abinda za ta ce nan. [172]

#: You could take this process even further, as several futurists predict. [173] <> Masana ma na hasashen cewa za a iya samar da fasahar dawwama a rayuwa wacce ma ta zarce makwafin mutum a intanet. [174]

#: Consider a robot that was commissioned by the entrepreneur Martine Rothblatt, called Bina 48. [175] <> Misali, wani dan kasuwa Martine Rothblatt ya kera wani mutum-mutumi mai amfani da fasahar zamani mai suna Bina 48. [176]

#: The robot is almost identical in appearance to Rothblatts wife, [177] <> An kera mutum-mutumin ne bisa siffar matar Rothblatt, [178]

#: and contains a database of her speech and memories. [179] <> kuma ya na dauke da muryarta da kuma bayanai game da abubuwan da ta yi a rayuwa. [180]

#: Rothblatt, author of Virtually Human and the CEO of United Therapeutics, [181] <> Rothblatt, shugaban kamfanin United Therapeutics, [182]

#: is a transhumanist whose motto is "death is optional". [183] <> wanda takensa shi nemutuwa zabi ce”, [184]

#: Rothblatt foresees a near-future world in which [185] <> na ganin cewa nan gaba [186]

#: the dead can be reanimated [187] <> matattu za su iya wanzuwa [188]

#: thanks to mind clone software that can [189] <> ta hanyar shirya manhajar kwamfuta, [190]

#: allow avatars to think [191] <> wacce za ta bai wa mutum-mutumi damar yin tunani [192]

#: and respond and be in an eerily similar way to those theyre cloning. [193] <> tare da amsa tambayoyi tamkar mutanen da su ke kwaikwaya. [194]

#: So, if the end-point is that a loved one carries on living, [195] <> Idan har hakan ta tabbata, ya zamo masoyanmu na ci gaba da rayuwa bayan mutuwarsu, [196]

#: how does that change how we grieve? [197] <> wane tasiri hakan zai yi kan yadda mu ke makoki? [198]

#: One of the seminal texts on grief is Elisabeth Kubler-Rosss 1969 On Death and Dying, [199] <> Daya daga cikin manyan littattafan da su ka yi bayani game da jimamin mutuwa shi neDeath and Dyingwanda Elisabeth Kubler-Ross ta wallafa a 1969. [200]

#: which outlines five steps of the grieving process: [201] <> A cikinsa ta wassafa matakai biyar na makoki: [202]

#: denial, [203] <> rashin amincewa, [204]

#: anger, [205] <> fusata, [206]

#: bargaining, [207] <> daidaitawa, [208]

#: depression, [209] <> damuwa, [210]

#: acceptance. [211] <> sai kuma amincewa. [212]

#: Since its publication, [213] <> Tun bayan wallafa littafin, [214]

#: modern experts have questioned and criticised its central claims, [215] <> masanan zamani sun soki matsayarsa [216]

#: particularly the understanding that successful mourners let go of the departed and move on. [217] <> musamman ma da yake nuna cewa karshen jimamin mutuwa shi ne amincewa mamata sun tafi ke nan ba za su dawo ba, don haka mu ma mu rabu da jimaminsu mu ci gaba da rayuwarmu. [218]

#: Today, many counsellors help mourners realise that their loved ones continue to be with them, in some sense, after they die. [219] <> Masana a yanzu kuwa na nunawa masu jimami cewa wadanda su ka mutu na nan tare da su cikin zukatansu. [220]

#: The relationship changes, but it is still there. [221] <> Dangantakarsu ce kan sauya amma dai ta na nan. [222]

#: Still, part of the grieving process does necessitate moving on, and, well, forgetting in some sense. [223] <> Duk da haka, wani bangaren na jimamin mutuwa ya hada da mu ci gaba da harkokin rayuwarmu tare da mancewa da mamatan. [224]

#: Not forgetting that our loved ones ever existed, but forgetting that they are in in this place with us. [225] <> Ba wai mu manta cewa sun taba rayuwa ba, amma dai mu manta cewa muna tare da su cikin wannan duniyar. [226]

#: Thats the catch of our brave new world: digital data does not allow us to forget. [227] <> A nan gizon ke sakar: a wannan zamanin, intanet ba za ta bar mu manta ba. [228]

#: In the past, remembering the dead had a physical element to it. [229] <> A baya dai tuna mamata wani abu ne na zahiri. [230]

#: You had to go somewhere to honour them: a graveyard, a church, a memorial. Or you had to take out a box of photographs or an album or an obituary clipping. [231] <> Kafin ka ga kushewarsu sai ka tashi ka je makabarta ko kuma ka dauko littafan adana hotuna. [232]

#: You had to take some time from the present to think about your past, your history, your time with that person. [233] <> Wato dai sai ka dauki wani lokaci da za ka tuna baya. [234]

#: In Facebook, all places are present, all times are now. [235] <> A Facebook komai a yanzu yake faruwa. [236]

#: My Aunt Jackie exists in this medium just as I do. [237] <> Don haka Gwaggo Jackie na rayuwa a shafin kamar yadda nake rayuwa, [238]

#: In a way, there is no moving on without her. [239] <> babu batun cewa ta mutu sai dai labari. [240]

#: Theres no moving on without any of the millions of dead Facebook users. [241] <> Haka kuma duk miliyoyin matattun nan na Facebook ba su zama sai labari ba. [242]

#: As of yet, theres no good solution to the problem of dead data, of digital ghosts. [243] <> A yanzu dai babu wata hanya da za ta magance matsalar wanzuwar matattu a matsayin fatalwoyin intanet. [244]

#: The only hope is that the internets memory will at some point begin to fade. [245] <> Fatana daya shi ne nan gaba ita ma intanet ta fara manta abubuwan baya. [246]

#: "The truth," writes Borges, "is that we all live by leaving behind." [247] <> N/A [248]

Contents