Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/076 Why we want food so much

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

  1. Why we want food so much it hurts [1] <> Me ya sa muke son abinci sosai? [2]

  1. Be it chocolate, cheese or chip shop curry, craving a favourite food is something weve all experienced. [3] <> Akwai abinci iri-iri da kusan kowane mutum zai ji a ransa ga wani da ya fi so a wani lokaci, kuma idan ba ya same shi ba, sai ya ji ba dadi ko da kuwa abincin nan ba wani na a-zo-a-gani ba ne. [4]

  1. Why do our bodies suffer such serious pangs? [5] <> To me ya sa jikinmu ke fama da irin wannan takura? [6]

  1. Veronique Greenwood investigates. [7] <> Veronique Greenwood ta bincika. [8]

  1. There's nothing like the salty tang of beef-flavoured Top Ramen broth and a mouthful of slightly overdone instant noodles. [9] <> Ba abin da ya fi dadi kamar ka samu taliya ruwa ruwa da zafinta ta sha romon naman shanu da kuma kayan hadi iri daban daban. [10]

  1. At least, not for me. [11] <> To amma dai ba da ni ba a wannan dabdala yanzu domin [12]

  1. I've gone on record about my obsession before, [13] <> ni kam na sha ta a da, [14]

  1. writing about how ramen noodles helped me get through adolescence. [15] <> inda har na rubuta yadda wannan abinci ya taimaka min a lokacin da nake budurwa. [16]

  1. But the truth is that I crave it still, [17] <> Amma a gaskiyar lamari har yanzu ina matukar san wanna abinci [18]

  1. especially when I'm tired or sick. [19] <> musamman ma idan na gaji ko ba ni da lafiya. [20]

  1. You probably have something similar in your personal food pantheon[21] <> Watakila kai ma kana da irin wannan sha'awa ta wani abinci a tarin irin abincin da kake ci, [22]

  1. the craving that tops all other cravings, [23] <> sha'awar da ta shafe duk wata sha'awa taka ta abinci, [24]

  1. the comfort food whose sensory portrait you can paint in your head over and over while you stand on the subway on the way home or creep slowly dinnerwards through the traffic. [25] <> abincin da yake kwantar maka da hankali ya sa ka nishadi, wanda saboda tsananin shiga ranka za ka iya tunanin yadda siffarsa take a kwakwalwarka a yayin da kake jiran jirgi a tashar karkashin kasa a kan hanyarka ta zuwa gida ko kuma kana tunkarar abincinka na dare a hankali a hankali tsakanin ababan hawa. [26]

  1. Not all cravings are so familiar[27] <> Ba duk abinci ba ne da ka zaku ka samu wanda ya shiga ranka yake sananne a wurinka. [28]

  1. have you ever craved something you'd completely forgotten about, like a discontinued flavour of doughnut or a salad dressing from a long-ago garden party? [29] <> Ko akwai lokacin da ka taba samun kanka a irin wannan hali da ma ka manta yadda abincin da kake so yake. [30]

  1. Pregnant women are said to crave extremely unlikely food combinations, from ice cream and pickles to strawberry and tuna. [31] <> An ce mata masu juna biyu sukan yi sha'awar abinci wanda yake kusan a ce na daban. [32]

  1. But all cravings worthy of the name seem to have that singular intensity. [33] <> Dukkan wani abinci dai da ya shiga ran mutum wanda ya amsa sunansa yana da wannan tsanani a ran mutum. [34]

  1. They feel like important messages from your body. [35] <> Za ka ji kamar wasu sakonni ne masu amfani daga jikinka. [36]

  1. But they're not. [37] <> Amma kuma ba haka suke ba. [38]

  1. Eva Kemps, a professor of psychology at Flinders University in Adelaide, Australia, [39] <> Farfesa Eva Kemps ta Jami'ar Flinders a Adelaide da ke Australia, [40]

  1. explains that [41] <> ta bayyana cewa, [42]

  1. despite a long folk tradition of trying to link cravings to nutrient deficiencies[43] <> duk da yadda aka dade ana ta kokarin danganta sha'awar wani abinci da mutum kan yi da rashin wasu sinadarai, [44]

  1. I need this chocolate, for biological reasons! ‒ that's not the case. [45] <> ina bukatar wannan alewar chakuleti ne ba don saboda wasu dalilai na jiki ba. [46]

  1. One common justification for chocolate cravings, [47] <> Wani fitaccen dalili da ya na tsananin sha'awar alewar chakuleti, [48]

  1. for instance, [49] <> misali, [50]

  1. is that the cravers are deficient in magnesium, [51] <> wadannan abubuwa da suke tasowa da mutum wannan tsananin sha'awa shi ne ba su da sinadarin magnesium [52]

  1. which chocolate can provide. [53] <> wanda chakuleti za ta iya bayarwa. [54]

  1. But many, many foods, [55] <> To amma kuma kayan abinci da yawa [56]

  1. including spinach, [57] <> da suka hada da alaiyahu [58]

  1. contain more magnesium than chocolate, [59] <> suna da sinadarin magnesium fiye da chakuleti [60]

  1. which is the most commonly craved food in Western societies. [61] <> wadda ita ce abar ci da ta fi shiga ran mutane a kasashen Yamma, na Turawa. [62]

  1. Funnily enough, people don't crave spinach,” she observes. [63] <> 'To sai dai kuma abin mamakin shi ne mutane ba sa tsananin bukatar alaiyahun. In ji Kemps. [64]

  1. Hormonal factor [65] <> Tasirin kwayoyin halitta [66]

  1. There are many rationalisations of this kind. [67] <> Akwai abubuwa dama masu kama da wannan. [68]

  1. But cravings are more strongly linked to emotions [69] <> Amma matukar sha'awar wani abinci ana ganin tana da alaka da yanayin mutum [70]

  1. and external cues that evoke memories[71] <> da kuma wasu dalilai na mu'amullar mutum da suke tasowa da mutum sha'awar ta hanyar tuna masa da wani abu na baya. [72]

  1. while being hungry can certainly be a factor in starting cravings, [73] <> Yayin da ake ganin yunwa za ta iya sa mutum ya ji irin wannan sha'awa, [74]

  1. they are more psychological than physiological. [75] <> ita yunwa ana danganta ta da abin da ya shafi tunanin mutum maimakon abin da ya shafi jikinsa. [76]

  1. Being sad, anxious, stressed, bored, or lonely is often the trigger for a craving, Kemps says. [77] <> Kasancewar mutum cikin yanayi na damuwa ko kadaici ko zakuwa da makamantansu wanna ka iya jawo masa wannan yanayi na matukar sha'awar abincin in ji Kemps. [78]

  1. Food as a comfort [79] <> Abinci a matsayin abin da ke sa mutum ya ji dadi [80]

  1. doesn't explain the precision of cravings, exactly, [81] <> ba ya bayyana dalilin da ke sa mutum ya tsinci kansa a wannan yanayi na matukar bukata, [82]

  1. except for the fact that we often crave foods we've had prior experiences with. [83] <> sai dai kawai saboda mukan ji sha'awar abincin da muka sani a baya ne. [84]

  1. We also tend to crave things that we've just seen a picture of [85] <> Haka kuma mukan yi matukar sha'awar abin da ba mu dade ba da ganin hotonsa [86]

  1. or that appear in our vicinity. (When muffins appear in your office mid-afternoon, it doesn't matter if you've just had lunch. You want that muffin.) [87] <> ko muka gani a muhallinmu. [88]

  1. It's not that biology is never involved. [89] <> Ba wai cewa babu alakar aikin jikin mutum ba ne a cikin wannan abu. [90]

  1. Statistically, women tend to report significantly more cravings in the days [91] <> Bisa kididdiga, an gano cewa mata sun fi samun kansu a wannan yanayi na sha'awar wani abinci a cikin kwanakinsu [92]

  1. just before their periods, [93] <> na kafin al'ada, [94]

  1. and the cravings of pregnant women [95] <> da kuma cewa wannan sha'awa ta mata masu juna biyu [96]

  1. as well suggest that there can be a hormonal component to these particular desires. [97] <> ita ma tana nuna cewa da alama akwai wasu kwayoyin halitta da suke jawo hakan. [98]

  1. But whether that's something that actually plays a nutritional role or just noise in the neurons, Kemps couldn't say. [99] <> Amma ko wannan abu ne da yake taso da wannan sha'awa ta abinci ko kuma kawai wata hayaniya ce a jijiyoyin mutum Kemps ba za ta iya tabbatarwa ba. [100]

  1. And obviously cravings are more universal than pregnancy or menstruation. [101] <> Kuma a zahirin gaskiya wannan sha'awar abinci abu ne da ya hada komai da kowa ba kawai sanadiyyar juna biyu ba ko al'ada ta mata ba. [102]

  1. Regardless of their origins, cravings can be extraordinarily intrusive. [103] <> Ko ma menene asalinta sha'awar abincin wata aba ce da ke matukar takura wa mutum. [104]

  1. Experiments have shown that they make it harder to perform cognitive tasks, [105] <> Bincike da dama da aka yi [106]

  1. suggesting that they are hogging some limited amount of mental bandwidth. [107] <> ya nuna cewa aba ce da ke da wuyar sha'ani wajen jarrabata kan wani bincike da ya shafi kwakwalwa. [108]

  1. James Wannerton, the taste-word synesthete interviewed for this column recently, experiences distracting cravings all the time, triggered by the sensations words generate. [109] <> James Wannerton masanin dan dano da aka yi wa tambayoyi a wanna shafi kwanannan, ya ce yana gamuwa da wannan matsala ta sha'awar wani abinci a lokuta da dama. [110]

  1. He craves mince pies so frequently that, despite not liking them, [111] <> Duk da cewa ba ya son abincin da ya kejin sha'awar ta sa, [112]

  1. he has to keep them in his freezer, so he can eat them to get the thought of them out of his mind. [113] <> ala dole yake tanadarsa ya ci domin kawar da wanna tunani ko sha'awa daga ransa idan ta taso. [114]

  1. Visual cues [115] <> N/A [116]

  1. To understand the process of craving and see how it might be interrupted, [117] <> Domin fahimtar yadda wannan lamari na matukar sha'awar wani abinci yake domin sanin yadda za a iya dakile shi, [118]

  1. Kemps and her colleague Marika Tiggemann have studied exactly what it feels like. [119] <> Kemps da abokiyar bincikenta Marika Tiggeman sun yi nazarin yadda lamarin yadda ake ji. [120]

  1. They asked 130 subjects to recall a craving they'd had [121] <> A nazarin da suka gudanar sun bukaci mutane 130 da su tuna wani da lokaci suka shiga wannan yanayi, [122]

  1. and write down a description, collecting what amounted to lyrical rhapsodies about the object of desire. [123] <> su rubuta daki-daki yadda ya kasance, ta yadda abin ya fara da yadda suka bullo wa lamarin. [124]

  1. They found that people don't think about sound [125] <> A binciken sun gano cewa mutane ba sa tunani a kan wani sauti [126]

  1. or touch all that much in cravings, [127] <> ko wani abu da za a taba, [128]

  1. with visual images playing a major role, [129] <> inda suka gano cewa abin da ke da tasiri a ciki sosai shi ne ganin yanayin siffar abincin [130]

  1. along with imagined taste and smell, of course. [131] <> da kuma tunanin dandanonsa da kanshinsa. [132]

  1. They wondered whether having people imagine non-food images, [133] <> Sun yi tunanin ko sanya mutane su yi tunanin siffar wani abu da ba abinci ba [134]

  1. like rainbows or rose gardens, could nip cravings in the bud. [135] <> kamar bakan-gizo ko lambun furanni hakan zai iya sa su yi maganin sha'awar tun daga farkonta. [136]

  1. As it turns out, [137] <> Kamar yadda sakamakon ya kasance, [138]

  1. these imaginings can lessen the intensity of cravings. [139] <> wannan na samar da hotunan ko siffa ya rage tsananin sha'awar. [140]

  1. Another team has found that they could smother subjects' cravings by having them play Tetris. [141] <> Wani rukunin masu binciken kuma ya gano cewa zai iya saukakawa mutane wannan sha'awa ta hanyar sa mutum ya yi wani wasan bidiyo na kwamfuta (tetris) ta yadda zai dauke masa hankali, [142]

  1. But the alternative visual process doesn't even need to be engaging. Staring at TV static works too, Kemps says. [143] <> kamar yadda Kemps ta ce kallon wasu hotuna na talabijin ma zai iya yin hakan. [144]

  1. She and her colleagues [145] <> Kemps da abokan aikinta [146]

  1. are now planning to see whether they can distract people before cravings develop into full-blown mental images, when they are still vaguer desires. [147] <> a yanzu suna shirya yadda za su jarraba wani nazari da zai iya dauke hankalin mutum daga wannan saha'awa tun kafin ta yi tsanani. [148]

  1. If cravings get out of control[149] <> Idan wannan sha'awa ta fi karfin mutum, [150]

  1. if they are a constant feature of one's day[151] <> ta zama kullum tana taso wa mutum, [152]

  1. that can of course play havoc with health, [153] <> ta haka za ta iya shafar lafiyarsa, [154]

  1. since eating the desired items can mean a pile-up of unnecessary calories. [155] <> saboda cin abincin da sha'awar ke so na nufin mutum zai tara maiko a wanda hakan wata illa ce. [156]

  1. (It might be worth playing a little Tetris at your desk while those muffins are outside.) [157] <> n/a [158]

  1. But if cravings are more intermittent, [159] <> Sai dai idan wannan sha'awa ta kasance tana tasowa mutum ko da yaushe [160]

  1. Kemps has some surprising advice. [161] <> Kemps tana da shawara ga wannan mutum. [162]

  1. It's actually better to let yourself have it,” she says. [163] <> Shawar ita ce, abin da ya fi dacewa kawai shi ne ka biya bukatarka kawai domin hakan ya fi [164]

  1. The stronger the craving's going to become, then you're going to be fixated on it.” [165] <> 'Idan sha'awar ta cigaba da kara karfi a jikinka, za ka zamar mata jiki kai ma. [166]