Line 498: | Line 498: | ||
# Duk wanda ya sayar da ayoyin Allah da 'yan kudi kadan, to lalle ya yi koyi ne da Yahudawa. | # Duk wanda ya sayar da ayoyin Allah da 'yan kudi kadan, to lalle ya yi koyi ne da Yahudawa. | ||
# Wajabcin bayanin gaskiya ga mutane da haramcin boye ta. Idan kuma wani ya boye gaskiya saboda wani abin duniya da zai samu, to wannan laifinsa ya fi tsanani. | # Wajabcin bayanin gaskiya ga mutane da haramcin boye ta. Idan kuma wani ya boye gaskiya saboda wani abin duniya da zai samu, to wannan laifinsa ya fi tsanani. | ||
# Wajibi mai | # Wajibi mai karantawa ko da'awa ya riqa qoqarin yaye wa mutane shubuhohi da yi musu bayanin duk abin da ba su fahimta ba. It is obligatory for the reciter or preacher to try to clear people's doubts and explain to them everything they do not understand. Kuma duk wanda yake a wurin da babu wanda zai koyar da mutane sai shi, to dole ne ya tashi ya koyar da su abin da suke buqata na addini. And whoever is in a place where there is no one to teach people except him, then he must rise up and teach them what they need in religion. | ||
# Haramun ne | |||
pg57 | |||
[[Category:Quran]] | [[Category:Quran]] | ||
[[Category:Quran/2]] | [[Category:Quran/2]] | ||
[[Category:Rijiyar Lemo]] | [[Category:Rijiyar Lemo]] |
Revision as of 22:43, 25 February 2025
Baqara 1-5
- Alif Lam Mim. --Quran/2/1
- Wannan littafi ne da babu wani kokwanto a cikinsa; shiriya ne ga masu taqawa. --Quran/2/2
- This is the Book about which there is no doubt in it! It's a guide/guidance for those mindful of Allah. (See also Quran/1/6, Quran/19/76, Quran/guidance)
- dhālika l-kitābu lā rayba fīhi hudan lil'muttaqīn
- Wadanda suke yin imani da gaibi kuma suke tsayar da salla kuma suke ciyarwa daga abin da Muka azurta su da shi. --Quran/2/3
- Who believe in the unseen, establish prayer, and donate / spend out of what We have provided for them
- alladhīna yu'minūna bil-ghaybi wayuqīmūna l-ṣalata wamimmā razaqnāhum yunfiqūn
- Wadanda suke yin imani da abin da aka saukar maka da abin da aka saukar a gabaninka, kuma suke sakankancewa da ranar lahira. --Quran/2/4
- And who believe in what has been revealed to you, [O Muhammad], and what was revealed before you, and of the Hereafter they are certain [in faith]
- and who believe in what has been revealed to you ˹O Prophet˺ and what was revealed before you, and have sure faith in the Hereafter.
- wa-alladhīna yu'minūna bimā unzila ilayka wamā unzila min qablika wabil-ākhirati hum yūqinūn (yaƙini)
- Wadannan suna kan (babbar) shiriya daga Ubangijinsu, kuma wadannan su ne masu samun babban rabo. --Quran/2/5
- Those are upon [right] guidance from their Lord, and it is those who are the successful
- It is they who are ˹truly˺ guided by their Lord, and it is they who will be successful.
- ulāika ʿalā hudan min rabbihim wa-ulāika humu l-muf'liḥūn
Tafsiri:
Allah swt ya bud'e wannan Sura da harufin Alif da Lam da Mim. Ban da ita wannan Sura da akwai surorin Alqur'ani da dama da Allah ya bud'e su da irin wadannan haruffa. Da dama daga cikin malamai suna cewa, Allah ne kad'ai ya san abin da yake nufi da su (only Allah knows the meaning of these disjointed letters). Wasu kuma sun yi qoqarin bayyana ma'anoninsu. Amma magana mafi inganci ita ce, Allah yana nuna mu'ujizar AlQur'ani ne ta hanyar ambaton wadannan haruffa. Domin suna tabbatar wa larabawa cewa babu wanda zai iya kawo wani abu irin Alqur'ani, duk kuwa da cewa haruffansa su ne haruffan da suke magana da rubutu da su.
Allah ya siffanta wannan Alqur'ani da cewa, babu wani kokwanto a cikinsa,
- Allah describes this Quran as having no doubt in it,
wato duk abin da ya qunsa tabbatacce ne kuma gaskiya ne,
- that is, everything it contains is certain and true,
don haka ne ya zama shiriya ga masu taqwa,
yana nuna musu gaskiya da bayyana musu hukunce-hukunce wad'anda suka shafi aqidunsu da ibadunsu da kuma mu'amalolinsu.
- showing them the truth and explaining to them the rulings that affect their beliefs, their worship, and their dealings.
An kira Alqur'ani da sunan Littafi duk kuwa da kasancewarsa ba a tattara shi wuri guda ba a lokacin;
- The Quran was called the Book, even though it was not collected in one place at the time;
an yi haka ne domin a yi ishara zuwa ga cewa, nan gaba za a tattara shi wuri guda ya zama littafi wanda Musulmi a kowane lokaci za su riqa karantawa.
- This was done to indicate that in the future it would be collected in one place and it will become a book that Muslims would read at all times.
Sannan Allah swt yana fayyace siffofin masu taqwa wadanda Alqur'ani yake shiryar da su.
- Then Allah (swt) describes the characteristics of the pious people whom the Quran guides.
Sun siffantu da siffofi guda biyar kamar haka: <> They are described with five characteristics as follows:
- Suna yin imani da gaibu. Gaibu shi ne duk abin da manzanni suka zo da shi, suka ba da labarinsa, kuma ido bai gan shi ba. Wannan ya had'a da imani da ranar lahira da abin da ta ƙunsa na hisabi da mala'iku da labarin manzanni da littafan da Allah ya saukar gabanin zuwan Manzon Allah swt. Imani da gaibu shi ne yake bambance wa tsakanin mutum mumini da kafiri, saboda yana imani da duk wani abu da Allah ya ba da labarinsa ko Manzonsa ya fad'a ko da kuwa bai gano shi da hankalinsa ba.
- They believe in the unseen. The unseen is everything that the messengers brought, reported, and the eye has not seen. This includes belief in the Day of Judgment and what it entails, the angels, the stories of the prophets, and the books that Allah revealed before the coming of the Messenger of Allah (swt). Belief in the unseen is what distinguishes a believer from a disbeliever, because he believes in everything that Allah has reported or His Messenger has said, even if he does not understand it with his own mind.
- Suna tsayar da salla, wato suna yin ta kamar yadda shari'a ta koyar da su tare da kula da lokutanta da rukunanta da wajibanta da sharuɗɗanta.
- Suna ciyar da abin da Allah ya azurta su da shi. Sukan fitar da zakkar dukiyoyinsu, hakanan suna sadaka ta nafila da abin da Allah ya hore musu.
- Su ne waɗanda suke yin imani da Alƙur'anin da Allah ya saukar wa Annabi Muhammadu (SAW) gaba ɗaya ba tare da ware ɓangare ko sun riƙa tawilin karkatar da ma'anonin wani ɓangare na Alƙur'ani ba, kamar yadda 'yan bidi'a suke yi ga wasu ayoyin waɗanda ba sa goyon bayan bidi'o'insu da aƙidunsu. Hakanan suna yin imani da dukkan littattafan da Allah ya saukar wa manzanni da annabawan da suka gabata, har da su kansu manzannin da annabawan.
- Su ne waɗanda suka tabbatar da zuwan ranar tashin alƙiyama da abubuwan da za ta zo da su na tayar da matattu da yi musu hisabi da suka wa mutanen ƙwarai da Aljanna; masu miyagun laifuffuka kuwa a saka musu da wutar Jahannama. An ware batun imani da ranar lahira duk kuwa da cewa ya shiga cikin batun imani da gaibu, saboda a zaburar da mutane ga ayyukan alheri a kuma tsoratar da su game da munanan ayyuka.
Sannan Allah swt ya faɗi sakamakon masu waɗannan siffofi da cewa, suna kan wata shiriya mai girma daga Allah mai yi musu tarbiya ta ƙwarai. Domin babu wata shiriya da ta kai siffantuwa da waɗannan siffofi. Don haka su ne waɗannan suke da babban rabo daga Allah, wato samun yardar Allah da gidan Aljanna ranar gobe alƙiyama.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Girman mu'ujizar Alƙur'ani.
- The greatness of the miraculous Quran.
- Allah swt ya yi ishara zuwa ga cewa, za a tattara Alƙur'ani wuri guda don ya zama littafin da Musulmi za su riƙa ɗauka suna karantawa a kowane zamani.
- Allah (swt) has indicated that the Quran will be collected in one place so that it will be a book that Muslims will carry and read at any point in time.
- Alƙur'ani shiriya ne ga mutane masu taqwa. Watau masu kiyaye dokokin Allah. Gwargwadon taƙawar bawa gwargwadon yadda zai dace da shiriyar Alqur'ani. Wanda kuma ya rungume shi yana aiki da shi to babu shakka shiriyarsa za ta riƙa hauhawa tana ƙaruwa.
- The Quran is a guidance for the pious. That is, those who observe the laws of Allah. The measure of a servant's piety is as much as it is in accordance with the guidance of the Quran. And whoever embraces it and acts upon it, then undoubtedly his guidance will continue to increase and increase. (See also Quran/19/76)
- Duk abin da Alqur'ani ya qunsa gaskiya ne babu kokwanto ko kad'an a cikinsa.
- Everything the Quran contains is true, without the slightest doubt. (See also Quran/2/2, Quran/18/1, Quran/difference_from_raib_and_iwaj)
- Falalar yin imani da gaibu, domin shi ne abin da yake buqatar qarfin imani, sab'anin abin da kowa yake iya gani ko yake iya ji, wannan abu ne da babu mai iya musanta samuwarsa.
- Girman sha'anin tsai da salla, domin ita ce rukuni na biyu daga cikin rukunan Musulunci.
- The importance of establishing prayer, because it is the second of the pillars of Islam.
- Falalar ciyar da dukiya don Allah. <> The virtue of giving zakat and donating sadaqa for Allah's sake.
- Siffar masu taqawa ta ƙunshi bauta wa mahalicci ba kyautata wa mahluki.
- Imani da duk littattafan da Allah swt ya saukar wa manzanninsa, domin sanin cewa Allah swt bai bar bayinsa hakanan sakaka ba tare da bayyana musu hanyar shiriya ba.
- Shiriya da rabauta ba za su taɓa samuwa ga bawa ba sai ya rungumi wannan hanyar, ya siffantu da waɗannan siffofi.
Baqara 6-7
- Lalle waɗanda suka kafirta, duk ɗaya ne a gare su, ka yi musu gargaɗi ko ba ka yi musu ba, ba za su yi imani ba. --Quran/2/6
- Allah Ya toshe zukatansu da jinsu, kuma akwai wani lulluɓi a kan idanunsu, kuma suna da azaba mai girma. --Quran/2/7
Tafsiri:
A nan Allah yana ba da labarin kafirai ne da irin taurin kansu wajen kafirce wa abin da Annabi SAW ya zo da shi na gaskiya.
- Here, Allah is telling the story of the disbelievers and their stubbornness in rejecting what the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) brought as truth.
Allah ya faɗa wa Annabi (SAW) cewa, waɗannan kafirai sun kai matuƙa ga kafircinsu; yana da wuya wa'azinsa ya sa su saurare shi, har su yi imani, don haka kada kafircinsu ya dame shi.
- Allah told the Prophet (PBUH) that these disbelievers had reached the extreme of their disbelief; it was difficult for his preaching to make them listen to him and believe, so he should not be troubled by their disbelief.
Domin Allah ya riga ya toshe musu zukatansu saboda zunubbansu, don haka imani ba zai sami hanyar shiga cikinsu ba.
- Because God has already sealed their hearts because of their sins, faith will not find its way into them.
Kuma ya doɗe musu kunnuwansu saboda kafircinsu, don haka ba za su taɓa jin kiransa ba balle su amsa masa.
- And He has deafened their ears because of their disbelief, so they will never hear his call, let alone respond to it.
Sannan akwai yanar da ta rufe musu idanuwansu ta yadda ba za su taɓa ganin gaskiya ba balle su yarda da ita.
- And then there is a web/barrier that has blinded their eyes so that they will never see the truth, let alone believe it.
Saboda haka suka cancanci azaba mai girman gaske. <> Thus why they deserve a great punishment.
Wannan yana nuna cewa, kafirci idan ya yi yawa a tare da bawa yakan toshe masa dukkan ƙofofin samun shiriya,
- This shows that, when disbelief becomes too much in a person, it blocks all the doors to guidance.
duk kuwa yadda aka yi fama da shi ba zai taɓa karɓar gaskiya ba, don ba ya jin ta, ba ya ganin ta kuma ba ya fahimtar ta saboda tsatsar zunubi da kafirci da suka lulluɓe shi.
no matter how people struggle with him, he will never accept the truth, because he does not hear it, see it, or understand it due to the sheer sins and unbelief that have enveloped him.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Lallashin Annabi SAW da nuna masa kada damuwa ta hallaka shi saboda ganin mutanensa sun ƙi yin imani da gaskiyar da yake kiran su zuwa gare ta.
- Idan mai kira zuwa ga Allah SWT ya bayyana wa mutane gaskiya suka bijre masa, to wannan ba zai cutar da shi komai ba, domin shi ya sauke nayin da yake kansa.
- Annabi ko waninsa babu wanda ya san abin da Allah ya riga ya rubuta wa wadanda ake kira na shiryuwarsu ko ɓatansu, Allah ne kaɗai ya san haka.
- Tsananin haɗarin girman kai da bijire wa gaskiya da dogewa a kan kafirci, domin yin haka yakan toshe zukata har ya zamanto duk wani alheri ba ya ratsa su.
Baqara 8-10
- A cikin mutane kuma akwai wadanda suke cewa: "Mun yi imani da Allah kuma mun yi imani da ranar lahira," alhalin su ba muminai ne ba. --Quran/2/8
- Suna ganin suna yaudarar Allah ne da wadanda suka yi imani, amma kuwa ba kowa suke yaudara ba sai kawunansu, kuma su ba sa jin hakan. --Quran/2/9
- Akwai wata cuta (ta munafunci) a cikin zukatansu, sai Allah Ya ƙara musu wata cutar, kuma suna da wata azaba mai raɗaɗi saboda ƙaryar da suke yi. --Quran/2/10
Tafsiri:
Daga nan har zuwa aya ta 20 Allah SWT yana mana bayanin munafuƙai ne tare da fallasa su da bankaɗo munanan siffofinsu don kowa ya gane su a kowane lokaci a kuma kowane yanayi.
A lokacin da Annabi SAW yana zaune a Makka mutane kashi 2 ne: muminai sai kafirai. To amma bayan Musulmai sun yi hijira zuwa Madina, sai aka samu kashi na uku, su ne munafuƙai. Munafiki shi ne wanda yake bayyana Musulunci a bakinsa, amma yana ɓoye kafirci a zuciyarsa. Allah ya bayyana wasu siffofinsu a nan.
Yana daga cikin siffofinsu suka riƙa bayyana imani da baki amma suna ɓoye kafirci a zukatansu, shi ya sa Allah ya ce: "Waɗannan ba muminai ne ba." Kuma saboda wautarsu suna yin haka ne wai don a zatonsu suna yaudarar Allah ne tare da muminai, watau a tsammaninsu Allah bai san abin da suke ɓoyewa ba. Wannan ta sa idan yaƙi ya ɓarke tsakanin muminai da kafirai to su ba za a taɓa su ba, kuma ba za a taɓa dukiyarsu ba, sannan in an ci nasara a kan cewa, kawunansu kadai suke yaudara ba, domin babu mai cutuwa da abin da suke yi su kadai.
Allah ya ce, akwai cuta a zukatansu. Cutar kuwa ita ce ta shakka da ruɗani da munafunci, wannan ya sanya Allah ya ƙara musu wata cutar, domin duk sanda aka saukar da wata aya ga Annabi SAW to za su kafirce mata, sai cutar zukatansu ta ƙara hauhawa, haka za su yi ta rayuwa har mutuwarsu sannan su je su tarar da azaba mai radadi tana jiran su a lahira saboda ƙaryar da suke ƙirƙira da kuma ƙaryara Annabi SAW da suka riƙa yi.
Narrated Abu Huraira:
The Prophet (ﷺ) said, "The signs of a hypocrite are three: 1. Whenever he speaks, he tells a lie. 2. Whenever he promises, he always breaks it (his promise ). 3. If you trust him, he proves to be dishonest. (If you keep something as a trust with him, he will not return it.)" https://sunnah.com/bukhari:33 |
An karɓo daga Abu Huraira rA yana cewa:
"Manzon Allah SAW yana cewa: "Alamar munafiƙi 3 ce: 1. Idan ya yi magana sai ya yi ƙarya, 2. kuma idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, 3. idan kuma aka amince masa sai ya yi ha'inci." [Bukhari #33 da Muslim #59] |
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Faɗakarwa a kan haɗarin munafurci da munafukai.
- Furta kalamar shahada da baki kawai ba zai wadatar ba har sai zuciya ta ƙudurce ta, domin Musulunci na gaskiya shi ne miƙa wuya ga Allah SWT a zahiri da baɗini.
- Munafukai suna nuna wa Musulmi cewa sun yi imani, alhalin ƙarya suke yi ba su yi imani ba.
- Luɗufin da Allah ya yi wa muminai yayin da ya tona asirin munafukai tun da wuri.
- Tabbatar da cewa munafukai ba muminai ba ne samsam.
- Munafukai mayudara ne, don haka wajibi ne ga muminai su yi hattara da su.
- Duk yaudarar mayaudari a kansa za ta ƙare.
- Munafurci yana toshe basira, don haka duk wani munafuki ba ya fahimtar cewa kansa yake cuta.
- Munafurci muguwar cuta ce wadda idan mai ita bai yi saurin magance ta ba, to za ta yi ta ƙaruwa ne har ta kai shi ga aukawa cikin azaba mai raɗaɗi.
- Haɗarin ƙarya da ƙaryara gaskiya. Ƙarya a wurin munafiki ƙaruwa take yi koyaushe.
Baqara 11-13
- Idan kuma aka ce musu: "Kada ku yi ɓarna a bayan ƙasa", sai su ce: "Mu fa masu gyara ne kawai." --Quran/2/11
- Saurara, lalle su su ne maɓarnata, amma ba sa jin hakan. --Quran/2/12
- Idan kuma aka ce da su: "Ku yi imani kamar yadda mutane suka yi imani", sai su ce: "Shin za mu yi imani ne kamar yadda wawaye suka yi imani?" Saurara, lalle su ne wawayen, sai dai ba su sani ba. --Quran/2/13
Tafsiri:
Har ila yau, Allah yana ƙara bayyana wani mugun halin na munafuƙai wanda shi ne, duk sa'adda sahabbai za su yi musu wa'azi su nuna musu kuskurensu, su neme su da su tuba zuwa ga Allah, sai su riƙa yi wa sahabban kallon wasu wawaye jahilai marasa hankali da har suka yarda suka bar garuruwansu da gidajensu da dukiyoyinsu suka yi hijira don wai su yi addinin Musulunci; sai su nuna su fa ba za su taɓa yin wauta irin wannan ba. Sai Allah ya mayar musu da martani da cewa, ai ko su ne tsantsar wawaye, tun da har suka guje wa abin da zai amfane su na imani da Allah suka rungumi abin da zai cutar da su saboda tsabar jahilci da wauta.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Munafurci babbar ɓarna ce a bayan ƙasa.
- Yana daga cikin babban bala'i ga mutum a ƙawata masa mummunan aikinsa har ya riƙa ganinsa kyakkyawa.
- Haɗarin dake tattare da rikirkicewar tunani wanda zai kai ga maɓarnaci ya riƙa ɗaukan kansa mai shi mai gyara ne.
- Daga cikin mummunar siyasar munafukai a kowane zamani shi ne yadda suke sanya rigar masu kawo gyara cikin al'umma, masu fafutukar daidaita rayuwar jama'a, amma a fakaice suna yaƙi da addini da masu addini, suna yi wa abokan gabar Musulmi farfaganda domin lalata aƙidun Musulmi da kyawawan halayensu na addini da zamantakewa da shugabanci.
- Faɗakar da muminai da jawo hankalinsu a kan kada su ruɗu da da'awar munafukai da yaudararsu.
- Kiran munafukai zuwa ga abin alheri sau tari ba shi da wani amfani, domin yadda suke taƙama da marnar da suke kai yana ƙara musu bijire wa gaskiya.
- Faɗakar da Musulmi da kada su ruɗu da farfagandar Munafukai.
- Kariyar da Allah yake ba wa sahabban Annabi SAW da muminai.
- Tabbatar da hajilcin munafukai.
- Duk ɓarancin da ba ya gane cewa shi maɓarnaci ba ne, to shi wawa ne.
Baqara 14-15
- Idan kuma suka haɗu da waɗanda suka yi imani sai su ce: "Mun yi imani." To amma idan suka keɓanta da shaiɗanunsu (iyayen gidansu) sai su ce: "Mu fa lalle muna nan tare da ku, mu kwai izgili ne muke yi." --Quran/2/14
- Allah Yana yi musu izgili, kuma Yana yi musu talala cikin shisshiginsu suna masu ɗimuwa. --Quran/2/15
Tafsiri:
Wata muguwar sifa ta munafuƙai kuma har ila yau ita ce, yin fuska-biyu, wato idan sun shiga cikin muminai ko sun haɗu da su a hanya sai su riƙa nuna musu suna tare da su, su ma wai muminai ne. To amma da zarar sun koma ga manyan kafirai ko Yahudawa sai su nuna musu cewa, mu fa tare da ku muke, ku bar waɗancan muminai izgili kawai muke yi musu, amma zuciyarmu ba ta son su ko kaɗan. Allah SWT ya mayar musu da martani da cewa: Ai Allah ne yake yin izgili gare su, shi ya sa ya ƙyale su ba tare da ya ba wa muminai dama su gama da su ba, yake kuma ƙawata musu munanan ayyukansu, har ma suke zaton ko a kan gaskiya suke, ba su san cikin ɗimuwa da duhu suke rayuwa ba.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Ƙasƙancin munafukai da wulaƙanta kansu da suke yi da kuma nuna son duniya shi ne ya haifar musu da munafurci a zukatansu.
- Duk wanda zai riƙa nuna fuska-biyu ya kuma riƙa ɓoye rashin gaskiyarsa, to wannan ƙasƙantaccen mutum ne.
- Bayyana yadda munafukai suke haɗa kai da kafirai maƙiya Musulunci domin yaƙar Musulmi.
- Damuwar munafukai har kullum ita ce, yadda za su gamsar da 'yan'uwansu kafirai cewa, manufarsu guda ɗaya ce, kuma su fa imaninsu ba na gaskiya ne ba.
- Bayanin yadda Allah SWT yake kunyata munafukai, yake fallasa abin da suke faɗa wa kafurai a asirce.
- Haɗarin yi wa muminai izgili, domin yin haka siffa ce ta munafukai.
- Irin aikin mutum irin sakamakonsu, yadda munafukai suke yi wa muminai izgili su ma haka Allah SWT yake saka musu da yi musu izgili.
Aya 16
Waɗannan su ne suka musanya shiriya da ɓata, don haka kasuwancinsu bai yi riba ba, kuma ba su zamo shiryayyu ba.
Tafsiri:
A nan Allah SWT yana fito da haƙiƙanin matsayin munafuƙai, ta yadda suke nuna tsananin sha'awarsu da ƙaunarsu ga hanyar ɓata, suke ɗaukar ta a matsayin wata kadara mai daraja da za su iya kashe ko nawa ne don su mallake ta. Don haka suka amince su bayar da shiriya a matsayin kuɗin da za su fanshi wannan mummunar kadara (wato ɓata) da ita. Wannan shi ne haƙiƙanin kasuwancinsu a duniya; ashe kuwa wannan kasuwanci ne maras riba, kuma mai cike da hasara ta duniya da ta lahira.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Bayani game da tsantsar wautar munafukai da rashin basirarsu wadda har ta kai su suke fifita ɓata a kan shiriya, domin kuwa babu wautar da ta kai irin ta wanda zai ba da kuɗi tsababa don a ba shi wata lalatacciyar kadara.
- Duk wani attajiri yana fatan samun riba ne daga abin da zai kashe kuɗinsa ya saya. To haka su ma munafukai suna zaton cewa za su sami riba a cikin wancan lalataccen kasuwanci da suke yi, alhalin asara kawai suke tabkawa.
- Shiriyar Allah ita ce riba ta gaske. Duk wanda yake kan shiriya ta Allah SWT to shi ne mai samun ribar kasuwancinsa a duniya da lahira. Wanda kuwa ya rungumi ɓata kamar munafuki, to ya tabka hasara ta har abada.
- Sau tari munafukai ba su cika shiriyuwa su dawo kan gaskiya ba.
Baqara 17-18
- Misalinsu kamar misalin wanda ya wahala ga kunna wuta ne, yayin da ta haskaka abin da yake daura da shi, sai Allah Ya tafiyar da haskensu Ya bar su cikin duffai ba sa gani. --Quran/2/17
- Su kurame ne, bebaye ne, makafi ne, don haka ba za su taɓa dawowa (kan gaskiya) ba. --Quran/2/18
Tafsiri:
A nan ma Allah yana ƙara yi mana bayani ne a kan waɗannan munafuƙai, inda ya yi mana kwatance na zahiri domin mu fahimta da gaggawa; ya faɗa mana cewa, misa;in halin da munafuƙai suka tsinci kansu a ciki kamar misalin wani mutum ne da yake tafiya ya samu kansa cikin matsanancin duhu, ga tsoro da ya mamaye shi ta ko'ina, sai ya yi ta fafutukar neman haske, ya wahala sosai har ya samo wuta wadda ta haskaka masa kewayansa, ya zamanto yana ganin komai da ke gabansa da bayansa, ya daina jin tsoron da yake ciki a farko, ya fara farin ciki, sai kwatsam hasken ya ɗauke, ga wuta na ci gabansa balbal, ga zafinta yana bugo shi, amma kuma babu haske sai dai duhu yana dukan duhu; ga duhun dare, duhun hadari, ga na ruwan sama, ga duhun rashin haske, ya samu kansa cikin duffai daban-daban ba ya ganin ko da tafin hannunsa.
To haka sha'anin munafukai yake. Da farko suna rayuwa cikin duhun kafirci, sai Musulunci ya bayyana, sai suka ɗosani haskensa, suka sami kariya ta rayukansu da dukiyoyinsu. To amma da yake ba a kan gaskiya suka yi imani ba, sai hasken Musuluncin ya ɓace musu, yayin da suka mutu aka kai su ƙaburburansu, sai suka tsinci kansu cikin duhu na dukan duhu, ga duhun ƙabari, ga na kafirci, ga na munafunci, ga na saɓon Allah iri-iri, ga uwa-uba duhun wutar Jahannama. Tir da wannan makoma.
Dalilin haka ya sa Allah ya ce da su, su kurame ne ba sa jin duk wata gaskiya ji na fahimta; bebaye ne ba sa iya faɗin gaskiya, sannan makafi ne ba sa ganin gaskiya su bi ta. Don haka ne ma babu yadda za a yi su dawo kan hanya.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Fasahar Alƙur'ani wajen buga misalai don a fahimta.
- Munafukin da ya yi imani sannan daga baya ya yi ridda, to munafurcinsa zai gusar da alamun hasken imaninsa, don haka rayuwarsa ba ta da sauran wani amfani.
- Munafukai sun shiga Musulunci ne saboda kwaɗayin samun ganimar duniya, don kuma su kare kansu daga kisa. To amma da zarar sun mutu duk wannan tagomashin da suke samu ya ƙare, sai azaba mai raɗaɗi ce za su haɗu da ita a ranar alƙiyama.
- Munafukai ba sa ƙaruwa da komai na hasken wahayi da shari'a. Idan sun halarci majalisin da ake karanta shari'ar Allah, to kafircinsu da munafurcinsu ba za su ƙyale su su amfana da komai ba.
- Sanin gaskiya ba zai yi wa bawa amfani ba idan har bai miƙa wuya ya karɓi gaskiyar ba.
- Munafukai a duniya suna rayuwa ne ta ɗimuwa da kiɗimewa, domin suna cikin duhu ne iri-iri da zai hana su ganin gabansu.
- Hanyar gaskiya ɗaya ce, amma hanyoyin ɓata yawa gare su.
- Munafukai ba sa amfana da zamansu cikin mutanen kirki, domin munafurcinsu ba zai bar su su amfana da su ba.
- Ishara zuwa ga cewa, duk wanda zai san gaskiya amma ya yi watsi da ita, to lamarinsa ya fi muni a kan wanda da ma can bai san gaskiyar ba.
- Gaɓoɓin da Allah ya ba wa duk wani mutum don ya amfana da su, munafukai sam ba sa amfana da su.
- Makantar zuciya da ta basira ta fi makantar ido muni. Kuma munafukai ba za su taɓa dawo wa kan gaskiya ba, domin suna ganin kyawon abin da suke aikatawa.
Baqara 19-20
- Ko kuma (misalinsu) kamar wani mamakon ruwan sama ne, wanda yake ɗauke da duffai da tsawa da walƙiya, har ta kai suna sanya 'yan yatsunsu tsawarwaki saboda tsoron mutuwa. Allah Kuma Yana kewaye da kafirai (da iliminsa). --Quran/2/19
- Walƙiyar ta kusa ta fauce idanuwansu. Duk sa'adda ta haska musu sai su ci gaba da tafiya cikin (haskenta); idan kuma ta rufe su da duhu sai su tsaya cak. Da kuwa Allah Ya ga dama da sai Ya tafiyar da jinsu da ganinsu. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai. --Quran/2/20
Tafsiri:
A nan kuma Allah SWT ya bayar da misali na biyu game da munafuƙai. Ya misalta su da mutanen da suke tafiya cikin dare sai ruwan sama ya goce kamar da bakin ƙwarya, sannan ga duhu ya baibaye su ta ko'ina; duhun dare da na hadari da na ruwan sama, baya ga haka, ga tsawarwaki da walkiya. Duk sa'adda walƙiya ta haska sai su ɗan motsa gaba ɗaya daga inda suke. Idan kuma duhu ya rufe su sai su ɗan motsa gaba ɗaya daga inda suke. Idan kuma duhu ya rufe su sai su tsaya cak a inda suke. Sannan idan rugugin tsawa ya dame su sai su sanya yatsunsu cikin kunnuwansu saboda tsoron halaka. Sun manta cewa ilimin Allah da Ƙudurarsa suna zagaye da kafirai.
To kamar haka su ma munafuƙai suke, suna rayuwa cikin duhu iri-iri, suna cikin damuwa, duk sa'adda Musulmai suka samu wata ɗaukaka da rinjaye sai su kawo kai don su sami ganima, amma duk lokacin da wasu ayoyin Quran da suka sauka suna maganar azabar Allah SWT da narkonsa ga munafukai sai su ji kamar asirinsu ne zai tonu. Ba su son sauraron ayoyin da suke bayanin wani umurnin Allah ko haninsa, don haka sai su riƙa toshe kunnuwansu da 'yan yatsunsu. To sai Allah ya razanar da su da cewa, da ya ga dama da ya gusar musu da jinsu da ganinsu, su wayi gari dunɗum ba sa ganin komai ba sa jin komai sakamakon biris da gaskiya da suka yi. Domin kuwa Allah mai iko ne kan komai.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Tsoratarwa da tsawatarwa ga kafurai.
- Yana da kyau Musulmi ya riƙa roƙon Allah SWT ya jiyar da shi daɗi da jinsa da ganinsa.
- Daga cikin mutane akwai wanda ba ya iya ginin hasken gaskiya ko mai karfinsa, domin zuciyarsa ba ta son gaskiya, kamar yadda ido ba ya iya jure wa kallon hasken walƙiya.
- Hasken ilimi da imani a tare suke ga mumini, da shi yake ganin hanyar binsa. Amma kafiri kuwa ba ya iya ganin hanyarsa.
- Guje wa sauraron gaskiya ba zai kuɓutar da mutum ba, ko ya nuna rashin tsayuwar hujja a kansa.
Baqara 21-22
- Ya ku mutane, ku bauta wa Ubangijinku Wanda Ya halicce ku, da wadanda suka gabace ku, ko kwa yi taqwa. --Quran/2/21
- Shi ne Wanda Ya sanya muku ƙasa ta zama shimfida kuma Ya sanya muku sama ta zama gini kuma Ya saukar da ruwa daga sama Ya fitar muku da arziƙi na 'ya'yan itatuwa, don haka kada ku sanya wa Allah kishiyoyi alhalin kuna sane. --Quran/2/22
Tafsiri:
Bayan da Allah ya gama maganar kashe-kashen mutane, wato muminai masu taqwa da siffofinsu da kafirai da siffofinsu da munafukai da nasu siffofin, sai kuma ya dunƙule su gaba daya ya kirawo su zuwa ga bauta masa shi kadai. Da ma bautar ita ce manufar halittarsu, kamar yadda ya fada a cikin Surat Az-Zariyati aya ta 56, Sannan ya kafa musu manya-manyan hujjoji guda hudu:
- Hujja ta farko ita ce, shi ne wanda ya halicce su har da wadanda suka gabace su, ya ba su ci da sha da bukatunsu, don haka wanda ya yi halitta ai shi ne ya fi cancanci a bauta masa ba wani can daban ba.
- Hujja ta biyu ita ce, shi ne wanda ya shimfida musu kasa wadda suke yawo a kanta, su yi gine-ginensu duk a kanta. Lalle wanda ya yi wannan ai shi kadai ya cancanta a bautawa ba wani ba can daban ba.
- Hujja ta uku ita ce, shi ne wanda ya daukaka musu rufin samaniya, ya ƙawata shi da rana da wata da taurari, wadanda suke amfanarsu a rayuwarsu a bayan kasa. Wanda ya yi wannan aiki lalle shi ne ya cancanci bauta ba wani abu ba can daban.
- Hujja ta huɗu ita ce, shi ne ya sauko musu da ruwan sama daga girgije, wanda suke sha su da dabbobinsu, kuma ya shayar musu da gonakinsu suka sami amfanin gona da kayan marmari iri-iri da ganyayyaki daban-daban. Lalle mai wannan aiki shi ne wanda ya cancanci bauta ba wani can daban ba.
Wadannan ayoyi suna nuni ne ga Tahudin Rububiyya wanda yake jagoranci zuwa ga fahimtar Tauhidin Uluhiyya, wato bautar Allah shi kadai ba tare da yi masa kishiya ba.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Imani da Tauhidin Rububiyya yana wajabta wa bawa ya yi imani da Tauhidin Uluhiyya.
- Zamantowar Allah SWT shi ne mahalicci komai, mai kuma bayar da arzuki ga bayinsa, shi ne ya sa ya cancanci a bauta masa shi kadai.
- Taqwa wani babban matsayi ne da ba a samunsa sa ta hanyar tsantanta bauta ga Allah shi kadai.
- A cikin ni'imomin na duniya ni'imar halitta ita ce mafi girma, domin duk wata ni'ima ta ginu ne a kanta.
- Rahamar Allah ga bayinsa da bayanin girman Ƙudurarsa.
- Allah yana ba da arzikinsa na duniya ga kowa da kowa; mumini da kafiri babu banbanci.
- Haramcin sanya wa Allah kishiya ta hanyar shirka babba ko karama.
Baqara 23-24
- Kuma idan kun kasance cikin kokwanto game da abin da Muka saukar wa bawanmu, to ku zo da kwatankwacin sura ɗaya kamarsa, kuma ku kirawo masu taimakonku ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya. --Quran/2/23
- To idan har ba ku aikata hakan ba, kuma ba za ku taɓa iyawa ba, to ku kiyayi wata wuta wadda mutane ne da duwatsu makamashinta; an kuwa tanade ta domin kafirai. --Quran/2/24
Tafsiri:
A wadannan ayoyi Allah yana magana ne a kan gaskiyar annabcin Annabi SAW da gaskiyar Alkur'ani da ya zo da shi. Allah ya kawo wata hujja ce mai karfi wadda za ta kawo karshen duk wani shaci-fadin da kafirai suke yi game da Alqur'ani. Allah ya bayyana cewa, shi fa Annabi SAW, mutum ne kamarsu, yana magana da irin harshensu, kuma bai koyi wani ilimi na rubutu da karatu ba. To idan har shi ne ya kirkiri Alkur'ani da kansa ba wahayi Allah ya yi masa ba kamar yadda suke da'awa, to su ma ai Larabawa ne irinsa, sai su kawo ko da sura daya kamar ta Alqur'ani wajen hikima da fasaha. Kuma suna iya gayyato duk wani wanda suke ganin zai taimaka musu don cim ma wannan bukatar tasu. Idan kuwa har suka kasa yin hakan, kuma ba za su iya din ba, to su yi maza su karbi gaskiya don kare kansu daga azabar Allah wadda wuta ce ba irin wadda suka sani ba a nan duniya, domin ita wannan makamashin hura ta mutane ne masu laifuka da duwarwatsu, kuma an riga an yi tanadinta musamman domin kafirai.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Alkur'ani mu'ujiza ce da Allah SWT Ya kuma ƙalubalanci duk masu fasahar larabawa da su kawo kamarsa amma sun kasa.
- Alkur'ani ne mafi girmar mu'ujiza da Allah SWT ya ba wa Manzonsa SAW.
- Matsayin zama bawan Allah matsayi ne babba, saboda haka Allah ya zabi ya siffanta Manzonsa SAW da shi a irin wannan babban wuri.
- Tabbatar wa kafurai cewa ba za su taba kawo wata magana kamar Alkur'ani ba har abada.
- Tabbatar da gaskiyar Alkur'ani, domin ya nuna musu cewa ba za su kawo kamarsa ba har abada, kuma ga shi ya tabbata din sun kasa kawo irinsa.
- Wuta tana nan, Allah SWT ya riga ya halicce ta, ya kuma tanade ta domin kafirai.
Baqara 25
25. Kuma ka yi albishir ga wadanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai cewa suna da wasu aljannatai wadanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu. Duk sa'adda aka arzuta su da 'ya'yan itatuwa daga gare ta sai su ce: "Wannan shi ne irin abin da aka arzuta mu da shi ɗazu." An kawo musu shi yana mai kama da juna, kuma suna da wasu matan tsarkaka a cikinta, kuma su masu zama ne a cikinta dindindin.
Tafsiri:
Bayan Allah ya ambaci sakamakon kafirci a ayar da ta gabata, sai kuma a nan ya ambaci sakamakon wadanda suka yi imani, domin wannan shi ne tsarin salon Alƙur'ani wajen haɗa tsoratarwa da kwadaitarwa. Allah ya fada wa Annabi SAW cewa, ya yi albishir ga wadanda suka yi imani da shi da abin da ya zo da shi na gaskiya, kuma suka aikata kyawawan ayyuka wadanda suka nuna gaskiyar imaninsu da su, ya yi musu albishir da cewa, a lahira suna da wani sakamako na gidajen Aljanna wadanda koramu suke gudana ta karkashin bishiyoyinsu da shuke-shukensu da dakunansu. Duk sa'adda aka kawo musu kayan marmari sai su zaci irin wanda aka taba kawo musu ne ba da dadewa ba a Aljanna, saboda kamanninsu iri daya ne, amma ba su san akwai banbanci ba wajen dandano. Sannan baya ga kayan marmari na Aljanna, har ila yau, suna da wasu mata na aure wadanda suke tsarkaka ne daga duk wani abin kyama, kamar yadda suke da kyawawan halaye da dabi'u. Sannan wani abin kwantar da hankali gare su shi ne, za su dawwama a cikin wannan jin dadi ba zai yanke musu ba har abada.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Babu mai shiga Aljanna sai wanda ya yi imani ya kuma yi aiki nagari.
- Sakamakon 'yan Aljanna ya fi ayyukansu.
- Cikar Kudurar Allah SWT.
- Sakamakon 'yan Aljanna ni'ima ce cikakkiya. Allah ya musu tanadin kayan dadi iri-iri tare da kari.
- Kwadaita wa zukata ni'imomin gidan Aljanna don zaburar da su su yi aiki nagari cikin nashadi da walwala.
Baqara 26-27
- Lalle Allah ba Ya jin kunyar buga kowanne irin misali komin kankantarsa, sauro da abin ya fi shi. To amma wadanda suka yi imani suna sanin cewa, lalle shi (wannan misali) gaskiya ne daga Ubangijinsu. Amma wadanda suka kafirta sai su rika cewa: "Me Allah Yake nufi da wannan misalin?" Yana kuwa batar da mutane da yawa da shi, kuma Ya shiryar da mutane da yawa da shi, kuma ba kowa Yake batarwa da shi ba sai fasikai. --Quran/2/26
- Wadanda suke warware alkawarin Allah bayan ƙulla shi, kuma suke yanke abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi, kuma suke ɓarna a bayan ƙasa. Wadannan su ne cikakkun hasararru. --Quran/2/27
Tafsiri:
A wadannan ayoyi kuma Allah yana sanar da cewa, ba ya jin kunyar bayar da wani misali da kowane abu na halittarsa komai/komin kankantarsa kuwa, kamar sauro da abin da ya ɗara shi girma ko kankanta saboda hikimar da take cikin wadannan misalan da fito da bayanai dalla-dalla don a gane. To yayin da Allah ya ba da irin wadannan misalan masu sauraro sukan kasu gida biyu;
- kashi na farko su ne muminai masu yaqini cewa, wannan misali da Allah ya bayar gaskiya ne.
- Kashi na biyu kuma su ne kafirai, sai wannan misali ya ɗimautar da su har su nuna rashin yardarsu a kai, suna ganin don me Allah zai rika bayar da irin wadannan misalin, sai su kara kafircewa a kan kafircinsu na farko.
Sun kasa gane cewa, hikimar da ta sa Allah yake yin haka ita ce don kara bambancewa tsakanin mumini da kafiri. Don haka wadannan misalan sukan zama sanadiyyar shiriyar muminai da dama, sannan kuma sukan zama sanadiyyar bacewar kafirai da dama. To amma fa ba wasu ne suke bacewa ta hanyar wadannan misalan ba sai wadanda suke kangare wa ɗa'ar Allah, wadanda suke warware duk wani alƙawari da suka yi tsakaninsu da Allah, sannan suke yi wa shari'ar Allah karan-tsaye, kamar ƙin sadar da zumunci, sannan su yi yaɗa ɓarna ta kafirci da munafinci da zalunci a bayan ƙasa. To irin wadannan halaye nasu su ne suka yi katutu a zukatansu har suka toshe musu zukata ya zamana ba su fahimtar duk wani misali da Allah zai bayar a Littafinsa.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Tabbatar wa da Allah SWT siffar kunya kamar yadda ya dace da girmansa da ɗaukakarsa.
- Haɗarin yin izgili da maganar Allah SWT.
- Duk wani abu na gaske da Allah SWT ya tabbatar da shi, ba ya halatta wani ya yi musun samuwarsa.
- Wani abu guda yakan iya zama sanadiyar shiriyar wani, kuma sanadiyar ɓatan wani.
- Haɗarin yin jayayya ba bisa gaskiya ba.
- Ma'abota shiriya ko da kuwa su 'yan kaɗan ne a cikin mutane, to amma alherinsu da amfaninsu mai yawa ne. Su kuma ma'abota ɓata ko da suna da yawa, amma alherinsu da amfaninsu kaɗan ne a cikin al'umma.
- Yin jayayya da hukuncin Allah SWT abu ne da yake kore imani.
- Bai dace kunya ta hana mai kira zuwa ga Allah ya bayyana wani hukunci na Allah ba ko faɗar wata gaskiya, ko da kuwa yin haka zai jawo masa suka daga masu suka.
Baqara 28-29
- Ta yaya kuke kafirce wa Allah alhalin a da kun kasance matattu, sannan Ya raya ku, sannan zai kuma mayar da ku matattu sannan Ya raya ku (a karo na biyu) sannan zuwa gare Shi ake mayar da ku? --Quran/2/28
- Shi ne wanda Ya halitta muku abin da yake cikin ƙasa gaba ɗaya, sannan Ya nufi sama Ya daidaita su sammai bakwai, kuma Shi Masanin komai ne. --Quran/2/29
Tafsiri:
A nan Allah yana nuna mamakin yadda wadannan kafirai masu kafirce masa da kafirce wa shiriyar da ya aiko Manzonsa SAW da ita, tare da cewa, dalilai masu nuna girman Qudurarsa sun bayyana a sarari. Daga cikin irin wadannan dalilai akwai ewa Allah ne ya kashe su sau biyu ya kuma raya su sau biyu.
- Kashewa ta farko, ita ce lokacin da babu si sannan ya samar da su;
- kashewa ta biyu, ita ce lokacin da yake karbar rayukansu yayin mutuwarsu.
Rayawa ta farko ita ce, halittarsu babu, sannan rayawa ta biyu ita ce, tayar da su daga ƙaburburansu bayan sun mutu. Su kansu kafirai za su tabbatar da hakan ranar gobe ƙiyama, kamar yadda ya zo a 'Suratu Ghafir', aya ta 11.
Sannan yana daga cikin manya-manyan dalilan cancantar a bauta wa Allah shi kadai, cewa ya halicci abin da yake cikin kasa gaba daya domin amfanin dan'Adam, sannan bayan ya gama halittar kasa ya nufi sama ya yi mata kyakkyawar halitta ya mayar da ita sammai bakwai. Kuma shi mai cikakken sani ne ga duk abin da ya halitta, kuma iliminsa ya game ko'ina.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Cikar Ƙudurar Allah da tabbatar da tashi bayan mutuwa, kuma makomar duk halitta zuwa ga Allah take.
- Ni'imar samuwa daga babu, ni'ima ce da ta cancanci a gode wa Allah SWT a kanta, a bauta masa shi kadai kada a kafirce masa.
- Bayanin halaccin komai daga abubuwan da Allah ya hore wa ɗan'adam domin amfaninsa, sai abin da nassi ya bayyana haramcinsa.
- Allah ya hore komai a duniya domin amfanin ɗan'adam, don haka bai dace ga ɗan'adam ba ya bautar da kansa ga duniya, idan kuma ya yi haka to ya hallaka kansa da kansa.
- Tunatar da ɗan'adam ni'imomin da Allah SWT ya yi masa domin ya gode masa ta hanyar bauta masa shi kadai.
- Yalwar ilimin Allah SWT da gamewarsa ko'ina.
Baqara 30-33
- Kuma ka tuna sa'adda Ubangijinka Ya ce da mala'iku: "Lalle ni zan sanya wani halifa a bayan ƙasa." Suka ce: "Yanzu za Ka sanya mata wanda zai yi ɓarna a cikinta kuma ya zubar da jini, alhali ga mu muna tasbihi tare da gode Maka, kuma muna tsarkake Ka?" (Allah) Ya ce: "Ni fa tabbas Na san abin da ku ba ku sani ba." --Quran/2/30
- ˹Remember˺ when your Lord said to the angels, “I am going to place a successive ˹human˺ authority on earth.” They asked ˹Allah˺, “Will You place in it someone who will spread corruption there and shed blood while we glorify Your praises and proclaim Your holiness?” Allah responded, “I know what you do not know.”
- And [mention, O Muhammad], when your Lord said to the angels, "Indeed, I will make upon the earth a successive authority." They said, "Will You place upon it one who causes corruption therein and sheds blood, while we declare Your praise and sanctify You?" Allah said, "Indeed, I know that which you do not know."
- Kuma sai (Allah) Ya koya wa Adamu dukkan sunaye (na abubuwa) sannan Ya kawo su gaban mala'iku, sai Ya ce: "Ku fada min sunayen wadannan abubuwan in kun zamanto masu gaskiya." --Quran/2/31
- Sai suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka, ba mu da wani ilimi sai wanda Ka sanar da mu. Lalle Kai ne cikakken Masani, Mai hikima." --Quran/2/32
- Ya ce: "Ya Adamu fada musu sunayensu." Yayin da ya fada musu sunayensu, sai (Allah) Ya ce: "Ba Na fada muku cewa, lalle Ni ne Nake sane da gaibin sammai da kasa ba, kuma Nake sane da abin da kuke bayyanawa da kuma abin da kuke boyewa ba?" --Quran/2/33
Tafsiri:
Bayan da Allah ya gama maganar halittar kasa da abubuwan da ke cikinta, da halittar sammai da abubuwan da suka kunsa, sai ya shiga bayanin halittar dan'adam na farko, wato Annabi Adam AS wanda Allah ya damƙa masa alhakin raya wannan kasar ta hanyar bin tsarin da ya hado shi da shi na shiriya, da kuma shimfida adalci a bayan kasa da bauta masa shi kadai ba tare da hada shi da komai ba.
Allah yana ba wa Annabinsa SAW labarin abin da ya fada wa mala'iku na cewa, zai halicci wata halitta da zai ajiye a bayan kasa, wadanda wasunsu za su rika maye gurbin wasu, wato Annabi Adamu AS da zurriyarsa.
- Allah was telling His Prophet (PBUH) about what He had told the angels, that He would create a creation that He would upon the earth, some of whom would replace some, namely Prophet Adam (PBUH) and his descendants.
Sai mala'ikun suka yi wa Allah tambayar neman sani, amma ba ta jayayya ba, <>
The angels then asked Allah genuinely for knowledge not out of argument,
suka ce: "Shin za ka ajiye wadanda za su rika barna a bayan kasa, suna kashe juna, alhali ga mu muna yi maka tasbihi da tsarkake ka a ko da yaushe? Me zai hana ka saka mu a madadinsu?"
Sai Allah ya fada musu cewa, akwai abin da ba su sani ba na maslahar da ke tattare da sanya dan-Adam ya zama khalifa a bayan kasa.
- Then God told them that there was something they did not know about the benefits involved in making Adam a caliph on earth.
Daga nan sai Allah ya fara nuna wa mala'ikun wasu hikimomin da yake nufi game da halittar Annabi Adam AS, sai ya koyar da shi sunayen dukkanin abubuwa sannan ya nuna wa mala'iku su nemi su fada masa sunayensu idan har gaskiya suke a da'awar sun san abubuwa, kuma sun fi Annabi Adamu AS cancantar khalifanci a bayan kasa. To fa a nan take sai mala'iku suka tsarkake Ubangijinsu, kuma suka ƙara tabbatar da cewa, lalle su ba komai suka sani ba. Allah ne ya san komai kuma shi ne yake saka duk wani abu a mahallinsa da ya dace. To daga nan sai Allah ya umarci Annabi Adamu AS da ya faɗa musu sunayen wadannan abubuwan. Yayin da kansu, kuma sai Allah ya ƙara tuna musu cewa, da man ai shi ne masanin gaibun da yake sama da wanda yake ƙasa, kuma ya san abin da suke bayyanawa da abin da suke boyewa.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Allah SWT yakan jarrabi bayinsa da abin da ya ga dama. Allah ya jarrabi mala'ikunsa da halittar Annabi Adamu AS, sai ya bayyana a gare su cewa, ba su gane hikimar da take tattare da halittar Adamu da ta 'ya'yansa a bayansa ba.
- Dacewar yabo ga wanda ya cancanci yabo da bayyana falalar mai falala, musamman ga wanda bai san shi ba, kamar yadda Allah SWT ya yabi Adamu AS.
- Mala'iku suna ƙin aukuwar ɓarna a bayan ƙasa.
- Halaccin yin tambaya game da hikimar yin wata halitta idan ya kasance manufar tambayar ita ce neman sani, ba nuna rashin yarda ba.
- Mala'iku ba su san gaibu ba.
- Falalar Annabi Adamu AS da matsayinsa a wurin Allah.
- Allah ya yi magana da Annabi Adamu AS, don haka shi Annabi ne da Allah ya yi magana da shi, kamar yadda ya zo a cikin hadisin da Ibn Hibban ya ruwaito. [Ibn Hibban #6190]
- Bayanin ladabin mala'iku ga Ubangijinsu.
- Dalili game da fifita annabawa a kan mala'iku.
- Girman matsayin ilimi da falalarsa da falalar mai ilimi.
- Allah ne kadai masanin gaibun sammai da kasa da abin da yake boye a cikin zukatan bayinsa.
Baqara 34-39
- Kuma ka tuna lokacin da Muka ce wa mala'iku: "Ku yi sujjada ga Adamu." Sai duk suka yi sujjada, in ban da Iblis, sai shi ya ƙi, ya kuma yi girman kai, kuma ya tabbata a cikin kafirai. --Quran/2/34
- Kuma Muka ce: "Ya kai Adamu, ka zauna gidan Aljanna kai da matarka, kuma ku ci (kayan marmarinta) cikin yalwa a duk inda kuka ga dama, kada kuma ku kuskura ku kusanci wannan bishiyar, sai ku kasance daga cikin azzalumai." --Quran/2/35
- Sai Shaidan ya sa suka zame, sai ya fitar da su daga ni'imar da suke ciki. Sai Muka ce: "Ku sauko ƙasa sashinku yana mai gaba da sashi; kuma kuna da mazauni a bayan ƙasa da wani jin daɗi zuwa wani ɗan lokaci." --Quran/2/36
- Sai Adamu ya karɓi wasu kalmomi daga Ubangijinsa (na neman gafara), sai Ya yafe masa; lalle Shi ne Mai yawan karɓar tuba kuma Mai yawan jin ƙai. --Quran/2/37
- Muka ce: "Dukkanku ku sauko daga cikinta, sannan idan wata shiriya ta zo muku, to wadanda suka bi shiriyata, babu wani ƙ a tare da su, kuma ba za su yi baƙin ciki ba. --Quran/2/38
- Kuma wadanda suka kafirta kuma suka ƙaryata ayoyinmu, wadannan su ne 'yan wuta, su masu dawwama ne a cikinta. --Quran/2/39
Tafsiri:
A wadannan ayoyi, Allah yana sanar da Manzonsa SAW cewa, ya umarci mala'iku da su faɗi su yi sujjada ga Annabi Adamu (AS), kuma nan take suka karɓa umarninsa suka faɗi suka yi masa sujjada, sai Iblis shi kaɗai ya nuna girman kai, ya bijire wa umarnin Allah ya ƙi yi wa Annabi Adamu sajjada. Sai Allah ya umarci Annabi Adamu da matarsa Hawwa'u da su shiga Aljanna su zauna a cikinta, ya yi musu izini da su ci komai na kayan marmari da ke cikinta a wadace, in ban da wata itaciya guda ɗaya wadda ya nuna musu ita ya ce, su nisance ta kada su ci 'ya'yanta domin idan har suka ci to sun ƙetare iyakokin da Allah ya gindaya musu.
Sai Shaiɗan ya yaudare su ta hanyar yi musu waswasi ya sa suka ci 'ya'yan wannan bishiyar, wanda a dalilin haka Allah ya fitar da su daga gidan Aljanna, ya umarce su da su dawo bayan ƙasa su zauna, wanda a nan ne ƙiyayya za ta bayyana a tsakaninsu, kuma nan ne wurin rayuwarsu, idan kuma sun mutu a cikinta ne za a binne su har zuwa lokacin tashin alƙiyama. Bayan haka kuma sai Allah ya laƙanta wa Annabi Adamu wasu kalmomi da zai faɗa Allah ya yafe masa laifinsa, sai ya faɗa shi da matarsa, kuma Allah ya karɓi tubansu domin shi ne mai yafe wa muminai duk wani laifi da za su yi su nemi ya yafe musu.
Daga nan kuma Allah ya umarci Annabi Adamu da Hawwa'u da Iblis da su sauko daga gidan Aljanna gaba ɗaya, kuma ya faɗa musu cewa, idan wani abu na shiriya ya zo musu, littafi ne ko kuma wani manzo ne wanda zai nusar da su hanyar shiriya, idan har suka karɓe shi suka yi aiki da shi to za su samu cikakken zaman lafiya da farin ciki na har abada. Wanda kuwa ya bijire ya ƙi yarda da gaskiya ya ƙaryata ayoyin Allah, to wannan sakamakonsa gidan wuta ne, kuma zai zauna ciki har abada babu fita.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Babbar karramawar da Allah SWT ya yi wa Annabi Adamu da zurriyarsa.
- Bayanin kafircin Iblis da girman kansa wajen ƙin bin gaskiya da wulaƙanta halittar Allah SWT.
- Falalar mala'iku da yadda suke amsa umarnin Allah cikin gaggawa.
- Duk hukunci na Allah ne, shi yake hukunta abin da ya ga dama. Ya yi umarni a yi wa wanda ya ga dama sujjada, ya hana yi wa wani sujjada idan ya ga dama, kamar yadda ya hana wannan al'umma yi wa wani sujjada ba shi ba.
- Wajabcin bin umarnin Allah SWT ko da ya saɓa wa son zuciya.
- Girman kai game da yi wa Allah ɗa'a yakan iya kai bawa zuwa ga kafurci.
- Bayani game da baiwar da Allah ya yi wa Annabi Adamu da matarsa Hauwa ta shiga gidan Aljanna.
- 'Ya'yan marmarin gidan aljanna ana samun su a koyaushe ake da buƙatarsu.
- Allah SWT yakan iya jarrabar bayinsa ta hanyar hana su wasu abubuwa.
- Idan shari'a ta haramta wani abu to sai ta hana duk wani abu da zai iya kai mutum ga abin da aka haramta masa.
- Mahallin zama da samun abinci suna daga cikin manya-manyan ni'imomi ga ɗan'Adam.
- Abubuwan da aka halatta sun fi waɗanda aka haramta yawa.
- Haɗarin saɓon Allah SWT, domin yakan yi sanadiyyar bawa ya rasa wata babbar ni'imata ta Ubangijinsa.
- Samuwar Aljanna tun gabanin halittar ɗan'adam.
- Ƙiyayyar Iblis ga ɗan'adam da ƙoƙarinsa koyaushe na ya ga ya ɓatar da shi, ya jefa shi cikin saɓon Allah SWT, ya raba shi da ni'imar Allah.
- Babu wani wuri da dan'adam zai iya rayuwa sai a bayan ƙasa. Duk wani yunƙuri da fafutuka da wasu suke yi na neman wani wuri na daban da za a rayu a cikinsa ba doron ƙasa ba, to aikin banza ne ba zai yi nasara ba.
- Duniya ba matabbata ce ba. Rayuwar dan'adam a cikinta iyakantacciya ce.
- Rahamar Allah SWT ga dan'adam da ya tanada masa matsuguni tun kafin ya saukar da shi ƙasa.
- Baiwar da Allah ya yi wa Adamu da Hauwa'u; bai bar su cikin zunubi ba, ya bude musu kofar tuba, suka kuma tuba Allah ya karbi tubansu ya kara musu daraja da matsayi a wurinsa.
- Falalar tuba zuwa Allah SWT. Idan bawa ya yi laifi ya kuma tuba zuwa ga Allah SWT tuba ta gaskiya, to Allah zai yafe masa ya karbi tubarsa.
- Wani abu marar dadi zai iya faruwa ga bawa, amma daga karshe ya zamo masa alheri. Don haka koyaushe bawa ya zamanto yana mayar da al'amarinsa ga Allah yana neman yardarsa cikin komai.
- Tun farkon saukowar dan'adam bayan kasa Allah SWT ya hado shi da shiriya da tsarin da zai rayu a kansa, saboda haka babu wani lokaci da Allah SWT ya bar dan'adam sakaka ba tare da wata shiriya ba.
- Bin shiriyar Allah SWT da tsarinsa kadai ne zai haifar wa da dan'adam nutsuwa da kwanciyar hankali a rayuwarsa ta duniya da ta lahira. Kauce wa tsarin Allah SWT shi ne yake bude masa duk wata kofar fitina da rashin zaman lafiya.
- Daga cikin dalilan dauwama a cikin wutar Jahannama akwai karyata ayoyin Allah SWT. Wanda ya karyata ayar Allah daya da ya saukar to ya kafirta, kuma zai dauwama a cikin wuta ranar alqiyama.
Baqara 40-46
- Ya ku 'ya'yan Isra'ila, ku tuna ni'imata da Na yi muku, kuma ku cika alkawarina zan cika muku alkawarinku, kuma ku kasance Ni Ni kadai. --Quran/2/40
- Kuma ku yi imani da abin da Na saukar yana mai gaskata abin da yake tare da ku (na wahayi), kada kuma ku zama farkon jinsinku da zai kafirce masa, kuma kada ku sayar da ayoyina da dan kudi kadan, kuma ku kiyaye dokokina. --Quran/2/41
- Kuma kada ku gauraya gaskiya da karya, kuma ku boye gaskiya, alhalin kuna sane. --Quran/2/42
- Kuma ku tsayar da salla, kuma ku ba da zakka, kuma ku yi ruku'i tare da masu ruku'i. --Quran/2/43
- Shin yanzu kwa rika umartar mutane da ayyukan alheri ku kuma kuna mantawa da kawunanku, alhalin kuna karanta Littafi? Ashe ba za ku hankalta ba? --Quran/2/44
- Kuma ku nemi agajo ta hanyar hakuri da kuma salla, kuma lalle ita (salla) babban abu ne sai dai ga masu kaskantar da kai. --Quran/2/45
- Wadanda suka tabbatar da cewa, su masu haduwa ne da Ubangijinsu, kuma su zuwa gare Shi suke komawa. --Quran/2/46
Tafsiri:
Bayan da Allah ya ambaci asalin halittar dan-Adam da kuma kiyayyar Shaidan a gare shi, ya kuma faɗa wa Annabi Adamu da zurriyarsa bayan ya saukar da su bayan ƙasa, ya ce kuma zai zo musu da shiriya wadda duk wanda ya bi ta to ya kuɓuta daga kowane irin tsoro da baƙin ciki. Sannan ya yi kashedi ga wadanda za su saɓa wa wannan shiriyar da fuskantar wata azaba mai tsanani ta wutar Jahannama.
To, a wadannan ayoyi Allah yana bayani a kan Banu Isra'ila ne wadanda suka yi ƙaurin suna wajen nuna wa annabawansu taurin kai da butulce wa ni'imar Allah mai yawa da ya yi musu.
Banu Isra'ila su ne jikokin Annabi Yaqoob AS. A nan Allah yana nuna musu ni'imar da ya yi musu, kuma yana umartar su da su zama masu cika alƙawari, idan sun yi hakan shi kuma zai ba su abin da ya alkawarta musu na shiga Aljanna. Ya tunatar da su kan su ji tsoronsa shi kadai sannan ya umarce su da su gaskata Alkur'ani ta hanyar imani da shi da aiki da abin da ya ƙunsa na shari'a, saboda yana ɗauke da irin abin da ya zo cikin littafin Attaura ta Annabi Musa wanda ya danganci Tauhidi, don haka ya gargaɗe su da kada su zama su ne na farko da za su kafirce wa wannan Alƙur'ani da wanda aka saukar wa Alkur'anin shi ne Annabi Muhammadu SAW. Har ila yau ya hana su musanya ayoyin Allah da wani abu na ƙyale-ƙyalen duniya wanda a wurin Allah ba a bakin komai yake ba, ta hanyar watsi da imani da Alkur'ani da abin da Manzon Allah ya zo da shi da ɓoye gaskiya da take ta.
Hakanan ya hana su cakuɗa ƙarya da gaskiya tare da ta alhalin sun san irin illar da take cikin yin hakan. Kuma ya umarce su da tsayar da salla da rukunnanta da wajibanta, su bayar da zakkar dukiyarsu, sannan su tsayar da salla cikin jam'i tare da sauran muminai. Sannan Allah ya zarge su da abin da suke yi na umarni da kyakkyawan aiki da hana mummuna, amma kuma su a karan kansu ba sa aiki da abin da yake cikinta na hukunce-hukunce, wanda yin haka ya saɓa wa aikin mutane masu hankali. Daga bisani Allah ya umarce su da su nemi taimako ta hanyar tsayar da salla da hakuri cikin duk al'amura, duk da cewa salla tana da nauyi ga wasu in ban da masu ƙasƙantar da kansu ga Allah wadanda su ne suka tabbatar da cewa, akwai ranar gamuwarsu da Ubangijinsu wadda ita ce ranar alkiyama.
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:
- Tuna wa bawa ni'imar da Allah SWT ya yi masa ya fi zama hujja a kansa, yakan kuma sanya shi ya karbi gaskiya da wuri.
- Allah SWT ya yi babbar ni'ima ga Banu Isra'ila.
- Idan Allah ya yi wa kakanni ni'ima to kamar ya yi wa jikokinsu ne, domin birbishin ni'imar da ya yi musu dole sai ta shafe 'ya'yansu da jikokinsu. Kuma ba don ya kuɓutar da kakanninsu ba ai da su ma ba a same su ba.
- Wajabcin gode wa ni'imomin Allah SWT da guje wa butulce masa.
- Wajibi ne wanda ya yi bakance na alheri ya cika bakancensa.
- Alkur'ani littafi ne da yake gaskata littattafan da suka gabace shi, yake kuma tabbatar da abin da suka zo da shi na gaskiya da kadaita Allah. Hakanan su ma littaffan da suka gabata suna tabbatar da gaskiyar Alkur'ani da ingancin manzancin Annabi SAW.
- Duk wanda ya fara kafirce wa Allah, kuma ya zamanto abin koyi ga na bayansa cikin kafirci, to lalle zai dauki nayin zunubansa da na wadanda suka bace a dalilinsa.
- Duk wanda ya sayar da ayoyin Allah da 'yan kudi kadan, to lalle ya yi koyi ne da Yahudawa.
- Wajabcin bayanin gaskiya ga mutane da haramcin boye ta. Idan kuma wani ya boye gaskiya saboda wani abin duniya da zai samu, to wannan laifinsa ya fi tsanani.
- Wajibi mai karantawa ko da'awa ya riqa qoqarin yaye wa mutane shubuhohi da yi musu bayanin duk abin da ba su fahimta ba. It is obligatory for the reciter or preacher to try to clear people's doubts and explain to them everything they do not understand. Kuma duk wanda yake a wurin da babu wanda zai koyar da mutane sai shi, to dole ne ya tashi ya koyar da su abin da suke buqata na addini. And whoever is in a place where there is no one to teach people except him, then he must rise up and teach them what they need in religion.
- Haramun ne
pg57